22 parts Ongoing Ga rayuwar da yawa daga cikin ƴan Adam sukan iya fakewa da ƙaddara ko ruɗin shaiɗan. Sai dai a rayuwar wasu duka babu ɗayan da ke kasancewa daga cikin biyun da na lissafa, ciki kuwa har da ni kaina. Na tsammaci shiga gidaje masu manyan benaye da zama a cikin su kan iya mantar da kai wani mataki kake a yanzu?Haka na iyakance adadin motocin da zuciya ke muradin hawa. Ga irin rayuwar da nake gudanarwa na tasamma ware nau'ikan ababen cimaka don gudun gamuwa da wata lalurar, ko da kuwa jariri ce. Duk wata kusafa da na san zan iya gamuwa da talaka ko mai matacciyar zuciya da baya ɗauke da buri, ina iya kokarin don ka da mu gamu.
A lokacin da lamarin zai soma ne duniya tamin atishar tsaki ta yadda komai da komai da ya wanzu a cikin rayuwa ta sai da ya zama ya disashe tamkar bai faru ba, hatta lafiyar da nake ganin ta jima tana walankeluwa dani wuri guda, yo i mana. Duk sa'adda wannan lamarin ke wakana ciwon kai banyi, sai dai a yau cutar dake tare dani, ko kuma ince cutuka, baza su zamo silar kai ni ƙas ba, sai dai lamarin da ya haɗoni da komai tunda fari ya zame min sanadi.