ROYAL CONSORT 2

By Oum_Tasneeem

7.6K 278 37

Cigaban labarin ROYAL CONSORT littafi na daya Labarin ROYAL CONSORT labarine irinshi na farko a cikin labara... More

Page 1:Part 4: The Special Court Lady
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Part 5: THE RETURN OF THE QUEEN
Page 15
Page 16
Part 6: THE ROYAL CONSORT
Page 18
Part 7: LABARIN SHUKRIYYA
Page 20
Page 21
Page 22
Page 23
Page 24
Part 8: CIGABAN LABARI
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Part 9: CONSORT SUK
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47
Page 48
Page 49
Page 50
Page 51
Page 52
Page 53
Page 54
Page 55
Page 56
Page 58
Page 59

Page 57

109 2 0
By Oum_Tasneeem

Page 57

Queen Afreen tana dawowa palace dinta shukriyya ta biyo ta,bata ma kai ga shiga ciki ba ta tsaya cikin murmushi ta kalli consort Sook

"Yaya kikai da fudail?"

Qasa shukriyya tayi da kanta

"An tafi da shi kurkuku! Amma yana cikin matuqar kaduwa da abinda ya faru domin baiyi tsammanin hakan ba!"

Lumshe ido queen Afreen tayi

"Hakane! Ba zai taba tunanin haka zata faru ba,Nima hankali na bai taba kawo min haka ba har sai da kika sanar dani cewar mai martaba yana son yayi murabus! Amma kafin sannan,na yadda da duk abinda fudail yake fada min dari bisa dari! Kuma na godewa Allah da yasa banyi mummunan kuskure ba!"

Murmushi shukriyya tayi

"Your majesty! Daga lokacin da na karbi umarnin ki na cewar zan bar masarauta a ranar,na damu sosai,shiyasa da nazo wajenki........."

FLASH BACK!

A ranar da shukriyya ta je wajen queen Afreen domin ta janye umarnin matso da tafiyarta har sai mai martaba ya dawo,Babu wanda ya san abinda suka tattauna,kawai dai shukriyya ta fito tace a shirya tafiyar kamar yadda queen tayi umarni,to ga abinda ya faru

"Your majesty! Ina son in yi miki wata tambaya! Shin saboda Fudail ne kika bada umarnin tafiya ta a yau? Har yanzu kina tunanin cewar zan cutar da crown prince ne?"

Shiru queen Afreen tayi,Shukriyya ta cigaba da magana

"Your majesty! Jiya daddare da kika je waje na,kin tuna ina qoqarin sanar da ke wani abu kafin a fada miki fudail yana neman ki?"

Jinjina kai kawai queen Afreen tayi,shukriyya tace

"Your majesty! Mai martaba Murabus zai yi! Kuma ya yanke wannan hukuncin ne domin ya kare rayuwar Crown Prince tare da Prince Yeon!"

Zaro ido queen Afreen tayi,wanda yayi daidai da mummunar faduwar gaba tace

"Me kika ce? Murabus?"

"Fudail ya san da haka your majesty! Abinda ya fi jin tsoro a yanzu ba ma tunanin ina son hallaka crown prince bane,abinda yafi tsoro shine Prince Yeon ya samu mulki da qarfin iko fiye da shi!"

A gigice Queen Afreen tace

"Consort Sook! Yanzu consort Sook...."

"Your majesty! Idan har Fudail ya tsara in bar cikin masarautar nan a yau,tabbas akwai wani abu da yake shiryawa,Hakan yana nufin matuqar muna son sanin abinda ya shirya din,ya zama dole sai na fitan,saboda tsarinsa ya tafi daidai! Amma kafin nan Shin zaki iya yarda dani? Ki bani wannan damar domin na nuna miki ainihin wanene fudail! Ki taimaka ki bani damar nan your majesty!"

*********
Sannan kuma bayan Shukriyyah ta samu labarin fitar crown prince a ranar,har ta he ta samu su nadeeyah,Nadeeyah ta bawa Afrah takadda ta kaiwa shukriyya,shukriyya ta fito zuwa Queen's palace da takaddar! Miqewa queen Afreen tayi

"Ga wannan! Na saka office of investigation sun yi min bincike yanzun nan! A yau dinnan an canja hanyar da crown prince ya kamata yabi domin zuwa liyafar da suka ce ya tafi,a maimakon hanyar da aka saba bi,sai aka canja zuwa hanyar da ni zan bi domin zuwa Yihyun palace! Hakan yana nuna akwai abinda suka shirya akan hanyar! Kuma hakan shirin fudail ne! Ki yarda dani your majesty!"

Duba takaddar takeyi cike da gamsuwa da abinda yake ciki.

Haka nan bayan fudail ya fada mata ta bayar da emergency decree ya tafi,ta rikice sosai domin ta rasa wanda zata yadda dashi tsakanin fudail da consort Sook! A qarshe dai ta bayar da decree din kama fudail ba tare da samun qwaqwaran dalili ba.

BACK FROM FLASHBACK

kallon shukriyya tayi

"A lokacin,nima kai na ban san dalilin da yasa na ji na yanke wannan hukuncin ba! Ban san meyasa na bayar da umarnin kama fudail ba ke ba! Sai dai dama na dade ina jin a raina kamar akwai baqon lamari a cikin abinda na gani daga gareki! Abu ne mai wahala mace kamar ke! Matar sarki,kuma wacce take da yaron da ta haifa! Amma kina qoqarin kare rayuwar Crown Prince! Duk wanda yake kallon hakan,zai ganshi ne a matsayin makirci zallah! Kuma ban san meyasa zuciyata ta yadda da cewar kina yin hakan har cikin zuciyar ki ba! Amma duk da haka ina buqatar hujjar komai daga gareki!"

"Yes your majesty! Zan tabbatar miki da cewar komai shirin fudail ne! Ba zan taba watsar da yaddar da kikai min ba!"

...................................

Fitowar abdallah kenan daga inda aka ajiye shi,naseer ya rako shi palace din consort sook! Bayan sun zauna suna magana naseer yace

"Kuna nufin kun san da haka shiyasa aka samo private guards din?"

Jinjina kai shukriyya tayi

"Hakane! Na fahimci cewar fudail ya karbi jagorancin dukka jami'an tsaro ne saboda mu dauki private guards! Shiyasa mukai hakan domin tsarinshi ya tafi daidai!"

Naseer kamar zaiyi kuka yace

"Amma kawai sai kukai tunanin ku dinga bin tsarin sa?"

Girgiza kai shukriyya tayi

"Ban taba tunanin zai saka rayuwar crown prince a ciki ba!"

Murmushi naseer yayi

"Toh ai kuma yanzu matsalar ta fara! Ta yaya zamu nemo qwaqwarar hujja?"

"Inspector Naseer! Ai tuntuni mun fara wannan shirin!"

"An fara shiri kuma?"

"Ehh! Mai martaba zai je ya samo hujjar da kanshi!"

Cike da rudani naseer yace

"Ta yaya kenan?"

"A lokacin da Fudail ya karbi jagorancin jami'an tsaro! Na sanar da yayana abinda nake zargi,ga yanda abin ya kasance......."

***********

FLASHBACK

Suna tsaye suna kallon yanda fudail yake rarraba sojojin a cikin masarauta,Shukriyya ta kalli Abdallah

"Fudail mutum ne mai tsananin wayo! Na tabbata ba zai yi yunqurin saka makami ya hallaka mu ni da Noor ba!"

"Kina nufin ba zai yi wani yunquri a cikin masarautar nan ba?"

"Ehh! Haka nake nufi! Shiyasa babu buqatar royal guards su dawo masarauta!"

"Kenan za'a buqace su a wani wajen?"

"Ehh! Shiyasa zamu turawa Chief Suh da mai martaba saqo!"

****

A lokacin da saqon ya riski mai martaba yana daji wajen farauta,karbar takaddar yayi ya bude,Seal din shukriyya ya fara cin karo da shi (Stamp)

"Wannan ai seal din Shukriyya ne!"

Chief eunuch da yake bayanshi a tsaye sai da zuciyarsa ta buga,zaro ido mai martaba yayi a lokacin da ya karanta abinda takaddar ta qunsa,shine dalilin zuwansa a firgice ya tarar da chief Suh yana hawa doki domin komawa masarauta,dakatar da shi yayi tare da bashi takaddar ya karanta

"Wannan shine saqon Consort Sook! Me kake tunani akai Chief Suh?"

Rufe takaddar chief Suh yayi

"Na yadda da hukuncin da tayi your majesty! A iya sanin da nayiwa fudail,ba zai yi yunqurin hallaka ta ba! Domin idan yayi hakan,karbar jagorancin jami'an tsaro zai zamar masa matsala kuma zai zama babbar hujja a kan sa! Hakan yana nufin......"

"Yana nufin ba Consort sook ko kuma Prince Yeon ne zasu shiga hatsari ba! Shiyasa tayi tunanin idan har za'a bi duk motsin mutanen fudail,za'a samu amsar abinda suke shiri! Idan yanzu na tura da umarnin cewa a bar jami'an tsaro daga cikin masarauta suyi aiki,za'a gano su da wuri! Amma tunda royal guards suna nan,zasu iya yin aikin ba tare da kowa a cikin masarauta ya sani ba! Ka fahimci me nake nufi Chief Suh?"

"Yea your majesty! Jami'an masarauta da suka fi dukkan jami'an qasar nan qarfi wato royal guards zasu fita cikin sirri!"

Jinjina kai mai martaba yayi cike da gamsuwa.

******

BACK FROM FLASHBACK

Shigowa tayi office of investigation,miqewa sukai dukkansu tare da rusunar da kansu

"Kun bincika abinda ya samu abincin?"

Kallon abincin da yake kan teburin su sukai

"Yes your highness! Akwai wata guba mara qarfi da aka zuba acikin ruwan da suka sha(masu daukar palanquin)"

Jinjina kai shukriyya tayi ta kalli nadeeyah

"Shikenan! Ku yi abinda ya kamata har a samo masu laifin!"

"Yes your highness!"

Ta amsa.

....................................

Ladies investigators ne suka shigo kitchen qarqashin jagorancin sumayya,an jere kitchen maids din gaba daya,su kuma jerin masu daukar palanquin din shukriyya suna biye da su sumayya,tsayawa tayi ta kalli kitchen maids din sannan tacewa mazan

"Zaku iya gane wacce ta baku ruwan?"

"Yes my lady!"

Duddubawa suka fara yi domin samo wacce ta bayar da ruwan don mai daukar palanquin din yayi rashin lafiya,wanda har ya jawo jinkirta tafiyar shukriyya da gan-gan.

........................................

Yayin da Royal guards suka cika cikin garin a boye,duk wani minista da yake bangaren Fudail akwai royal guard din da yake bin shi domin daukar bayanan abinda yakeyi,da inda yaje,da wanda yake mu'amala da shi.

Wasu royal guards su hudu suna labe suna hangen gidan babban minister,wasu ministocin ne guda uku suka shigo gidan hankali a tashe

"Your exceelency! Fudail fa yana can a tribunal! Zai fara amsa tambayoyi!"

Wani a cikinsu yace

"Wannan emergency decree din Queen ne! Babu abinda zamu iya yi a kai!"

Babban minista yace

"A'ah ba zamu bar hakan ta faru da fudail ba! Idan har yayi bayanin cewa mun san komai! To lallai tamu ta qare mu ma!"

Wani a cikinsu yace

"Abinda ya kamata muyi shine! Mu kawar da duk wani abu da zai danganta mu da abin! Mu batar da duk wata shaida!"

Da sauri babban minista yace

"Hakan zaku yi! Da hanzari! Dole mu nemi mafita kafin ya kira sunayen mu!"

Wani steward suka kirawo a take,suka aikeshi zuwa inda suka siya boma-boman da akai amfani da su,rashin sanin cewar royal guards suna biye da su har inda aka siya bomb din,sun fara magana da masu wajen kenan

"Zaku bar garin nan ne zuwa wani dan lokaci! Ga wannan na san zasu ishe ku har zuwa lokacin da his excellency zai neme ku!"

Kafin su ankara royal guards sun kewaye su,sunyi yunqurin guduwa hakan yasa suka fara fada da royal guards din,har aka yiwa chief Suh mummunan yanka a hannunsa,dafe wajen yayi yana kallon sararin samaniya yace

"Ashe wannan shi ne ma'anar faduwar tauraron da na gani?"

Da sauri lieutenant Nam yace masa

"Me kace?"

Murmushi chief Suh yayi

"Faduwar tauraro yana iya nuna ma'anar cikar buri!"

Ajiyar zuciya liutenant Nam ya sauke

"Hakane! Wani lokacin camfin mutane yana da ma'ana!"

...................................

Ministocin gaba daya hankalinsu a tashe kasancewar sun ji shiru daga wajen steward din da suka aika wajen masu bomb! Suna tsaye su hudu suna jira cikin alhini da tashin hankali

"Your excellency! Ko dai an samu wata matsala ne?"

Babban minista cikin kaduwa yace

"Bamu da lokacin batawa! Ku koma gidajenku ku shirya mu tafi masarauta! Ya zama dole mu samu Queen Afreen kafin mai martaba ya dawo......"

"Babu buqatar gaggawa Babban minister! Domin kuwa ban kai ga komawa masarautar ba!"

Jikinsu ne duk ya fara rawa ganin bayyanar mai martaba a gabansu,a rikice suka rusunar da kansu a tare suka ce

"Cheo-naaa!"

Ran shi a bace ya qaraso inda suke tsaye

"Kuma sannan babu buqatar sai kun koma gida kun shirya cikin alkyabbarku ta ministoci! Babban minister! War minister! Tribunal minister! Zaku yiwa royal guards rakiya!"

Ya fada cikin fada da cijewa,idanuwansu ne suka ciko da qwalla,a tare suka durqushe a wajen,tsohon banzan ya fara magana

"Cheo-naaa! Cheo-naaa!! Me kake nufi da haka? Bamu fahimci..."

"Yi min shiruuuuuu!!! Yi min shiru babban minister! Ina baka shawarar ka kama bakinka kayi shiru!!! Amma fa idan kana da burin yau ka kwana a duniya! Idan kuma baka da burin qara kwana a duniya sai ka qara magana ka gani!"

Kuka ne ya kubce musu gaba dayansu suna fadin

"Cheo-naaa!!!! Cheo-naaaa!!"

.................................

A hanya suka hadu,Shukriyya tana dawowa daga Office of investigation,shi kuma mai martaba yana kan hanyar zuwa palace din ta,Shi ya fara gano ta hakan yasa ya kira sunanta da qarfi

"Shukriyyahh!"

Dago kanta tayi cikin bazata da mamakin jin muryarsa tare da tsayawa cak tana kallon shi,da sauri ya matso inda take yayinda duk attendants din suka rusunar da kansu qasa,janyota yayi ya rungume ta,rarraba ido ta fara yi saboda attendants din da suke wajen,a hankali ta furta

"Cheo-naaah!"

Kafadarta ya riqo tare da cire ta daga jikinsa yana dudduba dukka jikinta

"Kina lafiya ko? Babu abinda ya same ki ko?"

Murmushi tayi

"Babu abinda ya sameni Cheo-naah! Lafiyata qalau!"

"Kiyi haquri shukriyya! Ya kamata ace nayi tunanin abu irin wannan zai iya faruwa idan bana nan!"

"A'ah Cheo-nah! Ka daina bani haquri,ai ka gama min komai,domin kai ne kayi min aikin!"

Girgiza ta yakeyi

"Ba zan taba yafe musu ba! Ba zan barsu da rayuwar su ba akan wannan abin da sukai miki ke da Prince Yeon!"

...................................

Washegari da safe,An riga an fara azabtar da masu laifin domin ana son su amsa laifin su da bakinsu,Babban minister,ministan tribunal,ministan yaqi na daya,na biyu,da na uku wato fudail duk suna zaune a kan kujerar katakon da ake gana musu azaba mai radadi,kuma abdallah ne yake jagorantar azabtarwar,duk sun galabaita sun fita daga hayyacin su,fudail kam har bakinsa ya karkace ma da qyar yake iya magana don bakin ya cika da jini saboda radadin azabar da ake musu,suna ta ihu mai tayar da hankalin mai sauraro,daga bakin qofar hall din da suke aka daga murya tare da fadin

"HIS MAJESTY! THE KING!"

Dakatawa akai da yi musu azabar har mai martaba ya shigo ya zauna yana qare musu kallo,Fudail ne ya bude baki da maganarsa da bata fita yace

"Cheo-naa! Na rantse ban san komai ba! Sharri ake min! Ni banyi yunqurin cutar da crown prince ba,Duk sharri da makircin Consort Sook ne your majesty!"

Ya qarasa maganar da qyar don ko kansa ma ya kasa tsayuwa sai karkata shi yake daga wannan gefen zuwa wancan gefen,cikin murtuke fuska da kakkausar murya mai martaba yace

"Ministan yaqi na uku! Ina ganin ba ka fahimci abinda ya kawo ni nan wajen ba! Ka bude kunnen ka ka saurareni da kyau fudail! Ban zo nan wajen don in ji wani uzuri daga wajenku ba! Kuma ba nazo bane domin ina son naji kun amsa laifin ku ba! Domin ta tabbata ka aikata komai dumu-dumu! Kuma kasan hukuncin laifin da ka aikata? To ba za ma ka mutu cikin salama ba! Ku cigaba da azabtar da shi!"

Ya qarasa maganar yana kallon abdallah da yake gefenshi,juyawa abdallah yayi ya kalli mutanen da suke tsaye a bayan su fudail tsawa

"Ku cigaba da azabtar da masu laifin!"

"Yes sir!"

Suka amsa sannan suka cigaba da gashi.

................................

"Your majesty! Consort Sook tana neman iso!"

Da faffadan murmushi a fuskarta ta bawa chief maid din amsa

"A shigo da ita!"

Shigowa shukriyya tayi tare da rusunar da kanta tace

"Your majesty!"

Sannan ta zauna,cikin farin ciki queen Afreen tace mata

"A qarshe dai kin bani gamsashshiyar hujja consort Sook! Kin burge ni sosai! Kuma ina mamakin yadda akai kika shirya komai!"

Murmushi itama shukriyyan tayi

"Your majesty! Saboda adalcin ki ne har na samu nasarar aikata komai! Hakan ba zai taba yiwuwa ba da ace baki bani yardar ki ba"

Girgiza kai Queen Afreen tayi

"Ina matuqar yi miki godiya consort Sook! Domin kin cece ni daga aikata gagarumin laifi,kin cece ni daga yiwa qasata da kuma karagar mulki mummunan zunubi! Nagode sosai!"

Murmushi shukriyya tayi ta sunkuyar da kanta qasa.

................................

Fuskar shi a murtuke ya zauna a kan karagar mulkinsa da take grand hall,Ministocin da suke zaman fada suna zaune duk a jejjere a qasa,gyaran murya yayi kafin ya fara bayani kamar haka

"A yau! Bana son jin wata jayayya ko roqo! Domin sun kamu dumu-dumu a cikin laifin da suka aikata! Saboda haka zan hukunta su ba tare da tausayawa ba! Babu sassauci a garesu! Ina fatan kun gane!"

Shiru kowa yayi a wajen,jin haka yasa mai martaba qara daga murya yace

"Chief Secretary! Fado musu hukuncin!"

"Yes your majesty!"

Chief secretary da yake tsaye a gefen mai martaba ya bude takaddar ya fara karantowa,sai da ya gama karanto sunayen masu laifin sannan ya cigaba da karanto hukuncin kowannen su kamar haka

"Ministan yaqi na uku wato Fudail Amir Fuzail,da kuma officer Liutenant din sa za'a fille musu kai ba tare da bata lokaci ba! Sannan kuma za'a rataye kawunan nasu a kan qofofin shigowa birnin joshun domin har masu tasowa nan gaba su samu irin baqin tarihin da ya kafa! Babban minista tare da sauran ministoci da suke tare da shi,za'a kore su zuwa qauyukan bayan gari tare da ayyuka masu wahala,daga nan kuma za'a kashe su bayan wata uku! Da fatan hakan zai Tabbatar da zaman lafiya,da kwanciyar hankali a cikin masarauta da kuma qasar baki daya!"

..................................

An kwashe masu laifin duka an fitar dasu daga masarautar domin yanke musu hukunci,kamar yadda mai martaba ya umarta,an ciro kawunan fudail da kuma liutenant dinsa,an saka musu wasu sinadarai da ba zasu taba rubewa ba,an saqala su a qofar shigowa birnin joshun,shikenan sun zama tarihi.

...................................

Ministocin dukkansu cikin hawaye suke roqon mai martaba bayan ya sanar da decree dinsa ta murabus,dukkansu kuka sukeyi suna roqon ya janye hukuncin sa amma ko kadan bai saurara ba,Chief Suh har ma da shukriyya sun qara qoqarin nusar da shi amma yaqi.

Crown prince ne a tsugunne a bakin qofar Grand palace yana kuka yana fadin

"Abaa-maamaah! Ba zan yi biyayya ga umarnin ka ba! Ka taimaka ka janye hukuncin ka! Ba zan karbi kujerar mulkin ka ba abaa-maamaah!"

Har dare yana tsugunne a wajen yana roqon mai martaba,bai ci abinci ba,ko ruwa bai karba ba tunda ya fara Repentance ritual din,shukriyya tana hango shi har cikin ranta tana jin ciwon tausayin yaron,dama ba lafiya ce da shi ba,jikin babu qwari gashi kuma yana repentance ritual,juyawa tayi ta kalli basma a rude tace

"Zan yi magana da Queen!"

Da sauri take tafiya har hardewa takeyi zuwa queen's palace,itama queen Afreen din tana cikin damuwa a lokacin da chief maid dinta take ce mata

"Crown prince yana can yana Repentance ritual! Ma'aikatan gwamnati gaba daya da kuma ministoci suna ta zanga-zanga! Amma mai martaba yaqi janye hukuncin sa!"

Shiru queen Afreen tayi sai huci kawai da take saukewa akai-akai,chief maid din ta qara cewa

"Your majesty! Meyasa ba zaki ce komai ba? Ko zaki je wajen mai martaba...."

"Shirya! Akwai inda zamu je yanzun nan.."

Queen Afreen ta fada tana miqewa cikin hanzari.

Oum tasneem ✍️

Continue Reading

You'll Also Like

37.6K 4.3K 50
ဘာသာပြန် by Legacy Novel Translation
22.1K 1.4K 23
labari ne a kan mata biyu wayanda suke soyayya da mutum daya. aminan juna ne, labari ne me tsantsar yaudara,fushi,butulci,amintaka,kisa ku biyo ni da...
Baveen By جيمي

Historical Fiction

166K 18.5K 40
__ ايتها الفتاة المنسيه التي لا يعلم عنها احد ، هذه البلاد تسير بالقانون لا بالاستثنائات __ مكانكَ هذا محرم عليه دخول الاناث وانا هنا ، الا يعد هذا...
2.1K 148 10
Aure Ko Ajali follows a story of a 21 year old Mait whose life took a complete turn after she was set on an arranged marriage with her cousin. This s...