RUHI BIYI (a gangar jiki daya)

By Abdul10k

1.9K 104 8

Hakan ya furta cikin kasar zuci,amma ko cikin karfi irin ta tsatsuba Nainah ta saurari komi....... Gajeriyar... More

EPISODE_1
EPISODE_2
EPISODE_3
EPISODE_4
EPISODE_5
EPISODE_6
EPISODE_7
EPISODE_8
EPISODE_9
EPISODE_10
EPISODE_11
EPISODE_12
SEASON_2 EPISODE 1
SEASON_2 EPISODE_2
SEASON_2 EPISODE_3
SEASON_2 EPISODE_4
SEASON_2 EPISODE_5
SEASON_2 EPISODE_6
SEASON_2 EPISODE_7
SEASON_2 EPISODE_9
SEASON_2 EPISODE_10
SEASON_2 EPISODE_11
SEASON_2 EPISODE_12

SEASON_2 EPISODE_8

40 3 0
By Abdul10k

🧟‍♂️🧟‍♀️☠️☠️🧟‍♂️🧟‍♀️

    
        *RUHI BIYU*
  _[a gaangar jiki daya]_
                       *RETURNS*

                       🧟‍♀️🧟‍♂️☠️☠️🧟‍♀️ 🧟‍♂️      ‍

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
      _Kungiya d'aya tamkar da dubu._

        *_SPECIAL EDIT 2021/2022_*

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*Phone no:*
2349077974042

         *REPORTS*

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*📣📣📣SANARWA SANARWA📣📣📣*
_Ga masu Bin littafin Kofar aljali littafi na biyu Ina Mai Baku hakuri game da rashin posting da kuka ga ba'ayi gaskiya abubuwa ne sukayi yawwa..._
_dan hakan Ina Mai Mika sakon ban hakuri ga fans inshallah bada jimawa ba zaku jini love you all_

*😷😷STAY SAFE...  STAY AT HOME😷😷*

*FREE BOOK💯✅*
*📚LITTAFI NA BIYU*
*EPISODE_0️⃣8️⃣*



"Raiha!."

"Na'am, You found anything?."

"Not Really,just Naga dakin ne Bata kama d'a na Miji ba."
Haka Harun ya Bata ansa ita ko Raiha ta juyo ganinta ta kalli cikin idanun sa kafin tace dashi.

"Hmm maiyasa kace Haka?."
Tambayar da Raihana tayi Masa kenan inda Harun ya mayar Mata da cewa.

"Just imagine Raiha,wannan kayataccen guri wa zai kasance cikin inba mace ba."

Da jiyo haka Raihana ta d'aga Idanu ta kalli cikin dakin Bayan tayi Haka ko tayi gajeriyar murmushi Hadi da cewa..

"Harun! Dakin da Babu komai a ciki,shine kake iyya banbance na mace ne ko na d'a Miji ne,hmm."

"Aww Daman baki ga hakan ba,Ni a tunani na zuwanmu tare Nan gurin zai saka mu iyya banbanta dakunan Jensin mu,Amma madadin Haka sai Ni naketa tantance Komi."
Fadar Harun kenan inda Raihana tayi saurin mayar Masa da martani.

"Harun gaskiya baka rabo da abin Dariya, Dalilin Zuwan mu Nan guri shene mu bawa kanmu haske akan abinda ke faruwa sa'annan mu warware kullin da muka kasance a cikin,mu Kuma San dalilin Safras na aikata wannan...and lastly Ina fatan mu iyya ceto rayuwar mu'azz...."
Bayan ta furta hakan tayi ajiyar zuci kafin ta cigaba da cewa.

"Domin 89% na zuciyarta na sanar Dani cewa wancen ba Mu'azz bane na gaske,domin Komi nashi ya banbanta Dana Mu'azz din asali....
A zahirance na nuna Babu Komi Amma a kasan Raina yana ta yimin rad'ad'in domin kullum fatana shine karna rasa shi kamar yadda na rasa Mahaifiyata.."

Kwalla ce ta zubo a fuskarta yayinda tayi saurin sharewa da hannu sa'annan ta juya ganinta Kan fuskar Harun yayinda tasa murmushi karya a fuska sai ta sake cewa dashi.

"Harun kafin nasan Safras kullum addu'a ta shine karna rasa Yaya mu'azz Kamar yadda na rasa Mahaifiyata domin shine wanda ya maye gurbin ta bayan ta rasu,ya daibemin kewa ya Kuma bani kulawa ta mussanman tamkar ta mahaifiya da y'ar ta,I always sleep a kafadar sa sa'annan yayinda na kasa bacci shima baya iyya bacci,yakan kawana idonsa biyu idan bani da lafiya,yakan Hana kansa abinci domin ya bani,ya bani Komi na rayuwarsa ya bani kula,gata,tarbiya wacce hakane yasa na iyya tsayuwa Yanzun a gabanka nake baka wannan labari...
Kafin yanzu ban Tabba sanin akwai Wanda Zan sake sakawa a Raina kamar Mu'azz ba,Amma bayan baiyanar Safras sai Wannan buri tawa ta kasance biyu Amma Yau sai gashi Ina gaf da rasa dukkanin su biyu."

Bayan ta furta hakan sai kwalla ta soma kwararo a fuskar ta yayinda take kokarin tsai dasu Amma ta gagara hakan...
Harun tuni jikinsa tayi sanyi bayan yaji wannan batu na Raihana,baidai zubar da kwalla ba Amma sun ciko idanun sa Kuma dalilin sa na rike kwalla ko shine daga zarar ya zubar da kwalla Babu ta yadda zaiyi ya iyya lallashe ta.

"Raiha a tunanina inada kwakkwarar dalili na zuwa Nan gurin,amma Bayan naji bayanin ki saina gane cewar bani da daya cikin Goma idan aka hada da naki,Domin da Zaki tambayeni meye dalilina bazai wuci nace Miki Dan soyayya ba,Amma ke sai Kika hada soyayya,kauna da Kuma muradi a lokaci guda Kinga kenan ko kafarki ban Kama ba....
Insha Allah Raiha Komi zai dawo daidai Mu'azz da Kuma Safras duk zasu dawo gare mu,kedai kawai ki kwantar da hankalin ki."

Bayan ya furta hakan yasaka hannu cikin aljuhu ya ciro hanki ya Mika Mata,itako ta ansa ta soma share kwallar dake fuskar ta.

Aiko duk wannan tattaunawar da Harun da Kuma Raihana sukayi ta sauka kunnuwan mu'azz din da jiyo haka ko fuskarsa ta sauya ya dawo abin tausayi...
Aiko cikin sauri ya Soma taku yayinda sauran mu'azz dinnan biyu suka bishi a baya...
Hayewa tololuwar ginin yayi inda ya tsaya cek bayan yayi arba da hadirin Nan Aiko baiyanar Mu'azz din Nan biyu a sama rufin yayi daidai da sakar wata matsifeffiyar Kara Mai fasa dokin kunnuwa wacce wannan Kara Saida ta ragargaza duk glas, mirrors dadai sauran kayan fashewar da suka kasance cikin wannan gini ba tare da sun lallace ba but duk suka fashe ta sanadiyar wannan kara.

Haka cikin wannan gini lungu da sako saida wanna Kara tabi wacce tafi karfin sauraron kowa Saida dukkanin mutanen da suka kasance ciki wannan gini suka taushe kunnuwansu illa Harun da Raihana ne kadai basuyi hakan ba..

Idan muka sake lekawa saman rufin ko still mu'azz na sakar wannan Kara wacce take fitowa daga makogoronsa wacce tasa mu'azz dinnan biyu suka taushe kunnuwansu Suma Danko Karan tafi karfin su.

Tsit kakeji yayinda gurin tayi Shiru Aiko Babu abinda sauran ke jiyo domin jinsu ta dauke na wasu Dakiku..

"Shugaba wannan karar zata iyya tarwatsa duk aikin da mukayi anan gurin,kasan da hakan?."

"Nasan da hakan,Kuma nama fika sanin Haka,domin Kai ka samune daga karfin ikona"
Hada fuska Wanda aka gayama wannan magana yayi yayinda dayan mu'azz din yayi furucin cewa..

"Bamusan mayya saka kayi hakan ba,Kuma bamu da bukatar sanin hakan Amma wacce tabbaci muke dashi na cewa daga Safras muke ansar wannan umurni badaga Nainah ba."

Aiko juyawar da mu'azz zaiyi sai ya yimar tsawa cikin fushi wanda hakan ne ta sakaci ya dagargaje ya dawo turbaya ya tarwatse...
Dayan Nan ko yayi saurin rusunawa gaban mu'azz din yayi saurin cewa.

"Kayimin ahuwa my Lord,domin ka Samar damune domin muyi maka hidima kawai badan bincike ba Amma ka sani bayan rashin Zuciyar da muke dashi munaji ba Dadi idan muka ga Shirin mu na rushewa,bawai Dan banason rabuwa da rayuwa bane nake furta haka A'a Dan banason kasake rasa sashi na jikin ka Kamar yadda kayi Yanzun wanjen Kona wannan abokin aikin nawa Domi dukkan ninmu biyu sashine na jikin ka."

Dajiyo hakan ya hada fuska sa'annan juyawa mu'azz din dake durkushe baya sa'annan ya ce dashi.

"Na baka umurni ka shiga ciki ka fituni kowa,ka Kuma sa su yabama Aya zakinta.."

"Angama."

Bayan ya furta hakan ya tashi tsaye Aiko cikin abinda bai wuci dakika guda ba ya bacce.

#Ramla
Rukiya akeyi Mata yayinda abban ta da Kuma ummarta ke tsaye bakin kofar suna kallon abinda ke faruwa,Malamin Rukiyan tare da Almajirin sa ke ta fafatawa wajen ganin Ramla ta dawo bacci...
Amma hakan ba Abu bane Mai sauki domin yayinda suke yimata rukiyar illa Shure Shure take yayinda idanun ta suka juye.

Aiko bude Idanu tayi inda ta kalli cikin idanun Malamin Rukiyan,ganin Haka yasa Malamin ya dibo ruwa a tafin hannun yayi wasu katu a ciki ya watsa Mata a fuska.

Ihu Ramla tayi sa'annan ta soma kokarin kwatar kanta daga hannun su...

"Mayyasa kake kokarin cutar Dani."

"Ko Kuma kuke kokarin cutar da baiwar Allah ba?,maiyasa kuke kaunar ku cutar da Mai rauni ne Bayan kunsan karfin ku tafi na bil'adama."

Aiko hakan kawai iyyayen Ramla suka iyya jiyowa bayan Nan Babu Komi domin Almajirin Malan din tashi yayi ya rufe kofar.

#Faruq
Tafe yake cikin tsoro yayinda duk motsi kadan dayaji Yana firgita.
Rike yake Kuma da wayarsa a hannu yayinda yake haska hanya dashi,Aiko Yana cikin wannan yanayi sai yajiyo sawun kafan mutum cikin sauri ya waiga inda yayi saurin tambaya.

"Waye?."

Shiru Babu ansa,shiko ya sake a Karo na biyu....

"Waye anan gurin."

Sake jiyo wani Kara yayi Nan da Nan ya razana,idan ya haske bangaren da touch light...
Taba kugunsa yayi yaga Babu bindiga Nan sai yayi fuskar kuka dukda yasan bindigar ba cetonsa zatayi ba.

Cikin sandan yake karasawa wajen da yake jiyo wannan sauti,Amma bayan yaji kukan mage ta fito ta lungun da yake jiyo wannan sauti sai hankalin ya kwanta yayinda ya Mike yaje gurin da confident...

Aiko madadin yaga Mage wani katon Abu marar kyaun ganin yayi arba dashi yayinda duk fuskansa Idanu ne suka cike gashin kansa ko na Jan kasa..
Abun baida kyaun gani gaskiya danko da zakayi arba da wannan abun Koda da Rana tsaka saika Suma.

Aiko juyawar dazaiyi sai yayi Karo da irin wannan halintar sak tsaye bayansa Nanfa ya kasa rike ihun sa,Danko buga ihun yayi..
A guje ya ruga yayinda yake gudu Yana Kuma kallon baya,Aiko bai tsaya ko Ina ba sai dayaji yayi Karo da wani abun kafin ya take biriki.

"Faruq."

"Malan!!."

"Ina kuka shige Faruq tuntuni nake naiman ku."
Tambayar da yayimasa kenan inda ya basa arsar cewa.

"Mun fito naiman Kane Malan, wannan guri gaskiya nada had'ari."

Bayan yajiyo hakan sai yace dashi...

"Karka damu Malan Faruq,tunda har kazo gareni ka saki jiki Babu abinda zai same ka."

Bayan ya furta hakan sai yaga Babu abinda fadar hakan ta ragewa Faruq danko fuskarsa cike da damuwa.

"Uhmm."
Haka ya furta yayinda ya Mika mishi hannu, Faruq ko yayi saurin tambayan sa "what?"

"I mean ka rike hannuna idan har Yanzun a tsoroce kake,mu haye saman domin duba Safwan."

Faruq sauke idanun yayi ya kalli hannun nasa,Aiko baida zabi daya wuce ya rike hannun nasa Danko a tsorace yake matuka.

Bayan ya rike hannun sa saiya jashi jikinsa ya rike kafad'ar sa takamar yadda Yara suke... Taku suke a hankali yayinda hankalin Faruq kacokal Kan abinda idanun nasa suka nuna Masa.

Aiko suna cikin tafiyar sai yaji kamar hannun Bokan nada gashi da yawa,basarwa yayi Danko tunanin sa tunda yau Bokan ya fara rikeshi a hakan shiyasa yakejin wani iri Amma bayan ya sakejin abin na dadd'a karuwa sai ya d'aga Idanun sa da niyar kallon fuskar boka bakin bawa.

A tunaninku Mai zai gani daya wuce wannan aba daya sashi cikin wannan Hali na tsoro,Aiko Bayan yayi Ido hudu da fuskar wannan Abu sai ya Kulle idanun nasa da sauri ya Soma karanta Alkur'ani Mai girma.

Bayan ya bude Idanu sai ya tarar Babu kowa a gurin Nan da Nan ya juya da niyar komawa a guje nanma saiya sake gamo da wannan halitta,kwarma bagidajiyar ihu yayi ya ruga a guje ya sake komawa upstairs Danko yasan ba ta yadda zai iyya fita daganan...

Aiko bayan faruwar hakan sai Wannan halitta ya fashe da muguwar dariya Hade da tarwatsewa.

Faruq ko gudu yake sai famar Haki yake,Aiko da yayi arba da Boka bakin bawa again saiya take biriki,Danko gadon bayan Bokan yayi arba dashi yayinda Bokan ke naiman wani abun a kasa....

"Wannan ba Malan bane, wannan ma wata sigace ta munafurci....
Hakan yakeso yayi ta tsoratani har sai kwakwalwata tayi bindiga, gaskiya ya kamata na cenza hanya tun kafin ya gani."

Haka ya cenza hanya yayinda ya kyale Boka bakin bawan na waige waige Yana naiman boron sa...

Wata sanyeyyiyar iskace ta buso cikin wannan guri inda ta riske bokan,Aiko juyawar da zaiyi sai yayi arba da Naina tsaye bayan sa....

"Rana Bata karya,Bakin bawa."
Aiko da jiyo wannan batu na Aljana Naina saiya zura idanu.

"Ina fatan baka manta kalmar karshe data Shiga tsakanin mu waccen Rana ba...
Idan ka manta Bari na tuno maka Dukkanin ku Kuna da hannu afaruwan Haka kuma kowannen ku saiya biya hakan da jinin sa shin ka tuno?."

Sauke idanun Bakin bawa yayi inda yaso yayi wani Batu Amma bayan yaji da wani Darin magani data rage a jikinsa sai yayi wani Batu kasan ransa.

"Wannan garin magini zai matukar taimakamin wajen kawota kasa Dan Haka ya kamata na cire na watsa Mata."

Aiko bayan ya furta hankan ya gyada Kai yasa hannu ya Ciro maganin d'ago Idanu dazaiyi sai yayi arba da Naina dake wannan guri takai Dubu domin kowace lungu da sako ita ake gani.

Zura Idanu yayi bayan yayi abar da Naina a cikin wannan yanayi...
Itako Naina ta fashe da dariya Hadi da Kuma cewa...

"Aiko tarihi bazata sake maimaita kansa ba wannan garin maganin banzan naka sai kasan yadda zakayi anfani dashi...."

Zura Idanu dukkan Naina's din yayinda Bokan ya tashi sama yadda kasan a duniyar taurari yake kafin Nan suka sakesa ya Fadi kasa dim.

Alhaji Sunusi ko na Ganin Abinda ke faruwa,ya tuno halin daya tsinci kansa a cikin lokaci daya hade da Naina...
Aiko Nan da Nan ya tuno jakar dayayi kafa ta fada waccen Rami Nan saiya sauka cikin sanda ya barsu cikin wannan yanayi....

Takawa yayi ya sauka har first floor wajen waccen Ramin yayinda yasa Idanu sai ya tarar da jakar ciki yaso ya Ciro jakar Amma ya gagara hakan tasakashi ya kwanta ya hannun domin ya ciro jakar Amma A'a hakan batayu ba..

"Did you need some help?."
Haka Alhaji ya jiyo,yayinda ya Dago idanunsa ko sai yayi arba da mu'azz tsaye gabansa..

"Yes."

Aiko Saida ya furta hakan kafin ya tuno wannan fuska...

Mu'azz ko sauka yayi yasa hannu a wuyarsa ya d'aga shi ahankali har saida kafarsa ta daina taba kasa.

Sauke idanun da mu'azz yayi a wannan gurin ko sai Ramin ta Marne...
Alhaji Sunusi ko akayi jifa dashi...gefe guda,daga Idanu da zaiyi ya soma bada hakuri.


"Raiha! Raiha!."

"Lafiya? Dai Harun."
Haka Raihana ta furta yayinda take kokarin fitowa daga cikin Dakin Nan da suka kasance ciki.

Yi Mata nuni yayi da yatsa,inda ta Kai ganinta gurin.
Arba tayi da wata kofar wacce aka gargame da katuwar kwad'o yayinda saman wannan kofa an rubuta Stay outside.

Juyawa suka kalli juya Aiko Nan da Nan sukaje ga kofar suka balle wacce ta daukesu mituna goma kafin nan kofar ta bude.
Suka shige ciki,Aiko bayan Nan kofar taja kanta ta rufe.


*😥Sad Episode Gaskiya na tausayawa Raihana Allah dai yasa ta iyya ceto rayuwar mu'azz.....*
_Sa'annan Kuma da dukkan alamu suna gab da samun wannan aboyeyyen al'amari_

Continue Reading

You'll Also Like

17.3K 2.6K 28
සමකෝණී ත්‍රිකෝණයක ඔබත් මමත් ඔහුත් !
7K 932 36
𝓝𝓸 𝓲𝓬𝓮 𝓯𝓵𝓪𝓴𝓮𝓼 𝓯𝓪𝓵𝓵𝓼 𝓲𝓷 𝓽𝓱𝓮 𝔀𝓻𝓸𝓷𝓰 𝓹𝓵𝓪𝓬𝓮~ ✿❯────「✿」────❮✿ 𝙒𝙚𝙡𝙘𝙤𝙢𝙚 𝙩𝙤 𝙘𝙝𝙞𝙡𝙡𝙮 "𝙄𝙘𝙚 𝙁𝙡𝙖𝙠𝙚 𝘾𝙤𝙣𝙩�...
1.2M 192K 118
Type - Web Novel Author - 冰块儿 (Little Ice Cube) Genre - Comedy, Drama, Romance, School life, Yaoi Chapter status - 114 chapters 14 extras (complete...