🧟♂️🧟♀️☠️☠️🧟♂️🧟♀️
*RUHI BIYU*
_[a gaangar jiki daya]_
*RETURNS*
🧟♀️🧟♂️☠️☠️🧟♀️ 🧟♂️
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
_Kungiya d'aya tamkar da dubu._
*_SPECIAL EDIT 2021/2022_*
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*Phone no:*
+2349077974042
*REPORTS*
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*📣📣📣SANARWA SANARWA📣📣📣*
_Ga masu Bin littafin Kofar aljali littafi na biyu Ina Mai Baku hakuri game da rashin posting da kuka ga ba'ayi gaskiya abubuwa ne sukayi yawwa..._
_dan hakan Ina Mai Mika sakon ban hakuri ga fans inshallah bada jimawa ba zaku jini love you all_
*😷😷STAY SAFE... STAY AT HOME😷😷*
*FREE BOOK💯✅*
*📚LITTAFI NA BIYU*
*EPISODE_0️⃣5️⃣*
⬇
*11:00AM*
*Safwan* cewa yayi....
"Guys bayan guraren nan uku da akwai gurare shida da muke dasu wacce muka Kasa samun su,a wannan gari Dan haka zamu zubar dasu"
"Yeah haka za'ayi"
Harun ne ya furta haka,Raihana dake zaune saman Dani ko tace dasu...
"Sai kuma wani Hanzari ba gudu ba,naga wata location,da aka daina anfani dashi tun shekaru shida da suka wuce......
Shin meye za'ayi da wannan naga ka wareshi guri guda Harun?"
"Gurin zamu soma ziyarta and I want you to get ready,sabida zamu wuce yanzun nan"
Suna kan wannan maganan kuwa *Safwan* ya Saki jiki ya wuce dakin Raihana....bayan ya dudduba ya wuce next door,shigewa dakin da suka rufe mu'azz a ciki....yayi,shigarsa kuwa ya Kwarma ihu hade da rugawa waje yana cewa ku kawomin agaji....wallahi ghost na gani....
Da jiyo hakanko Raihana da Harun suka wuce izuwa garesa a guje....
A daidai wannan lokacin kuwa both mu'azz's din suka farka hatta daga hannu a lokaci daya suke duk da long distance dake tsakanin su.
Shigarsu dakin suka tarar da mu'azz din a zaune,Dan kuwa basu ma tsaya wajen Safwan din ba...
Tsallakeshi sukayi izuwa dakin......
Kura musu ido yayi hade da cewa
"What's going on,waye wancen daya fice a guje?"
Harun and Raihana suka kalli juna hade da cewa....
"How are you feeling,Yaya mu'azz" cikin hadin baki"
Kafin ya budi baki yace wani abu saiga kiran mahaifinsu ya shigo wayar Raihana,nan da nan ta daga kiran....
Shiko mahaifin nasu yace da ita....
"Mu'azz ya farka"
Dajiyo haka ta zura idanu hade da ambata *What* cikin Kara...
"Eh Raihana,yama matsa mu koma gida domin ya ganki danko yace yayi missing naki"
😲😲😲😲
*boka bakin bawa da Faruq* tsaye suke a gaban wata gidi wacce aka daina anfani da ita tun da dadewa......
Da dukkan alamu wannan ginin itace wacce Raihana da Harun ke shirin ziyarta.....
🧟♀️
Ji tayi an wuce a bayanta cikin sauri........a razane ta waiga hade da furta cewa
"Faruq jikina bai bani nan gurin ba da wani anan gurin.....gaskiya
Akwai wanda ke binmu a alabe,naji takun wani"
"Ramlah just relax,nothing is going to happen"
Haka #Faruq din ya bata ansa,cikin abinda bai wuci dakika guda ba... Gurin ta dau duhu,sararin samaniya ko ta gauraya da haduri baki wuluk.
Al'amarin data faru dasu kenan bayan sun shige cikin ginin daman cen tuntuni ramlah natare dasu har suka shige wannan gini.
Busar iska ta ratsa wannan gini,nan da nan suka zaro wayoyin su cikin aljihu suka haska fitullu....
"Shin cikin ku dakwai wanda zai iyya tuno wani abun a cikin wannan gidin?
Naga komi ya sauya na kasa gane kan ginin"
*Ramlah* ce tayi wannan batu,inda bokan yace da ita....
"Wannan kadan daga cikin tasirin sihiri aljanun kenan.....
Bazamu iyya gane komi ba dukda cewar mun taba rayuwa anan gurin amma karku damu da karfin tsafin mu ta bokaye zana binciko komi"
*Wannan ginin da suka shiga ta kasance babban hotelne a da,wacce ta shahara a wannan jaha....ta tara dakuna sama da dubu.....*
Da rufe wannan Hotel yanzu shekaru Biyarne da wasu watanni...
Ganin yadda ginin ya koma kuwa kaikace shekaru dubu yayi ba'a bude taba,wajen wannan gininma abin tsorone ballantana ka tsinci kanka a ciki....
*bokan* tafiya yake inda Ramlah da faruq suke biye dashi a baya....
Kwatsam sai bokan ya taka biriki ya tsaya cek kamar daukewar ruwan sama.
Nan da nan suma sukayi hakan inda Ramlah tayi saurin tambayansa cewa....
"Malam yadai?"
Alamar tayi shiru ya nuna mata.....nanfa ya sako hannu cikin jakar dake rataye a kafadar sa...
Ciro garin magani yayi cikin wannan jaka,inda ya watsa cikin wannan daki gabar da yamma sannan ya zubar da sauran akasa,kana kuma ya ciro wata katotuwar *kwai* mai kama dana maciji ya dire kan garin maganin...dake kasa.
Nanfa ya soma surutan sa na tsafi yana karanto muggan kalaman sihiri....
Wannan hadiri kuwa sai dadd'a dugunzuma yake yana dawowa jajir....
Duk gurin ta dau jar haske.....nan aka soma tsawa....
Cen sai bokan ya daga kai ya kalli fuskar Ramlah yace da ita..
"Aikin ki anan guri shine ki zauna anan,domin ki tsare wannan koyi....(egg)
Sannan ki sani duk wani motsi da kika jiyo karki kuskura ki sauke idanun ki a kan wannan kwai, sa'annan duk halin da wannan kwai ta shiga kiyi gaggawar sanar damu"
Bayan yagama furta hakanne Ramlah tace dashi.....
"Ah wai duk akanmeye kake wannan bayanan naga bani kadai zan tsaya a nan gurin ba ko, kodai ni daya zan zauna anane kake nufi?"
"A'a da jatumarki zaki zauna?"
Haka faruq din ya furta inda Ramlah ta buga Masa harara, bokan ko yace.....
"Karmu Kaiga wannan,please Ramla be serious about this, this is the only way to find the truth believe me."
Bayan ya furta hakan ya mika mata wata yar mitsitsiyar garaurawa,bayan ta ansa daga hanunsa sai yace da ita ...
"Kiyi gaggawan kad'a wannan karaurawa daga zarar kin shiga halin kaka nikayi"
*AL'AMARIN* Mu'azz da abbansa ko kaiwa gidan sukayi inda suka tarar da *Harun* *Raihana* dakuma *Safwan* suna dakon zuwan su...
Shigarsu falon *mu'azz* ya soma jujjuya idanu alamar jikin sa bai sake da wannan gurin ba,cewa yayi dasu...
"Sister su din su waye wayennan?"
Haka ya furta yayinda yake nunasu Harun da yatsa.....
"Su din ai abokan tane,and kamarfa kun tamba haduwa indan baka manta ba"
Haka abban nasu ya furta inda yayi saurin cewa.....
"Never,we haven't meet before....."
Hakan ya basu ansa yayin da ya hade rai....karawa yayi da cewa
"Zan Haye izuwa dakina,ina bukatar hutu so don't bother me"
*"Wait!!!!"*
Cikin hadin baki suka furta hakan,inda mu'azz yayi saurin tambayan su what?.
"Zayafi idan ka zauna anan falo domin air condition naka ya lallace"
Haka Raihana ta furta Harun ko shima yace dashi....
"Sannan toilet naka ta samu matsala"......
"And Also kofar dakin ka ta kulle ta ciki" karashe maganan safwan yayi da hakan,inda Raihana and Harun sukayi furucin *what* cikin hadin baki.
Haka suke ta surutu a downstairs inda wannan murya tasu tana kaiwa dakin mu'azz.
Mu'azz bayan ya saurari komi ya yunkura hade da murmusawa karasawa yayi jikin madubi....
Hmm abin da ya dauremin kai shine ta cikin madubin suffar Nainah ake gani amma kuma wanda ke tsaye gaban madubin mu'azz ne.🤔
Downstairs kuma tura dayan mu'azz din sukayi izuwa dakin Raihana dukda cewa bai kaunaci hakan ba amma lallai lallai suka sakashi ya amince.
"Safwan kai zaka tsaya tare dasu ukun ka kula dasu,i mean both mu'azz din da kuma abba"
Haka Raihana ta furta inda Harun ko yace dashi.
"Mu kuma zamuje mu naimo tarihin."
"What? You gotta be kidding me,ni daya na zauna da wayen nan,no no no ya kamata ku cenza shawara i can't wallahi"
Haka ya furta inda Raihana tace "daddy zai kula da kai amma karka sanar mishi komi kaji.....sai Bayan mun dawo."
Karashe maganan ne sukayi yayinda already sun shige mota,Safwan din kuma na tsaye a waje yace dasu "already naji,sai Kun dawo"
Aiko tafiyar su ya Ciro wayar sa ya soma danne danne ciki... Hade da murmushi.
Al'amarin Faruq kuwa tsaye take yayinda boka bakin bawa ke kokarin sa magani a gurin,inda Faruq din ya Sami sako ta wayarsa.
Da ganin sakon ko ya taka izuwa gurin da Bokan ke kokarin saka maganin yace dashi.
"Suna Hanyarsu ta zuwa Nan gurin,kaga kenan plan namu na tafiya yadda muka tsara so get Ready."
Murmushi Bokan yayi Hadi da cewa
"Aha Barsu suzo domin su kawo karshen wannan kitimurmurar."
Idan muka Laika floor na kasan karshe ko zamu tarar da Ramlah zaune ta kurawa wannan Kwan da boka bakin bawa ya Bata.. Idanu.
*Readers na Tambaye ku lokacin da akayiwa Ramla allurar bacci shin maiya faru bayan Nan?.*
Aiko abinda ya faru waccen lokacin Abu ne Mai sauki domin farkawar ta keda wuya Bokan Nan da Faruq suka shawo kanta hade Kuma da jaddada Mata cewa idan ta kuskura ta sanar da wannan *Boyeyyen al'amari* zata rasa ranta domin Aljanu basa cika alkawari,shine dalilin dayasaka ta amince harma ta bisu wannan guri,domin tana zanin zata Sami tsaro a tare dasu.
Al'amarin Safwan ko tsaye yake a Tsakiyar falo inda yayi shiru Yana ta nazari game da Su Harun,daga karshe kuwa yayi magana kasan Ransa kamar Haka.
"How can I be so sure,Harun zai kasance cikin koshin lafia? Gaskiya ya kamata nabi Bayan su,Amma Kuma sun umurce Ni Dana Zauna tare Mu'azz, what can I do right now."
Bayan wannan sai ya daga Idanu a kalli dakin Raihana wacce suka saka 1st mu'azz sa'annan Kuma ya daga Idanu ya kalli upstairs...
"Gaskiya Ina cikin chakwakiya."
Takawa yayi izuwa dakin da abban Raihana ke kwance,Kuma ya gane kwancen yake ne Bayan ya bude kofar a hankali ya Laika ciki bayan nanko ya juya izuwa dakin Raihana inda nanma ya bude kofar yasa Ido..
Tadda mu'azz yayi kwance shima akan katifa Nan saiya koma baya Hadi da Jan kofan ya kulle shi aciki.
Murmushi yayi Hadi da cewa...
"They are both sleeping, wannan itace damar da nake da shi domin na fice daga Nan."
Aiko bayan ya gane dukkan ninsu bacci suke ne yasaka shi barin gidan yabi bayansu Harun....
Aiko fitarsa keda wuya wannan mu'azz dake dakin Raihana wacce yake zaton bacci yake, ya bude Idanu..
Mikewa yayi Kai tsaye yajega kofar yasa hannu da niyar budeta Jin kofar ya rikene ya saka shi murmushi Hadi da zura Idanu wacce zura idanun da Yayi ne ta basa karfin ikon hango abinda ke bayan Wannan kofa. *Tirkashi mu'azz dake upstairs hoton Nainah yake hagowa yayinda ya tsaya gaban mirror sai Kuma gashi wannan danake tsammani shine na gaskiyan shima yayi wani abun rud'arwan*
Gani yayi Babu kowa a falon Haka ta sakashi yabi jikin kofar ya fita daga dakin,Nan sai gashi ya baiyana a wajen dakin Nan da Nan ya wuce saman upstairs da niyar zuwa waccen dakin wacce tunkan ya karasa wannan guri mu'azz daya kasance cikin Dakin yasan da abinda ke faruwa.
*Ramla* zaune take sai taji sautin sawun mutum na dinfarowa inda take,Aiko harta so ta waiga but saita tuno da fadan boka bakin bawa...
*Karki kuskura ki sauke idanun ki a kan wannan Kwan*
Nan saita sake bushewa ta gagara motsi a tunaninta Aljanu ne suka fara bayyana.
Indan muka gangara bangaren da Wannan sautin ke fitowa ko zamu tadda Harun ne tare da Raihana ke taku inda Raihana ke cewa.
"Wannan babban guri ne Harun,a tunaninka ta wace bangaren zamu fara dubawa."
"Raiha Gaskiya nima kaina ban San ko ta Ina zamu fara ba Amma Ina ganin zamu haye izuwa Sama domin mu fara binciken tacen."
"Mai yasa sai saman why not mu fara daga Nan."
Fadar Raihana kenan, inda Harun yace da ita "kawai Ina ganin zamufi dacewa idan muka fara a saman."
"Okay shikenan muje."
Aiko fadar hakan keda wuya sai sukajiyo karar fadiwar tangaran Nan da Nan suka juyo ganin su izuwa gurin hade da haske fitular..
"Hello is anyone there?."
"Raihana karki wahal da kanki,domin wannan guri ta Dade da daina aiki,Kinga Dole beraye suyi yawa Dan Haka kizo mu fara dubawa Danko bamu da ishesshen lokaci Kuma Kinga hadiri data gwarwaye sararin samaniya."
Dajiyo hakan sai ta juya tace dashi "alright let's go." Aiko tafiyar su keda wuya sai Safwan ya baiyana a gurin yayinda ya dafa kirji yayi ajiyar zuci.
"Thank God basu ganni ba....
Amma wannan gini mashiga daya gare ta, and Ina bukatar na shike ciki kafin su suyi."
Bayan ya furta hakan yabin bayansu a labe.
Aiko hango Gadon bayan Ramla ne yasa Harun ya rude Hadi da Kirawo sunanta cikin tsauri.
Ramla ko da jiyo hakan ta zura idanu Hadi da dauko karaurawa ta rike a hannu.
yayinda Harun da Kuma Raihana ke tunkaro ta sai Wannan kwan ta soma motsawa a hankali..
Ganin hakane yasa Ramla ta sake tuno da batun Bokan Nan.
"Wannan Kwan ita zata banbanta Aljani da Kuma bil'adama Dan Haka karki kuskura ki sauke idanun ki akan sa."
Bayan ta tuno hakan sai ta sake rike karaurawar da karfin tsiya kamar zata buga...
Aiko da suka dad'a kusanto ta Kwan ta soma juyawa da karfin tsiya Kai kace fanka Aiko dafata da sukayi sai Kwan ta fashe yayinda jini ta fesa ma Ramla a fuska.
Ramla Bata da zabi daya wuce ta kada wannan karaurawa,Aiko yin Haka keda wuya karar takai ga Bokan Nan inda yayi wub ya Ciro wata madubi acikin jakar dake rataye a wuyarsa..
shafar madubin yayi inda yin hakan keda wuya yayi arba da wani guri Mai hudun gaske madadin Hoton Ramla..
"Tirkashi."
Abinda ya fito daga bakin Bokan Nan kenan inda Faruq yayi saurin jefo Masa tambaya kamar Haka.
"Lafiya dai?"
"Ina kaga lafia na kasa ganin komi."
"Mai kake nufi da ka kasa ganin Komi?"
"Kamar yadda na fada na kasa ganin Komi to Haka ne na kasa ganin komi,da dukkan alamu Ramla tayi jinkiri wajen kada wannan karaurawar."
*RUHI BIYU*
_[a gaangar jiki daya]_
*RETURNS*