A kitchen kuwa cous-cous da miyar ganye tamusu wanda mai yaji a cous-cous ɗin yayi wara-wara dayake tirarawa tayi,miyar ganyen kuwa yasha stock fish da tantaƙwashi sai ƙamshi ke tashi duk yacika parlourn ,kunun aya mai kauri tayi wanda yasha madara da kwakwa ga ishashshen dabino yayi fari kyel tazuba a babban jug tasa a ɗan karamin fridge ɗinsu dake parlourn,ta gyara koina na kitcen ɗin kamar ba'ayi komaiba tana gamawa takalli agogon hannunta taga bakwai saura kenan taci awa ɗaya a girkin datayi,jera abincin tayi akan ɗan ƙaramin centre table ɗin dake parlorn tashiga banɗaki ta ɗauro alwala,Sallah suƙayi su duƙa suna zaune suna azkar har aƙa ƙira isha ɗon haka suka gabatar daga haka aka hau fira ana kallon film ɗin friends but married sunmaida hankali sosai suna kallo don film ɗin akwai daɗi sosai ya haɗu,Falmata ce tace"wlh ku saƙƙo aci abincinnan donni gaskiya yunwa naƙeji,Saleema tace"yunwa ko ƙwadayi ba,oho de cewar Falmata,abincin sukafaraci suna zuba santi Falmata harda lumshe ido tana korawa da kunun aya mai sanyo,su Haleema duƙ kaucewarsu saida suka yaba da abincin don ya motsa musu kunnuwa,duk yawan abincin saida suka cinye tas Saleema wacce tatashi tanata musu dariya don itakam ba ma'a bociyar cin abinci bace,kallo sukaci gaba dayi har ƙarfe goma tukun sukaje suka kwanta,dayake katifar tasu babbace kawai suka hau suka kwanta".

Dukansu sunyi bacci face Haleema wacce taketa tunanin yadda plan ɗinsu zai tafi batare da wata gargadaba tana ƙoƙarin ɗaukar wayarta donyin chat taji ringing wayar Saleema,hartakai hannu zata ɗauƙa sai Saleema tatashi taɗau wayar batare da talura da Haleema ba,picking call ɗin tayi cikin ƙasa-ƙasa da murya haɗe da shagwaba  tace"Hayatee sai yanzu ko,dariya yayi yace"afwan Sururi yau sam munshiga kasuwane raka wani abokinmu siyayya sai ƙarfe tara muka dawo bayan nayi wanka naci abinci shine na kwanta na huta bacci ya ɗaukeni,kinsan meyasa banci gaba da baccin ba?,cikin murmushi tace"a'a,yace"saboda banjin muryarkiba babu yadda za'ayi nayi ɓacci harnakai safe batare da naji muryarnan taki mai zaƙi ba,wannan karon murmushi take mai ɗan sauti wanda ya tabbatarwa da Haleema da Saleem take waya kunne ta baje donjin firar dasukeyi,ganin suna bacci yasa Saleema hankali kwance tasaki murya take magana,tace"wlh nima sam nakasa bacci da kwanciyar hankali saboda banji muryarkaba namaka msge ba reply,"kinsanme bari inmiki reply ɗin messagw ɗinki ta bakina,a saƙonƙi kince kin mallakamin zuciyarki naja Linza minta,sannan kin buƙaci na riƙemiƙi amana karna haɗa soyayyarki da wata toh buɗe kunnuwanki kiji amsar saƙonki ni Saleem Tameer na amshi amanarki ko bayan ranki duk matan duniya abayanki suke sannan  ba linzamin soyayyarki kawai zanjaba harda ta rayuwarki ,Saleema kobabu komai tsaƙanina dake ke ƙanwatace mafi soyuwa agareni wanda zan iya bada rayuwata akanki balantana soyayya tashiga tsaƙanina dake matsayinki da darajarki sunƙaru a zuciyata,wlh Saleema bazanso wata amace ba kina raye,numfashina yana bugawane tare da ƙara sonki a zuciyata,soyayyarki wata baiwace daga Allah bana ganin kowacce ƴa mace a duniya koda kuwa baƙyagun inde kina raye bana tuna komai dangane da soyayya inba nakiba,fatana kisoni akowane hali ko ƙawa ko zugi ya taɓa soyayyar dakikemin,Saleema shiru tayi kunnuwanta,zuciyarta da ruhinta na ƙarbar kalaman soyayyarsa cikin shauƙi tace"insha Allah zansoka yau da gobe harma ƙarshen rayuwata babu me zugani akanka Hammana kai ƙaɗaine burin rayuwa da raina,zan rayu dakai tare da soyayya kuma acikin kowane hali zan rayu dakai,ngd sosai Saleema Allah yabarmin ke,amin nima Allah yabarmin kai,naga tsatsona daga gareka,ina alfahari dakai,sosai fa sukasha kalaman soyayya har wajen ƙarfe 12 tuƙun sukayi sallama cikin bege,soyayya da shauƙin juna,itakuwa mutuniyarku zuciyarta kamar zata faɗo don baƙin ciki saboda tanajin firarsu taji kalaman da suketa zubawa juna bacci sam ya kauracewa idanuwanta ,a ranta tana raya dolema taga bayansu duk sunbi sun hanata sukuni a rayuwa,haka ta kwanta ba bacci har asuba,5:00am Saleema ta tashi sanadiyyar wayarta dake ringing cikin sakalci da shagwaba tace"haba mana Hayatee baka barni nayi bacciba jiya kuma ina kwanciya saika tasheni,cikin son shagwabarta yace"am sorry Babyn Hamma Saleem lokacin sallah yayi kiyi hƙuri kutashi kuyi tunda yau sunday bakida karatu saiki koma bayan kinyi sallah kinji Baby na yaƙarasa zancen cikin shagwabe murya,baki ta turo kamar yana ganinta tace"to naji zantashi amma naɗan ƙara baccin koda minti talatinne sai in tashi,dakyar yasa ta tashi tana zumburo baki,dariya yayi yace"ki zumɓuramin wannan ƙaramin bakin zamu haɗu dake ne,tace"eh aikaima kanayi taƙarasa maganar tana kallon Haleema wacce ta tashi fuuuda fushi tayi banɗaki tare da buga tsaƙi,katse wayar Saleem yayi yana murmushi saboda yana bala'in son shagwaba,sakalci da tsoro irinna Saleema,itakuwa Haleema tana shiga banɗaki tace"shegu yana wani lallaɓata ta tashi saikace kabari ɗaya za'akaisu mtsww taƙara jan wani tsaƙi tace"sunbi sun hana mutum bacci,tohm Fans kunjitafa wai sun hanata bacci kede kifaɗi meyahanaki bacci ah to,alwala tayi tafito fuska a ɗaure,Saleema ce ta tashi Falmata da Fareeda daga haƙa tashige ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah,suma sallah suƙayi sukayi azkar da karatun qurani banda Haleema da Fareeda da suna sallama suka kwanta musamman su o'o daba'asamu bacciba,tana ajiye qur'anin zata kwanta Saleem yasake ƙiranta,ɗagawa tayi cikin muryar jin bacci tace"Hamma Saleem bacci zanyifa,yace"naƙira nasaki baccine ai,tace"yauwa Baby Hamma kasani mai daɗi,kalamai yafara mata masu daɗin sauraro nan danan bacci yayi gaba da'ita saida yaji numfashinta na sauƙa a hankali ya kashe wayar yana murmushi,Haleema wacce harta fara bacci taji Saleema na shagwaba ta buɗe ido tana saurarensu harsaida Saleema tayi bacci taji Saleem ya mata kiss ya kashe wayar tukun itama takulle idonta donyin bacci amma inaaa zuciyarya tamata nauyi da ɓaƙinciki dakyar bacci ɓarawo ya ɗauketa,HH Haleema kintaro aiki aradu,Anti Fauziya,Maman Afnan da Maman Ahmad ku kawowa Haleema maganin bacci kozata samu bacci mai ƙyau mana hh😒😄.

Sai ƙarfe goma suka farka banda Saleema wacce jaruma ce gun bacci ,Falmata doguwar riga armless tasa tayi hanyar kitchen ,ruwan zafi ta dafa musu wanda yasha kanunfari da citta ta soya irish patoto da kwai tamusu warming ɗin pepper soup  ɗin da Saleema tayi jiya ta jera a ƙasa a parlour tashiga ta wanke banɗaki tayi wanka har lokacin Fareeda da Haleema na zaune amma harsunyi wanka sun sa kaya,tana fitowa ta tada Saleema tana cewa to sarauniyar bacci kitashi tunkan yunwa yajiyoki kije kiyi wanka kizo muci abinci tunkafin Mijinki ya ƙira ya balbaleni nabar masa mata da yunwa,wata uwar harara Haleema ta gallara mata wanda sarai Falmata taganta anma ta basar, Saleema ta miƙe tana turo baki tashige bathroom,murmushi Falmata tayi taciro mata da kaya irinnata,riga pink da wanda three quarter blue sai hular sanyi itama blue ,harara Fareeda tamata tare da cewa shegen iyayi harda wani ciro mata kayan dazata saka kowa yasata,Haleema tace"kyale shegiya fuska kamar ta aljanu duk suna maganarsu ƙasa-ƙasa ne,Fareeda tace"bari muje parlour mujiraku daga haka suka wuce parlourn suna yatsina fuska,tana fitowa daga wanƙa tashafa manta tare da fesa turaruka tasa kayanta suka fito kamar ƴan biyu,zama sukayi donyin breakfast ,suna tsaƙa dacin abinci wayar Falmata yayi ringing picking tayi tasa a handsfree ta ajiye tare dayin Sallama,amsawa yayi yace"ina Baby na,gatanan Hamma Saleem tana breakfast duk yau tabarmin aiki tanata bacci kodan dama inakayi waya dakai da daddare tofa washegari aiki yasameni dariya yayi yace"karki damu dake zamu tare don zamu rigaki aure,tace"tabdijam lallema aikaikam aka kaimaka Saleema wlh duk wanda yaje gidanka yasiyama kansa takaici don sai ya gwammace baijeba,dariya yayi yace"kenan sharri zakimana tace"nida aƙemin practical anan inkuna waya ko inkazo Saleema tamantani tab rufamin asiri aino ko zanje gidanku sai bakanan inba hakaba nasna ko ruwa baza'a baniba,Saleema ce takaimata rankwashi tare da ƙarbe wayar tace"kyaleta kar kowama yazo in za'a kainima su huta kazo ƙadaukeni mu tafi abinmu ko,yace"sosaima don ba a nigerai zamu zaunaba, baride kigama cin abincin mayi waya anjuma,tace"toh Allah yaƙareminkai daga dukkan sharri,amin my Wife katse ƙiran tayi taci gaba dacin abincin suna gamawa ta tattara kwanukan ta wanke tadawo akaci gaba da fira,anan Haleema ke sanar musu gobe fa zasu koma don  aranta batajin zata juri kwana huɗu Saleem da Saleema suna cusa mara ɓaƙin ciki,Falmata da dariya keson kufcemata don tagano abindake damunta tace"amma da kunce kwana huɗu zakuyi meyafaru zaku koma,harara ta watsa mata ƙasa-ƙasa tace"wlh Mummy ce taketa damuna mu dawo tunda munzo angaisa,Saleema tace"to shikenan Allah yakaimu goben lafiya duka suka amsa da amin,Haleema aranta tace"shegiya so takema na tafi,tayi kwafa aranta tana girmama shirinta na gaba.

Tohm masu karatu anmin uzurin typing ƙadan,kunsan jiki da jini ga ayyuka.

Share.
Comment.
Vote.

Young-Novelist✍️
Novel ɗina na kudine

KANKI KIKA CUTAWhere stories live. Discover now