shin mace mai ciki in jini yazo Mata haila ne?
jinin da ke fita ga mai ciki, baki,ja da kauri ko babu kauri duk ba haila bane, jinin ciwo ne (istihala) shine magana mafi inganchi.
Malamai sun yi saɓani dangane da mai ciki cewa idan ta ga jini haila ne ko ba haila ba ne?
Na farko,suka ce mai ciki ba ta yin jinin al'ada kwata-kwata. Saboda haka idan aka ɗauki wannan ƙaulin, (maganar) duk jinin da ya zowa mai ciki, jini ne na rashin lafiya ba zai hana ta ibada ba. Don haka za ta wanke wannan jini ta ci gaba da yin ibadarta kamar yadda ta saba. Kuma wannan shi ne abin da mafi yawan likitoci na duniya suka tafi a kai, kuma ita ce mazhabar Malam Abu Hanifa da Imamu Ahmad da wasu manyan malamaiNa biyu, suka ce ana iya samun mace mai ciki ta yi jinin al'ada, duk da ba kasafai a kan samu ba, amma kowacce mas'ala akan sami abin da yake ya fita daban. Akan sami macen da ta fita daban a cikin mata, ga ta da ciki kuma tana al'ada. Sai dai a nan idan an sake ta ba za a yi la'akari da cewa sai ta yi jini uku ba. Tun da dai tana da ciki lallai sai ta haihu, don haka ba za a yi amfani da wannan al'adarta ba a wajen idda ba, sai dai a yi amfani da ita a wajen ibada. Abin nufi sai bayan wata uku ko bayan wata shida, idan ta ga jini yana fita yadda ya saba zuwa a lokacin al'ada da kalarsa da lokacinsa yadda ta saba, haka take da ciki ma tana al'ada. Wannan sai a yi mata hukunci da abin da ya bayyana daga ɗabi'arta da halinta. Saboda likitoci sun ce ba a yin haila idan mace tana da ciki, ga shi ita kuma ta yi ɗin. Amma fa da wuya a sami mace tana da ciki kuma tana yin haila. Idan kuwa an samu ɗin sai a yi mata hukunci da abin da ya bayyana a gare ta, domin ita ta bambanta da sauran mata: ga ciki ga al'ada. Ana samun 'yan kaɗan mata masu yin wannan, amma dai asali shi ne, idan mace tana da ciki ba ta jinin haila.
YOU ARE READING
hukunce-hukunce da mas'alolin mata
Spiritualhukunce-hukuncen al'ada menene istihala(jinin ciwo) ? menene kudra da sufra(brownish discharge)?da hukunce hukuncen su menen nifasi, haila da mas'alolin su ? shin menene alamomin tsarki? ya akeyin wankan tsarki? ya ya kamata ace mace ta tsaftace...