maleek 59 _ 60

539 40 0
                                    

  
   59 _ 60

Not edited

Dr murad yana dawowa ranar aka Sanar dashi akwai emergency baiko huta ba ya wuce Asibiti direct kawai,

Saida ya dubbuba marasa lpian sa sannan ya hau duba file din maleek rubuce rubuce yayi a tarkada y fitowa daukeda da takardar ya iske su mom zazzaune suna zaman jiran tsammani,

Gaisuwa sukayi a mutunce yace plss ana son wani nasa  yayi signing sbda zuwa gobe zaa masa aiki, if possible his dad or his mom,

Mom da cikinta ya duri ruwa tamike kafaffunta na rawa tace nice mahaifiyarsa, toh muje kawai yace yayi gaba tana biye dashi abaya sit ya nuna mata yace have a seat zama tayi tazuba masa ido kana ganinta kasan ba cikin natsuwarta take ba,

Mrs zulaikha right, gyada masa kai tayi, yayi gyaran murya tareda cewa calm down madam insha Allah he will be alright d problem here ix kansa yasamu problem sanadinyar buguwa daya yi, sai kuma sakamakon bincike da nayi yanuna yana fama da depression meaning ciwon damuwa in addition kuma yanada ciwon zuciya ma so abin yayi affecting dinsa sosai, Ammam insha Allah he will be fine.

Inalillahi wa inna ilaihi rajiun nashiga ukkuna yaushe duk wadannan cuttuttukan suka kamasa har suka masa yawa haka,

Kallonta kawai murad yake Amman as a mother taya zaki ce baki San danki na daukeda irin wadannan cuttukan ba, girgiza Kai kawai yayi Mike da niyar fita.

Itama mikewa tayi tana tafiya ahankali kamar bata son taka kasa jikinta duk yayi la'asar da zancen maleek,

Daren Ranar babu wanda yayi bacci cikinsu kowa da abinda ke ransa mussanman meenal karshe da taga baccin ya gagara mikewa tayi tadauro alwala tacigaba sallolinta tana mika bukatunta gurin ubangiji.

Dukansu suna zazzaune akan waiting chairs da ke asibitin wanann karan harda da su mamy da abba,

Maleeka ce ke rungume da meenal da keta barzar Kuka ba kakkautawa kowa ya kifa uban tagumi kana ga ninsu de kasan suna cikin tashin hankali.

Murad da yayi shirinsa tsab nashiga dakin theatre dashi da wasu doctors guda biyu shirya maleek shima akayi cikin green din kaya aka Dora akan stretcher an lullube shi da farin kyalle,

Fitowa sukayi kowa da mask Sanye a fuskar su idonsu kawai kakegani turo shi sukayi zuwa dakin theatre, wucewa sukayi ta gaban su mom,cikin tashin hankalin mom tamike tabisu aguje Amman kafin takawo har sunshige an kulle kofar tana zuwa aka Dakatar da ita komawa tayi kwalla na sharara kamar an bude famfo,

Zuwa tayi gaban meenal da idanunta da sukayi jajur muryarta na rawa cikin kuka tace meenal nasan nacutar dake nasan bazaki yafeminba Amman ina rokonki da ki yafemin ko narage nauyin dake kaina, nasan nazama uwa mai son zuciya da kuma zalunci na gane kuskurena dan allah ki yafemin kimin alkawarin Idan maleek ya tashi zaki aure shi kuyi rayuwa mai inganci mai cike da farinciki tafada tana dukewa,

Duk yanda meenal Taso yin magana kasawa tayi saidai takifa kanta a cinyar tana shiga wani sabon babin kuka.

Matsawa  gaban su Abba tayi tana don girman Allah ku yafe min nayi kuskure nashiga ukkuna wallahi hakkinkune da na alummar Dana zalunta ke bibiyata ku yafe min ko na samu rangwame da kuma saukin abinda nakeji a zuciyata tafada tana kwacewa dawani irin kuka mai taba zuciya da kyar mamy tadaga ta tareda rungume ta tana ya isa haka hajiya komai yawuce munyafe miki fatar mu kawai Allah y tashi kafadun maleek.

Muhassin mikewa yawuce masallacin asibitin ya daura alwalwa ya cigaba da sallah ko ze samu sauki abinda ke zuciyarsa.

3hrs laters

Mom nahango kamar Mara hankali tana ta safa da marwa a kofar theatren,

Abba da mamay sun kifa uban tagumi suna jiran fitowar likita, meenal kuwa idon nan nata Itada meenah sukoma kamr jini sbda tsabar ja na kuka da suka ci, meenal har dishi dishi take gani ga wani matsanancin ciwon kai dake addabarta.

Adduah kawai sukeyi Allah yasa asamu nasara, muhassin da yadawo shima yana nan zaune kamar kurma ba uhm ba uhuhm

About 40mins sukaga an bude kofar theater room din doctor Williams ne yafara fitowa fuskar nan tasa babu annuri saiga doctor usman nabiye dashi sauke mask din fuskar su sukayi da niyar shiga office dinsu,

Jim an bude kofar atare suka Mike gaba dayansu cikin tsananin tashin hankali, mussanman da sukaga fusko kin doctors din are not encouraging,

Murad da yakasa fitowa tsaye yayi sbda baisan yanda ze fara cemusu sai dai suyi hakuri ba,

Da kyar yayi karfin halin fitowa jikinsa a sanyaye ganinshi yasa duk sukayo kansa aguje, maleeka da takasa magana kallonsa kwai takeyi da jajayen idanunsa, kansa a kasa ahankali yace

"Am very sorry but he is late"yana gama fada yayi saurin wucewa office dinsa sbda kwallan dake neman fito masa,

Meenal da Jim kalmar da murad yafada yasa ta daskarewa tsaye,meena dukawa tayi agurun tana wani irin kuka mai Sosa zuciya,

Mom kuwa aguje tafada dakin taga maleek kwance anrufesa da wani farin kyalle ya kice kyallan tayi taga idanunsa a rufe durkusa tayi tana kuka sosai nooo maleek bamuyi haka dakai ba plss karkamin haka yazaka mutu ka barni plss u are my only son ka tashi Dan Allah durkusa tayi gurun tana barzar kuka kamar Ranta ze fita, na cuci kaina shine abinda take ta maimaitawa mamy ce tashigo da kyar ta kamata tana son fita da ita Amman sai tirgewa takeyi da kyar aka fito da ita bajewa tayi akasa tana kuka tana sokana sai kace sabon kamu

Wata matace dasukazo asibiti Itada mijin ta ta duka tana kiyi hakuri madam sai kace ba musulma ba kidauki kaddara dukkan mai rai mamacine kiyi hakuri Dan Allah kimasa addua, tana gama fada tamike tawuce cikeda tausayin mom.

Muhassin ne yashiga dakin Amman kafewa  yayi abakin kofa yakasa shiga cikin sbda kafafunsa dake rawa kifa kansa a bango yana kuka yanajin zuciyarsa na masa zafi abba ne yadafasa akafada tareda Dan bubbugawa alamun lallashi, ya maleek zatafi yabarni nikadai yana tunanin zan iya cigaba da rayuwa bashi nan, yafada yana kifa kansa akafadar abba shima abba kwallan idonshi kawai yake sharewa,

Muhsin dazuwan sa kenan kasar yashigo agigice ganin kowa na kuka yasa shima baisan sanda kwalla suka fara fito masa ba ko magana shi yakasa zama kawai yayi don kafarsa dake bara zanar yardashi.

Maleeka zaune  takw ko tashi takasa Banda innalillahi wa inna ilaihi rajiun babu abinda take maimatawa sai kuma kwalla dake ambaliya a idonta,

Wata razanniyar kara da sukajiyo yasa duk suka juya cikin sabon tashin hankali ganin meenal kwance a kasa kamar mattaciya, Wanda ita sai a lokacin kwakwalwarta tagama detecting abinda ke faruwa, aguje suka nufe ta cikin firgici da tsananin tashin hankali.........

Mrs Abdool ce

"MALEEK"Where stories live. Discover now