maleek 39_40

734 45 4
                                    

39 _  40

"Da shirinta tsab tafito Sanye da hijab don zuwa yi musu cefene gurin mamy ta karbi kudin bayan tagama mata lissafin abinda zata siyo.

Tafito taga mama zaune tsakar gida tana fice gyada, ko kallon gefenta batayiba bare ma tasaran gaisuwa wucewa tayi har takai kofa tajiyo muryar mama tana to "zaatafi gantalin da aka Saba ko mude kubari saikun koma gidan naku kar ajamana abin kunya a gida ehe"

Meenal de bata juyoba kuma kokadan bata damuba don tasaba da irin wadannan maganganun na mama harda wanda sukafisu ma.

Tanafita ta tsaida Keke napep direct kasuwa tawuce ta musu siye siyen su harda su kwai,Irish,indomie Dade sauransu tana gamawa wani yaro yakowo mata bakin titi tabashi hamsin.

Tadade tsaye bakin titin bata samu abin hawa ba wata arniyar jibce kirar highlander tawuce gabanta, har tawuce kuma motar tayo reverse zuwa sai tinta itade kanta gefe bata juya ba, yayi minti biyar kafin ya sauke glass din kasacewar shi tinted sai da yagama kare mata kallo tukun

Sallama yamata yana Ina zuwa haka da kaya,
Jin ya dameta da suratai yasa tajuyo ta kalleshi a karon farko sai aloakcin taga ashe ma ba yaro bane don babban mutunne amma kana ganinshi kasan kudin sun zauna masa don babu alamar talauci attareda dashi hasalima yana zuje glass din daddadan kamshine mai gauraye da sanyi ya bugeta, saurin dauke kanta tayi gabanta na faduwa, Dan gaba ta matsa daga Inda motar take ahankali shima ya taka motar zuwa Inda take "kinga yan mata kiban nombanki sai muyi mgan kokuma kimin kwatance gidanku sai nazo anjima, yana gama mgnar dede mai napep yazo wucewa tayi saurin tareshi ta shiga ya zuba mata kayanta tace "muje" Alhaji ganin tawuce ma ya tabe baki yana nasoki da murad dina  Amman as she wish fizgar motarsa yayi gaba yabar wajen shima.

Tana sauka gida tabashi kudinshi ta kwashe kayanta da daddaya tana shiga dasu, kawu ta tarar a tsargida yana sauraron radio Dan durkusawa tayi tana "sannu da gida baba", "sannu meenal andawo", eh "baba to barka dazuwa"

Saidata tagama shigar da kayan gidan tawuce dakin mamy tana nuna mata abinda tasiya

Kawu  dake zaune wayarsa ta dau Kara, dubawa yayi yana dauka da hanzari,

"A'a alhajin Allah kenan kwana biyu ya gida ya aiki kuma"

Daga  dayan bangaren akace: "Alhamdullh malam bukar ya naka iyalan dama nashigo garin jiya ne nace in kana nan nashigo mugaisa"

"Ah Ina nan Alhaji ka shigo kawai"

"To masha allah zuwa anjima zanshigo kamar da yamma"

"To Allah ya kawo ka lpia"

Yana kashe wayar ya kwala ma falmata kira, karaso tayi tana wannan kira kuma haka malam lpia kuwa,

Lapiyar cemtakaeo haka maza je kifara shiri Alhaji bello mainasara ne yamin waya yashigo gari,

Falmata da tabata fuska da tawashe hakora Kai yaushe zaizo to kaga daman nayi shinkafa da miya je siyo salad a hada masa kasan tuwon girma miyarsa nama,

"Hakane bari  infita yanzu fadar kawu"

"To harda Dan lemon na kwali duk kahado tafada tana mikewa"  

Bayan kawu yafita babu dadewa saigashi yadawo daukeda leda, ledar falmata tafara budewa tana Kara washe baki, babban kwalin exotic ne da ruwan roba sai yar kaza dakuma salad,

Dauka falmata tayi tanufi cikin kitchen cikin kankanin lokaci tagama hado komai, har kulas sabba akasaka Wanda akafara saima adama na aure.

Mama tashigo daki taga adama kwance tana waya, ke  dalla tashi kiyi wanka kiyi shafa kazama kawai, mama name kuma, mama datayi kasakasa da murya tace Alhajin Abuja abokin babanku zezo kika sani ko a dace koshi ko dansa,

"MALEEK"Where stories live. Discover now