BARADEN DAKARU

730 48 0
                                    

nan aka runka basu horo mai tsananin wahala.
lokacin da suka kai matakin samari ne mahaifin su ya tarasu yace " yaku yayana kusani cewa malamai na sun duba sun gano cewa ajalina na dab da riskata

gashi bana so na koma ga mahaliccina ban cika burina na duniya ba na Lashe Kambun Sadaukantaka ba
amma sai dai kash ina ji ajikina bana Raye lokacin da za'a samu jarumin dazai lashe wannan kambun.
da sauri zaid ya karaso yace " ya abbanmu shin wannan wanne irin kambu ne da kake wannan kalami akanshi.?
A'ina yake.?
abbanmu kabamu ikon zuwa my dauko maka shi.

sarki Iqbal ya dubesu yace "yaku 'ya'ya na kada kuyi yunkurin salwantar da rayuwarku,
Ina Hasko goben Ku y'ay'a na,
Amma inaji a jikina jinina ne zai cikamin burina Dana kasa cikawa
Kusani cewa Kambun Sadaukantaka asalinsa na wani shahararren jarumi ne a yankin larabawa
Ya numfasa ya cigaba da cewa " sunan wannan jarumi marwan ibn mar'oun .
ya kasance gwarzon mayaki a wannan karnin har ya zamana cewa mutanen zamaninsa sun manta sunanshi sai dai su kira shi da abul shaja'a saboda tsananin jarumtakarsa.
shi kadai yakan yaki bataliyar runduna guda inda yana tare da kambun nasa .
yaku yayana kusani cewa a wannan lokaci sai ya kasance cewa kaf duniya babu Wanda make tsoro sama da abul shaja'a 
Ya zama har wadansu suna bauta mashi har ya rasu inda aka rufeshi a kasar Kashmir .
Kambun kuma wani boka Wanda  make kira ruhul auzar ya tsafance shi yasa hadimansa sukai shi dajin NUSUFUL MAUT
dajin dake tsananin birnin Hindu da birnin sin.

Manage with this

KAMBUN SADAUKANTAKAWhere stories live. Discover now