BAƘAR ASHANA 20•21

6 0 0
                                    


*BAƘAR ASHANA*

*Safnah Aliyu jawabi*
(His Noor)

Page 20•21

*PERFECT WRITERS ASSOCIATION*

Follow the PERFECT WRITERS ASSOCIATION channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vad1bE05a249vbEcab0r

" Sannan bara na faɗa miki Hidayata tuni ta daɗe da mutuwa har an binne ta a cikin gidan nan, shin kina so ki ga kabarinta dan ki yarda da zance na?" Ba tare d jiran amsarta ba Kaka ta shiga janta har zuwa bayan ɗakinta, da farko  tunanin ko Kaka ta samu taɓin hankali ne ya fara bijiro mata, saidai  ganin kabarin da aka yi a gurin ya sa ta fahimci tabbas Kaka da hankalinta kawai dai so da ƙaunar da take mata ne ya sa ta kasa jurewa har ta yi kabarin karya dan samarwa kanta saukin tunanin da take a kanta. Nan da nan kuwa tausayinta ya mamaye mata ruhi har ba ta san lokacin da ƙwalla ya fara kwaranya a kan fuskarta ba.

"Kin gani ko? Wannan shi ne kabarin Hidayata wacce ta daɗe da rasuwa ta bar min ƴaƴa gudu biyu marayu masu tsanani so da ƙaunata. kuma kullum cikin yi mata addu'a na ke ban taɓa fashiba."

Rungume ta, ta yi ta fashe da kuka mai sauti zuciyarta cike da so da ƙaunar 'yar tsohuwar kakarta.

Saidai suka gama koke-koke sannan suka samu wuri suka zauna, can ta kalle ta tace"Yanzu irin rayuwar da kika ɗaukarwa kanki ke nan? Yanzu wannan ita ce duniyar da kullum kike muradi? Wannan itace mafarkinki? Kaico! kin zamarwa al'umma bakar Ashana dan kuwa ba na iya hango miki karshe mai kyau muddin a haka za ki kasance, shin ta ina kike ganin za ki zamarwa 'ya'yanki abin koyi? Shin a haka kike tunanin za ki zama madubi abin dubawa ga al'umma? Ina jiye miki tsoron ranar da za'ayi kwatance da ke ya yin da ake bada misali ga rayuwar da bata da al'fanu ga ƴaƴan maƙota, ko kuma wa 'ya'yan cikinki, shin idan kika mutu cikin wannan halin me kika shirya faɗawa Ubangijinki? kin yi tunani da akwai mutuwa? kai ko babu mutuwa ai akwai tsufa, shin waye ya yi miki alkawarin gobe? gobe ma dai da nisa shin minti ɗaya ki na da yaƙinin za ki ƙara yi cikin wannan duniyar mai ciki da ruɗani da shagaltuwa?. To wallahi ina miki nasiha da ki ji tsoron Allah, ki tuna akwai ranar ƙarshe?"

Sauke ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce"Kaka duk na ji zancanki, amma ina so ki sani yanzu cikin duniya na ke ba na da lokacin tunanin lahira dan kuwa ba a cikinta  na ke ba. Bayan haka idan duniya ce ki sani na samu na samu fiye da yadda kike tsammani, zan tashi a kudi na kwanta a kudi ba tare da damuwar komai ba, Kaka ki lamunce min na canza miki rayuwa, na dawo da ke duniyata mai ciki da jin dadi da ƴanci, ni nan na yi alkawarin sai na mantar da ke wannan duniyar da kike kira mai cike da kunci da ruɗani,  zuwa duniya mai ciki da jin dadi da kwanciyar hankali Kakata."

Buɗe baki ta yi da niyyar mayar mata da martanin maganarta. Jin sallamar Hassan da Husaina ya sa ta dakata ta na murmushi mai ciki da tsantsan so da ƙauna, da gudu suka rungume ta suna cewa"Kaka yau dai kam mun yi kewanki sosai da sosai Malama kuma ta hana mu dawowa gida bare mu ganki".

"Lallai kuwa Malama ba ta kyauta ba, ya kuma za ta hana ku dawowa ku ga Kaka?"

Husainace ta yi saurin cafke zancan ta na cewa"Ni dai ki daina cewa ke Kaka ta ce dan kuwa ke ba Kaka ta ba ce ba, ai an faɗa min komai ke Kakar Maminmu ce".

Wani irin gigitacciyar mari taji wanda saidai ta faɗi ƙasa, cike da mamaki Kaka take kallonta su kuwa 'ya'yan musamman Husaina wacce sai a yanzu ne ma take fahimtar akwai mutum a gurin ban da Kakarsu, kallon kallo suke wa juna tsakanin Husaina da Hidaya wacce ke huci kamar zakanyar da ta fito farauta ta na cewa, "Ke idan na sake jin wannan kalmar a bakinki sai na illata rayuwarki banza bakar ƙaddara".

"Kaka wace ce wannan? Kuma mene ne ya sa ta kirani da bakar ƙaddara? Me na yi mata ta mare ni?" Kuka take sosai duk da kuwa shekarunta ba su isa fahimtar abin da wannan kalmar take nufi ba, amma tabbas ta san cewa kalma ce mai ɗacin gaske hakan ya sa ta sake fashewa da kuka.

Ita kuwa Kaka cike da ƙunar rai ta ce"Shin kin san abin da kika aikata kuwa? Ke fa mahaifiyarsu ce, amma kuma kike kiransu da baƙar ƙaddara?"

Nan da nan Husaina t aji zafi da raɗaɗin da take ji sun ɓace ɓat kamar ba su taɓa wanzuwa ba, wani irin murmushi take wanda ke nuni da tsantsar kaunar dake tsakanin uwa da ɗanta, da gudu ta rungume ta na cewa,"Ammi dan Allah kar ki kuma tafiya ki bar mu, na yi alkawarin ba zan sake ɓata miki rai ba."

Da gudu ta nufi wurin Kaka har ta na tuntuɓe ta ce"Kaka ki faɗawa Ammi yadda kullum nake ƙoƙarin zama ta farko a makaranta, inda har kika min alkawarin za ki kai ni gunta, Ka'ka ki faɗa mata cewar kullum sai na yi kuka idan na ga Ammin ƙawayena sun zo makaranta ɗaukarsu. Ki faɗa mata Kaka" Nan da nan kuma ta fashe da kuka sake komawa gun Hidaya ta yi da zummar ta sake rungume ta, Cikin fusata ta yi wurge da ita saida ta buga kai da bango nan da nan kuwa jini ya ce bismilla.

Tsaki ta yi ta na cewa"Lallai kin cika ƴar Babanki dan kuwa haka ya ke da naci da ƙulafici a kan abu, sannan ki sani ko ana alfahari da ƴaƴa ni ba zan taɓa yin Alfahari da ke ba dan kuwa kamar yadda na faɗa ɗazu ke ɗin bakar ƙaddara ce, ko ana amfanuwa da ƴaƴa ni dai babu wata rana da za ta zo min a rayuwa da zan nemi taimako daga gare ki, daga ke har mugun mahaifinki, kalla ki gani kinga Hassan shi ne yake da irin halayyata na dakiya da kuma rashin tsoro, dan haka idan a na alfahari da ƴaƴa tofa Hassan shi ne abin alfaharina..

Cike da ƙunar Zuciya ka'ka tace, "Lallai kin amsa sunan ki Baƙar Ashana kona gari, Hidaya tafiyarki bai haifar da komai ba sai damuwa da tashin hankali, haka dawowarki ma babu abin da ya haifa sai damuwa, tur da wannan ƙazamin hali naki."
"Ka'ka ni ba dawowa na yi ba, zuwa na yi na ganki kuma na duba iyaye na."
"Su wane ne iyayanki a cikin gidan nan?"
Cikin sauri ta rusuna dan kuwa ko a mafarki ta ji wannan muryar babu shakka ta san na mahaifinta ne.

Sake wurga mata wata tambayar ya yi  "Na ce su wane ne iyayanki cikin wannan gidan.??
"Abba kayi hakuri"
"Idan kika sake kirana da wannan sunan sai na tsine miki albarka, saboda haka tun kafin raina ya ɓaci ki  tashi ki fice min daga gida"
Haka kuwa ta tashi ta fice babu ko ɗigon nadama a tattare da ita.
Fitarta ke da wuya Husaina ta fashe da kuka, kuka mai cin rai. Nan kaka ta shiga aikin rarrashi a haka har tayi bacci.
Shi kuwa Hassan ko a jikinsa dan kuwa babu wata ƙauna ko shaƙuwa a tsakaninsu, dan haka bai ma damu da abin da ya faru ba.

************
Karatu ya yi daɗi sosai dan kuwa cikin ƙanƙanin lokaci yake fahimtar komai har ma ya koyar da sauran ƴan aji. abu ɗaya ke damunsa har yanzu, shi ne yawan mafarkin Hidaya da yake cikin matsanancin hali, kullum ya kwanta sai ya yi wannan mafarkin, hakan yasa cikin kwanaki biyu nan babu wanda ke gane kansa.

BAƘAR ASHANA Where stories live. Discover now