33
LATYFAH IMAM
Nana diso
ONLINE BUSSINESS IDEAS CLASS
(DABARUN INGANTA KASUWANCI)TARE DA DEEJARH BERVER.
DATE :- 1 November 2023
VENUE:- TELEGRAM
PRICE :- N5000
- YADDA ZAKI BUNKASA SANA'ARKI
- YADDA AKE ADANA RIBA.
- DABARUN KASUWANCI
-YADDA AKEWA COSTUMERS.
- SIRRUƘAN KASUWANCI
- SAMUN MABIYA A KAFAR SADA ZUMUNTA. YouTube,IG,TIKTOK.BAYANI DANGANE DA WASU SANA'OIN...
- YADDA ZAKI FARA SANA'AR CAKEPOPS.
- YADDA ZAKI FARA SANA'AR PANCAKE MIX
-PUFF PUFF MIX
-GARIN DANWAKE
-GARIN KUNUN AYA
-TEA SPICES..
- HAIR GROWTH OIL.
AWO,STICKTERS,LEDA..DA SAURANSU.kindly pay into:
Deejarh Berver Enterprises
2041774069
FirstbankSEND YOUR RECIEPT TO 09079274454 ..AFTER PAYMENT
_______
Rirrikeshi sukayi dady harda zubda hawaye saboda tausayin ɗan nasa suhail dake kusa dashi ne yace " Kayi hakuri kayi hakuri matarka tana nan kadaina saka kwakwalwarka atunani danAllah" A hanƙali kuma sai yayi shiru sai hucin numfashinsa dake tashi. Hajiya dake gefe guda araƙube abun duniya ya'isheta tace " Yanzu suhail shikenan Abdul yadawo mara hankali? Kuma yadawo karamin yaro?" " A'a Hajiya birkicewar tunani ne shima na wasu mintunan ne amma idan akayi masa magana mai daɗi kokuma aka bashi hakuri zuciyarsa zata tsaya kokuma ayimasa allurarsa." " To Allah yabada lafiya kai kuma sabi'u ba kuka zakayi ba addu'a zamuyi masa." Sallama umar yayi yashigo yadda yagansu jigum jigum yatabbatar masa babu lafiya saukar da idonsa da zaiyi ne yagano Abdul zabura yayi yakarasa yana mai rungumeshi yafashe da kuka yana faɗin ashe mafarkina gaske ne ashe mafarkina dagaskene baka mutu ba yayana ina kashiga? Ina kaje ? Me akayi maka ya jijjira masa tambaya yana mai kuka." Shi dai Abdul baice masa komai ba sai " Ina matata umar? Tana nan ko? Ai tana sona ko? Kuma ma ai tana kaunata ko?." Ohh ni uwar sabi'u da mutum biyu yanzu kuma matar taka kakeso tabbijan Allah yatsare dai amma aure ma babu ai tsakanin su." Dady dayakejin duniyarsa gabadaya ta juya yace " Hajiya yayazanyi? Kawu yazanyi?". Umar ne yace " Dady abashi matarsa mana dady." " Umar tayaya tayaya?." " Dady ai kawai siyeta zakayi da kudi.shine mafita." " dayake shi talaka bashida zabi sai kudi to wallahi bari kuji ko diyata ce bata komawa ciƙin gidan nan wallahi indai dankane yarage aduniya bana aura mata shi kamajini."
******
Hajiya marsi wannan boƙan fa lubabatu tahdani dashi asiri yaƙeyi mai zafin gaske. " Haba kawata bazakiyiwa ƙanki karatun ta nutsu ba bazakiyiwa kanki faɗa ba? Sabida Allah inake ina komawa makaryatan bokayanki? Kina ganin yadda akayi miki saki 1 idan da bokayen naki suna aiki sunhana hakan mana shikenan ke kenan cikin lallata ƴaƴan kishiyarki sannan yaron ma dayarasu kada kimanta asiri kikayemasa ya lallace. Kuma ke kice yaranki zasu zauna lafiya da tarbiya? Ta'ina bayan kullum cikin wulakanta yaram mijinki kikeyi wallahi ba baki nake miki ba idan baki daina bin bokaba to tabbas igiyar aure tana kasa!...
****
Yau Tunda natashi sallar asubahi ban koma ba lura da baffa duk safiyar Allah yana shiga gurin shanunsa ya gyarasu yasa Nima yau nace zangwada hakan, duk da tsoron shanun danakeji haka na kokarta nashiga na gyara gurin to shanun ma basu da yawa gaba daya basu huce biyar ba, ina fitowa na nufi dan gefen gurin da su fulany suke girki Na hada kara sannan na izza huta, tabbas babu mai biyan iyayen mu sai Allah kwana biyun nan dana takurawa kaina gurin ganin na hada hutar girki bana cikakken bacci dan kuwa sai nazo kwanciya sannan ne idanuwa na suke min mugun zafi da radaɗi na hayaki danake kwasa amma nasawa kaina kome zaije yadawo bankara barin fulany wani aikin acikin wannan gidan, Nalura da irin rashin wadata na mahaifina da sai yanzu naƙejin zafin abun araina acikin wannan Watannin da nayi banga dahuwar hatsi ko dayaba sai dai sa'i da lokaci akan kawo mana agidan ardo. Tashi nayi naja hijjabin fulany na fita daga gidan ganin na gane gidan yayata yau nace sammako zan mata, ko dana karasa bantadda kowa gidan ba sai habu ɗanta cikin girmamawa ya gaisheni da fulatanci na amsa masa haba haba yacemin tana gidan maƙota tana surfe, lokaci daya naji babu daɗi ganin yayi hanyar fita yakirata yasani samun gefen wani ɗan dutse na zauna, wallahi duk kyauna da kyan jikina gaba daya yanzu babu dan kuwa duk na yamushe nayi kalar tausayi, sallamarta naji tashigo sai kuma naji tace " Fatsime ne sannunka sannunka habu kawo masa ruwa Ajamo (kana lapy)?." Ina ganinta ta shimfida wata jagaliyar tabarmarta muka zauna nace mata " Yaya baƙida turmi ne sai kinje maƙota?" " Fatsime turmi ai duk rugar nan bashi dashi sai gidan zaino shi kadai yaƙe dashi dayake yana tsada shi turman anan fa dubu har biyu." Wani takaici ne yatsayamin sai kuma naga hawaye yana bin kumatuna dubu biyu? Nafada araina shine kudi?. Kamo hannu na tayi naji wata ƙarta hakan yasani saurin kallon hannunta duk ya faffashe yayi faso. " To menene kaƙe kuka ko maganata ce tabaka haushi." Riko hannunta nayi sosai Nace kuyafemini yaya Tabbas bakasance tagari ba, bayan tilin dukiyar da nikaina na mallaka da yarana amma kuna nan kuna rayuwar talauci da azaba. Nazo in gayamuku ku shirya mu bar garin nan ke kadai zaki iya sabar da baffa ya yarda idan nice nasar mishi bazai amince ba. Inada gidaje da rumfuna a can birni gwara mukoma can da zama danAllah karkice A'a kinga kema habu kadai yaragemiki." " Najika duka fatsime Amma ina tsoron wataran ki koremu." " Kaicona yaya kaicona wallahi ina jinƙu har cikin raina bazan iya rabuwa daku ba danAllah."
" goge hawayenka ." " To kidaina surfin nan naira ashirin fa ake baki nifa natawo da kudi sosai amma bangansu ba ko nabarsu motata habu yazo yaje yadakko mana banason wannan rayuwar danake ganin kunayi wallahi zuciyata zata buga." Sallama wani yaro yayi yace " Wai baffa yace fatsime yazo." Tashi muje yaya nafaɗa ina kamo hannunta har cikin raina najita sauran ƴan uwana dake auran nisa nakeso naje amma baffa yace babu inda zanje babbar mota jeep nagani kofar gidanmu atake naji wani sanyi ya saukarmin saboda ko ba'a fadamin ba nasan mijinane yazo. Sallamar da mukayi nida yaya yasaka hameed mikewa yana rungumeni zuciyarsa nadan masa zafi ganina da yayi duk a sukurkuce. " Hameed nazata kaida mahaifinku ne." Kallona yayi yaja hannuna muka zauna yace "Aa Ammy nikadai ne dadyne yace nazo natawo dake." " tare da su baffa dai zamu tafi dan bazan barsu nan garin ba babban gidana na cikin unguwa zasuzauna." Murmushi yayi yace " Mashaa Allah daman haka nakeso nima." Dakyar na lallaba baffa ya amince da fulany da yayata da kuma ɗanta habu muka kama hanya nazo ardo da matansa su bimu yace Sam Sam yadai amince intafi da nawa iyayen.
Hira muka shigayi sosai abun mamakin da su laila. Aliyu kam tunda muka gaisa ya huce yadda na sakar musu jiki basu taba tunani ba kasancewa zanje nakai noor allura nana sai kawai ta kaini mukaje muka dawo. Nan fa laila tace anan zata kwana bazataje gida ba bance komai ba dan nasan ina magana iyami zata rufeni da faɗa. Yanzu dai dole idan kika kwana biyu muje asiyo cream masu kyau kishafa ko?" " Nima daman nayi tunanin nan ai macce sai da gyara mama dana zauna gidanta tabani wani manta nake shafawa wallahi bakiga yadda nakara kyau na." " Har gyran jiki duk zamuyi ai bari dai akwana biyu." Garawuni ɗan kadan da madara iyami ta miƙomin tace gashi insha yanzun nan duk da dacen da yake haka na ƙarba nasha. Inajin laila da nana sunata shirya yadda zasu gabatar da suna amma bankula su ba. Ko da Noor yasaka kuka nana ce ta daukeshi ta goyashi shima ban hana ba. Saboda iyami tacemin wanda ya nunawa ɗanka so ai yagama maka komai acikin duniya. " iyami ƙin gama awarar? Nagama mana latyfah lafiya? Ko yunwa kikeji kinga na dora abincin tuwo da miyar kuka." " To iyami ko xaki dauki ko dubu uku ce asiyo mana kaza sai asaka amiyar kinga baƙi suna shigowa ni wallahi abincin su laila bazanci ba." " Tohm bari Na gangara nasiyo da kaina ki shiga ki kama ruwa ga ruwan zafin nan na kawomiki." To sannu inna na gode. Sallama muƙaji ana kokarin shigowa cikin gidan ganin dady da kawu ga kuma hajiya abayansu sai mukaga Abdul yashigo ai bani kadai ba hatta iyami sai tasaka gudu nima nashige daƙi aguje ina jan numfashi laila da ummy da Nana suna tambayar lafiya..???
YOU ARE READING
LATYFAH IMAM
Short StoryBA KYAU BANIBA ABUN DAMUWA DA ABUN ALFAHARI ƘYAN HALI DA KYAKYAWAR ZUCIYA SHINE CIKAKKEN ƘYAN FUSKA! KOWANNE BAWA DA TASHI JARABAWAR ITA KUMA LATYFAH ADNAN AHAKA TATA JARABAR TAZO MATA...