17

36 4 0
                                    

17

LATYFAH IMAM

Tunda nagama secondary sai yazamana ina gida itadai iyami tafison inyi aurena batason cigaban karatun nan Nikuma Har raina inason cigaba da karatuna saboda ko banda kyau da ake fadi ilimi na zai iya ƙaini inda makiyana basa tunani, samarin da nake dasu ko Aisha take kama da mahaifiyarta kyakyawa batadasu a malaman islamiyyar mu kuwa hatta  mai makarantar sai da yanuna shifa abanishi kawai yanasona, Anan ne na yarda ba kyanne abun dubawa ba a rayuwa quality na abu da kuma kyan halinsa, Asatin naje dangin mahaifiyata dake gaba damu to suma dai babu yabo babu fallasa amma gaskiya basa nuna suna sona da niyar kwana biyu naje yadda kakata tashiga faɗa tana faɗin zandamemiyar budurwa ta'isa aure amma anki yimata shine zatazo tajira kafaɗa da'ita A'a gwara in koma cam gurin wanda zasu iya. Ina baƙin cikin abunda suke mun amma ganin babu yadda zanyi dasu yasani nake haƙuri a hanyata ta dawowa ne nayi wani saurayi wai shi Alhaji gaddafi kai mun zuba soyayya dani dashi kamar bazamu rabu ba, Ashe dan iskan mutumun nan zuwa yayi ya lallatani dan kuwa lok'acin da nace yaturo iyayensa tun daga nan bai ƙara zuwa ba! Nana tazo ta nunamin sabuwar wayarta da kuma system da abiy yasiya mata ta shiga jami'a Abun mamaki hardani asiyayyar komai namu iri daya! Iyami tayita fada tana faɗin gaskiya hidimar tayi yawa nana tace A'a wallahi iyami wanene take dashi bayan ni nan iyami tayimata godiya nima nayi mata, kunsan abun mamaki ko sau daya bantaba takawa gidansu ba saboda ina gudun wulakanci dan muntaba zuwa gidan alhaji mai lema mai gadin ya kallemu ya watsar alamun bamuyi kala da wanda zasu shiga gidan ba, wannan karan ni dakaina na shirya naje har gida na gaida ummy nayi mata godiya sosai.

  Ashe wai duk samarin danakeyi ita umma tana gefe tana ɓatamin suna bansaniba! Akwai Alhaji lukman shima har iyayensa yace zai turo ya gudu! Danayi masa text sai yarubutomin ƙalma kamar haka " _KINA BUKATAR MAN WANKE FATA DAN GASKIYA MUNINKI YAYI YAWA GASHI ANCE BAKIDA NUTSUWA HAKA UMMANKI TACEMIN WARI KIKEYI GASKIYA BAZAN IYABA DAMA ACE MAHAIFINKI ZAI BANI GIDA DA MOTA TO DA TABBAS ZAN AUREKI."_ nayi kuka sosai, sannan naki nunawa iyami nakuma godewa Allah da yadda ya halicce ni, Daga lokacin nafahimci soyayya karyace dan haka bankara ɓata lokacina agurin kowa ba sai malamina Mudassir dake mun Soyayyar gaskiya duk da bashida wani karfi amma bantabaji na tsaneshi ba, rana tsaka iyami tayi lafiyayyar miya tace sai munje gidan Alhaji mai lema in gaisheshi kada yazata dani da'ita bamuda hankali wannan hidimar da yake mana! Nanfa umma da yaranta suka shirya suma dayake muna shiri da abbas sai na kama hannunsa muka tari taxi mukaje.

  ALHAJI MAI LEMA babban dan kasuwani wanda yake safarar kayayyake daga kasashe yana shigowa dasu cikin garinmu, yanada kudi sosai amma duk kudinsa naga anfi ambatar na alhaji auwalu dogo, matansa guda biyu Mumy wacce ake kira da Sadiya tanada yara guda biyar Akwai farrah da fannah da zakkiya da Wafiyya sai umar itama kyakyawar macece ga kirki dan mutanen unguwa sunyi mata shaidar kirki sai kuma Ammy wacce take cikakkiyar bafulatanan riga kyauta mahaifinta yabawa dady ita Sunanta faɗima tanada yara kamar haka akwai hameed babban danta sai Abdulkarim sai Aliyu sai lailah yaranta Allah yayi musu nutsuwa Amma kuma Abdulkarim yafita zakkah saboda tsananin kyan da yaƙe dashi, hakan yasa dafy kaishi America yayi karatu acan tundaga nan tarbiyarsa sai tazama sai ahankali, tsananin son ɗa da kuma wayewar da ammy take ciki yasata bata ganin laifin yaran nata. Ko sanda muka isa matan da yaran suk sunyi tafiya dan haka akayimana iso zuwa  bangaren saukan baƙi! Kai zo kuga karamci babban mutumin da yasan darajar mutane " latyfah imam diyata mashaaAllah kice angirma ya karatun ankammala." Kumyar duniya taisheni nan na shiga sunkuyar da kai! Nan take umma ta nuna bacin ranta ta hanyar cewa " Ai Allah yasa ba asarar kudinka kakeba dan in banda kule kulen samari babu abunda tasaka agaba!." Cikin nuna rashin damuwa yace " Ai maganar samari ma hajiya a jiyeta gefe guda har nawa take inshaa Allahu zaki fara zuwa private university dinnan zuwa karshen makon nan dan angama komai ma yafada yana murmushi, ai iyami wannan matar abdul dina ce inshaa Allahu  yafada har cikin ransa! Nan yayimana alkhairi ba kadan ba.

  LATYFAH IMAM shine abunda kowanne ajinmu yake kirana! Na karanci BUSSINESS admistration, bakaramin ja kaina yakeyi ba kasancewa itama nana shi takaranta nan muka haɗe zumuncin mu yayi karfi sosai! Acikin shekarun munyi farinciki da akasin haka har Allah yasa nakammala jami'ar naje nayi bautar kasa! Alokacin jikina yabayyana sosai bafa wata kibar zo.agani nake da'ita ba amma yanayi boobs dina da hips sai kazata wata kibace dani.

  Ranar da nakarbi takarduna na gama karatu har gidan alhaji mai lema naje nayi masa godiya nan fa na tarar dashi abashida  lafiya ga dan uwansa gefensa yanata bashi hakuri, nima nashiga bashi hakurin jin zai koro abdul daga gidansa! Kawu yace aure yakamata kayimasa ba zato babu tsammani naji yace latyfah danAllah zaki auresa nasan bai dace dake ba ke dakike tsatson imam mutumin kirki kema yarinyar kirki amma bansaniba ko ta dalilinki ya shiryu! Har ga Allah inason nayi auren amma kuma inani ina dan gidannan! Yadda naga hawaye A fuskarsa yana mini magiya sakani cewa na amince! Sosai yayi murna !

Asatin munga barazana dan ummy har gida tazo ta zage iyami da kuma mata gargadi.

Ranar danaga abdul a kofar gidanmu shine na fita waje ina zuwa yace " hy pls latyfah imam fa?" Nace masa sannu da zuwa nice batare da naga kamarsa da alhaji mai lema ba danshi da ammy yake kama kuma banma taba ganinta ba ko sanda tazo ta zagi iyami bana gida! " You ugly? Ke mummunan nan zan aura? Bakiga tazarar mu baniba and after all lukuta baka mummuna? Allah yakiyaye! Atake hawaye yashiga bin fuskata ba tare dana farga ba!

LATYFAH IMAMWhere stories live. Discover now