15
LATYFAH IMAM
KUYI FOLLOWING DINA A AREWABOOK https://arewabooks.com/u/nanadiso10
____
Murmushi Ummy tayi batace dashi komai ba, har tashiga bandaƙin tana mai rudu da irin duƙiyar abiy din, wani lokacin har tsoro abun yake bata! Ko datayi wankan tafito rigar wankan kawai tasaka ta iso zuwa inda yake tana faɗin " Ina yaran nawa suke ne?" Baice mata komai ba yacigaba da dannah system dinsa har ta nufo kusa dashi ta zauna!. Kai tsaye yace mata " Shiyasa nace Amaryata tazo ai!" Murmushi tayi duk da maganar tayi mata ciwo amma batace komai ba tace " Kayi hakuri abiy da dayanzu ba daya baniba ni girma yafara rikeni dole wani lokacin jiƙina zanjisa babu dadi, Amma gani yanzu ai tafada tana zuba masa kyawawan idanunta! Sosai yaji kunyar maganar da yayi mata amma duba da idonsa arufe yaƙe gurin ganin yabiya buƙatarsa sai yarikice yashiga aika mata da saƙonni da ya nuna tabbas yayi kewarta! Shiyasa yake kaunarta ako da yaushe da girma yaci mata bata daina kula da tsaftar jikinta da kuma bashi zafaffiyar soyayya ba danshi duk yadda macce take idan bazata iya sarrafasa a ƙan gadonsa ba sai yaga kamar batacika macce ba! Amma wannan karatun na ummy kullum kara riketa masa tunani da kwakwalwa yakeyi! " Hayaty yafaɗa da rarraunar muryar da sai da ummy ta ƙauda kanta! Allah yayi miki albarka ya faɗa." " uhm tafada cikin sanyin murya da lumshe idanu. Yana daga cikin abunda ummy tarike akan aurenta dan mijinta mai son kulawa ne yasha gayamata shi bazai nemi mata ba Amma yanason matarsa tawaye dakuma iya kula da shimfidarsa! Shiyasa itama tayi darasi na musamman awannan fagen! Yadda take koyar yadda zata sarrafa mijinta bata shan mganin mata haka! Dan ta yarda da gamshashen jima'i shine abunda ke riketa duk wata kwakwalwa ta zaman takewa! Bazata manta ba sanda kakarta ta zaunar mata haihuwar Babbar ƴarta tasha gayamata shan magungunan nan da tusa su basu ke sakawa miji rawar akafa akanki ba, iya sarrafa miji da salo a yayin kwanciya shine babban sirri kuma abun rikewa dan tasha cewa bariki da karuwanci ai ba'a maganin mata yake ba a shimfiɗa yake!
*****
Bazaiyihu ina tufka ana warwaremina ba! Menene kuma wai yadinga addu'a? Malam harfa abun yawarware bakaganshi ras ba! " hajiya shifa sihiri indai zayi addu'a da neman tsarin Allah to tabbas sai ya rabuda wanda akayi masa! Yanzu dai mekikeso ayi?" Ita wannan yarinya nagama fa da nata nashafa mata asaman gashinta kamar yadda kace dan ingayamaka jaɓama tafita farin jini, " dariya yayi yace ranki yadaɗe haka zatayita zama bata auru ba!. Sai kuma me kikeso ayi yanzu! Inaso ka haɗa masifar da ita matarsa zata bar gidannan da ƙafarta inaso na azzah kujerar mulkina banso karaga ko.ka daga kafa idan da hali akashe rai." " zanbada garin magani akawomiki ki zuba mata acikin abinci ina tabbatar miki sai ta barmiki gidan da ƙafarta zankuma haddasa masifa atsakaninsu amma inason insane lokacin al'adarta" " mai sauki kenan malam farkon wata takeyi." " To zamuyi amfani da wannan lokacin da batada tsarki muyi aikin da zamuyi akanta!." " Nagode malam sako zai taddaka adaren nan."
******
USAZaune yake a offices din yana kallon aboƙinsa yana murmushi! " Zaka zauna haka ne? Kai nifa ko da aurena sai naji dadi na babu ruwan matata da ƴammatana, kai yusuf ka takura kanka! Ga kudi ga jiki mai kyau ga kyau amma baka zuwa club!, yanzu haka danake gayamaka yara biyu nayi booking zansha daɗi yadda yakamata!, danAllah kazo muje nasamar maka zafaffun yara.
" Idan na mutu ina aikatawa fa? Inje incewa Allah me? Kaifa muhsin naga baka tsoron Allah kwatakwata bariki ne agabanka kana ganin kanada damar kudi, to wallahi kasani masifun dake ciƙin zinar nan sunada yawa! Kuma yaya zakaji yau idan kaga anayi da matarka ko kanwarka ko ƴarka?" " haba yusuf yazakayimun wannan baƙin ai wallahi sai na kashe wanda ya kwanta da daya daga ciƙinsu." " Ohh really? Amma kai kake aikatawa ga yaran wasu! To kasani akwai kazanta akwai kwayoyin cutuka akwai masifa akwai bala'i akwai rashin imani akwai azaba sannan akwai sakayya! Duk acikin zina idan zakayiwa kanka faɗa kayi idan bazakayi ba kaje can kayi bayani ya faɗa yana barin gurin.Ko sanda ya karasa gida yatarar da Nana tana murnar ummy shima harda rungume mahaifiyar tasa yana faɗin" Wallahi muhsin yatsareni abiy." " Amma nahanaka yawo da yaron nan ko Yusuf?" " wallahi abiy ba yawo mukayi ba na taimaka masa da aikine ta document dinsa." " Mashaa Allah yafɗa yana mikewa ya'isa, " Bari naje na huta Nana." Sai da safe sukayi mata sannan ta nufi bangaren mahaifin nasu ta a isa yana kwance nan tashiga yimasa maganar kursum duk yana jinta bai tofa komai ba har tagama! " Yanzu dai kinaso Inyiwa ɗana auren dole?" " Haba hayaty auren dole? A'a ni bahaka nake nufi ba naga dai ƙursum din nan kanwar matarsa ce." " Nima banƙi haƙan ba sai kuyi magana yafaɗa."
GIDAN YARIA lok'acin da kike raina katifar bancin ki wani yana kwance a kan kasa ne, alokacin da kike masifa akan bazakici cimar da mijinki ko iyayenki suka tabadarmiki ba wani yana nan yana kukan yunwa, alok'acin da kike raina sutturar da mijinki yake miki mu muna nan muna yawo da kazamar riga wacce ake kiranta da uniform! najikinmu da suka same mana! Daman haka masu kudi suke? Wannan wulakanci har ina? Daman akwai soyayyar karya wannan shine ke yawo dani acikin kaina dangane da alhaji mai lema! Aminintakar karya da Nana ta nuna min shine abunda yafi komai kuntatamin duk da naji ance sunbar kasar hakan kuma a arzukin mahaifinsu bakomai baniba, zaune nake ina tunani ina ƙallon yanayin yadda kafata ta ƙumbura, ambatar da akayi Lokacin abincin rana yasakani hanzarin mikewa inajin bayana ƙamar zai ɓalle ga kafata da faso ya faffasa zafi sosai takemin, jin nauyin jikina yasakani kasa gudun amma inayin sauri sosai har na nufi layin namu rike da kwano a hannuna!
Tsananta danayi da addu'a da zikiri sai nasamu nutsuwar zuci amma har yanzu hawaye baya rabo da ƙumatuna ga masu horon basuda imani yanzu dan basa ragamin kamar da, zuwan lauyana gidan yarin yabamu ikon zantawa dashi inda ya karfafamin guiwa sosai dangane da shari'ar yakuma tabbatar min da zasu ƙarbi bele na, ban yarda da maganar tashi ba na dauka yaudarar masu kudi ce shiyasa har yafita ina masa kallon rashin yarda!
LATYFAH Wannan dattijuwar tafaɗa tana dafani. " Karfe 12 amma baki daina kuka ba!." " babah idan kukan cikin jikinane babaah idan yanzu suka ki ƙarbarsa? Idan aka shegantamin shifa?" Murmushi dattijuwar tayi tace ai ba'azo nan ba har yanzu latyfah wannan ihun bakyason cikin dakikeyi sai kinzo kina yaqar dangin uban cikin dashi, kina yawan gayamin bake kika kashe shi ba? To wanene ya kasheshi? Ke wacece dattijuwar tafaɗa.
YOU ARE READING
LATYFAH IMAM
Short StoryBA KYAU BANIBA ABUN DAMUWA DA ABUN ALFAHARI ƘYAN HALI DA KYAKYAWAR ZUCIYA SHINE CIKAKKEN ƘYAN FUSKA! KOWANNE BAWA DA TASHI JARABAWAR ITA KUMA LATYFAH ADNAN AHAKA TATA JARABAR TAZO MATA...