6

46 3 0
                                    

LATYFAH IMAM

Nana Diso

KUYI FOLLOWING DINA A AREWABOOK https://arewabooks.com/u/nanadiso10

Naje gida? Tafaɗa cike da shock me kenan ya saƙeni? Tasaka kuka tana mai barin shashin nasa, yau dai tashiga uku dan tasan mijin nata ba'irin mazan nan ne zaka juyasu anyhow ba, tabbas sai tabar gidan nan ko da na kwana daya ne, sashinta ta shiga tana ƙara rushewa da kuka mai tsanani, sosai hankalin yaran nata yatashi suka rikota suna zaunar da mahaifiyar tasu Ali ne yashiga tashin hankali dan zatace duk yaranta irin yarannan ne masu masifar son uwa, " ammiey menene yafaɗa idonsa yana ciccikowa da ƙuka. Yadda ammy ke shasheƙar hawaye zai tabbatar maka da tana ciƙin tashin hankali " Wai dadynku ne yace natafi gida, daga Nacewa ugly girl dinnan monkey harda marina." Laila ce tace " Tabbijan akan waccan jaƙar yarinyar mai ƙama da buhu? Shine za'a wulaknta mana ammy?." Aliyu ne yashiga ajiyar zuciya yanajin wani zafi ciƙin ransa saboda abunda mahaifin nasu yayiwa uwarsu miƙewa yayi zai fita ammy ta ƙamo hannunsa tana faɗin " No Ali karkaje zai iya tsinemaka kaga jiyama sai da yayimun magana akanka kubarni na zauna lafiya dashi kuna ganin sauran ƴan uwan naku lafiya lafiya dasu." " Haba ammy marinki yayi fa! Har ma yace kije gida akan monkey girl dinnan haba ammy wulakantacciyar yarinyar nan itace za'a haɗa dake to kitafi ina? Kauyen zaki koma cikin gidan kasa? Haba ammy." Babban yayan nasu hamid yanajin komai dama dashi bayashiga shirgin sabgar su dago ƙansa yayi yace " ammiey kiji tsoron Allah kisani wannan yarinyar da kuke wulakantawa Allah ne ya halicceta ba ita tayi ƙanta ba mutum kamar dan adam ace kuna haɗashi da dabba? Shifa dan adam mai daraja ne? Hasken fatanku ko duhun fata nazai ƙaremu da komai ba sai tsoron Allahn mu, wallahi daƙinsan latyfah imam da cigaban da taƙawo arayuwar dady da bakiyimata wannan muguwar tsanar ba, ke kuma laila wallahi kiji tsoron Allah ina gayamiki bakisan gidan wa zakije ba zakiyi aure kuma zaki haihu daga ke har Ali wallahi dukanku zaku haihu kuma duk abunda kukayi sai anyi muku." Ammy ce ta rufeshi da faɗa sosai tana fada masa daman bayasonta ai ita tanama tantama ko ita tahaifeshi anya badan kishiya baniba." Allah yabaki hakuri ammy gaskiya ce sai nafada muku sannan shi Abdul din dakikeyi danshi sanin darajarki yayi yanzu kwana nawa rabonsa dayazo yaganki? Babu abunda yasa agaba sai shaye shaye da bin mata saboda tsabagen iskanci har offices lalata yakeyi da mata sannan kina zagin matar dake hakurin zama dashi." Sai da gabanta yafaɗi najin maganar hamid din dan tasan shi baya karya no matter what gaskiyar nan sai yafaɗeta kuma sai ya tabbatar da'ita kamin yayi maganar. " Ni yau zamu tafi da dady sai Allah yakara sadamu da alkhairi yafaɗa yana ficewa daga daƙin." Aliyu ne yace " kinji sharrin dayakeyiwa Abdul ko? Wallahi karya yakeyi shi wayasan menene yakeyi aboye. Duk banza tayi musu tatashi tashiga ciƙin daƙinta tana kuka dan tabbas aliyu gaskiya yafada bazai taba yiwa Abdul karya ba.

Haba dadyn umar kayi hakuri mana maganar tatafi gidama adaina zancen nan dajin kakeso taje? " Mumyn umar abun yana damuna akan dabi'unta da'ita da yaranta hameed ne kadai ya bambanta wallahi sai ace ke kika haifesa duk yarana ina kokari akansu kuma Allah yataimaka min akan tarbiyarsu shi da yatashi naga take takensa bagashi nayi masa aure ba yazauna da matarma ya gagara daga tozarci sai wulakanci kwanaki ancemin gaban ƴan aiki ya mare yana zaginta. Mumy ce tace " Ni wallahi yarinyar ma nakeji baiwar Allah rannan gabana ammy kece mata monkey saboda Allah fa! Amma kayi haƙuri dadyn umar inshaa Allahu zasu gyara su yaran harda yarinta shima Abdul harda yarinta." " uhmm ga katina nan dayan zai kibawa ammy yanzu jirginmu zai daga zan haɗu da sauran abokaina acan tafiya ce da zata daukarmin lokaci sosai dan zanyi kusan shekara nida hamid. " Batare da nuna damuwa ba tace ubangiji Allah yakaiku lpya yatsareku yabada sa'ar abunda akaje nema to amma umar fa tafaɗa badan nuna damuwar jin haushinta ba sai dan ganin matsyar da mahaifin nasa yasakashi tunda shi kadai ne danta namiji sai mata da duk suna gidan aurensu." " Bazai taba yihuwa intafi da su biyu ba duk masu hankali nabar Ali akan dukiyata wannan kuskurene shine zai kula da komai nawa na nan." " To badamuwa dady Allah yashiryamana su yayi musu albarka tafaɗa dattijuwar." " Ameen kema Allah yayimiki albarka.

LATYFAH IMAMWhere stories live. Discover now