Page 57

109 2 0
                                    

Page 57

Queen Afreen tana dawowa palace dinta shukriyya ta biyo ta,bata ma kai ga shiga ciki ba ta tsaya cikin murmushi ta kalli consort Sook

"Yaya kikai da fudail?"

Qasa shukriyya tayi da kanta

"An tafi da shi kurkuku! Amma yana cikin matuqar kaduwa da abinda ya faru domin baiyi tsammanin hakan ba!"

Lumshe ido queen Afreen tayi

"Hakane! Ba zai taba tunanin haka zata faru ba,Nima hankali na bai taba kawo min haka ba har sai da kika sanar dani cewar mai martaba yana son yayi murabus! Amma kafin sannan,na yadda da duk abinda fudail yake fada min dari bisa dari! Kuma na godewa Allah da yasa banyi mummunan kuskure ba!"

Murmushi shukriyya tayi

"Your majesty! Daga lokacin da na karbi umarnin ki na cewar zan bar masarauta a ranar,na damu sosai,shiyasa da nazo wajenki........."

FLASH BACK!

A ranar da shukriyya ta je wajen queen Afreen domin ta janye umarnin matso da tafiyarta har sai mai martaba ya dawo,Babu wanda ya san abinda suka tattauna,kawai dai shukriyya ta fito tace a shirya tafiyar kamar yadda queen tayi umarni,to ga abinda ya faru

"Your majesty! Ina son in yi miki wata tambaya! Shin saboda Fudail ne kika bada umarnin tafiya ta a yau? Har yanzu kina tunanin cewar zan cutar da crown prince ne?"

Shiru queen Afreen tayi,Shukriyya ta cigaba da magana

"Your majesty! Jiya daddare da kika je waje na,kin tuna ina qoqarin sanar da ke wani abu kafin a fada miki fudail yana neman ki?"

Jinjina kai kawai queen Afreen tayi,shukriyya tace

"Your majesty! Mai martaba Murabus zai yi! Kuma ya yanke wannan hukuncin ne domin ya kare rayuwar Crown Prince tare da Prince Yeon!"

Zaro ido queen Afreen tayi,wanda yayi daidai da mummunar faduwar gaba tace

"Me kika ce? Murabus?"

"Fudail ya san da haka your majesty! Abinda ya fi jin tsoro a yanzu ba ma tunanin ina son hallaka crown prince bane,abinda yafi tsoro shine Prince Yeon ya samu mulki da qarfin iko fiye da shi!"

A gigice Queen Afreen tace

"Consort Sook! Yanzu consort Sook...."

"Your majesty! Idan har Fudail ya tsara in bar cikin masarautar nan a yau,tabbas akwai wani abu da yake shiryawa,Hakan yana nufin matuqar muna son sanin abinda ya shirya din,ya zama dole sai na fitan,saboda tsarinsa ya tafi daidai! Amma kafin nan Shin zaki iya yarda dani? Ki bani wannan damar domin na nuna miki ainihin wanene fudail! Ki taimaka ki bani damar nan your majesty!"

*********
Sannan kuma bayan Shukriyyah ta samu labarin fitar crown prince a ranar,har ta he ta samu su nadeeyah,Nadeeyah ta bawa Afrah takadda ta kaiwa shukriyya,shukriyya ta fito zuwa Queen's palace da takaddar! Miqewa queen Afreen tayi

"Ga wannan! Na saka office of investigation sun yi min bincike yanzun nan! A yau dinnan an canja hanyar da crown prince ya kamata yabi domin zuwa liyafar da suka ce ya tafi,a maimakon hanyar da aka saba bi,sai aka canja zuwa hanyar da ni zan bi domin zuwa Yihyun palace! Hakan yana nuna akwai abinda suka shirya akan hanyar! Kuma hakan shirin fudail ne! Ki yarda dani your majesty!"

Duba takaddar takeyi cike da gamsuwa da abinda yake ciki.

Haka nan bayan fudail ya fada mata ta bayar da emergency decree ya tafi,ta rikice sosai domin ta rasa wanda zata yadda dashi tsakanin fudail da consort Sook! A qarshe dai ta bayar da decree din kama fudail ba tare da samun qwaqwaran dalili ba.

ROYAL CONSORT 2Where stories live. Discover now