Page 50

94 6 0
                                    

Page 50

A daren ranar mutuwar jaleela,Ruwa akeyi kamar da bakin qwarya,yayinda crown prince ya kasa daukan qaddarar rasa mahaifiyar sa,ya kasa yadda da cewar mijinta da kanshi ya yanke mata hukuncin kisa,watsi yakeyi da duk wani abu da ya ci karo dashi a cikin dakinsa,hatta abincin da aka kawo masa ma sai da yayi watsi da komai,ciwuka ne a hannunsa saboda yadda yake wasa da kwalba da tangaraye ba tare da damuwa ba,gunjin kuka kawai yakeyi gashi kuma an rufe qofar dakin sun hana shi fita ko'ina,attendants din da suke tsaye ya cillawa kwanukan abincin da suka kawo masa cikin kuka yake cewa

"Ku fita! Bana son ganin ku kuma! Babu abinda zan ci,ni ma zanbi mahaifiya ta inda ta tafi! Ku fita ku bani waje nace!!!"

Kwana biyu tsakani amma crown prince yaqi yadda ya ga kowa,babu wanda yake shiga wajensa kuma sannan baya cin abinci,Noor kullun sai yazo amma attendants din suce masa crown prince ya bada umarnin kada wanda ya shiga wajensa,Mai martaba da shukriyya ma sun damu sosai,amma ya za'ayi? Dole ayi haquri har sai lokacin da ya gama alhinin abinda ya samu mahaifiyar sa.

Da yammacin ranar,Noor ya dawo daga makaranta ya taho garden din crown prince ya zauna,fitowar crown Prince kenan daga daki tun da abin ya faru,garden din ya nufa domin shan iska,a durqushe ya hango noor yana tono ciyawa,juyowar da noor zaiyi ya hango yayan nasa,tasowa yayi cikin farin ciki yace

"Yaya! Nazo na zauna a anan ne ko zaka fito yau! Na damu sosai a kan halin da kake ciki! Da fatan Kana lafiya! Naji ance kwananka biyu baka ci abinci ba,ina ta tsoron kada wani abu ya sameka"

Saroro crown Prince yayi yana kallon noor,a zuciyarshi yana tunanin duk abinda mahaifiyarsa tayi na yunqurin kashe noor amma har yanzu noor baya jin haushin sa? Shi wace irin zuciya ce da shi? Crown prince ba zai taba iya jure wannan qaunar da noor yake nuna masa ba,bayan ya san ahalin mahaifiyarsa masu laifi ne a wajen noor da mahaifiyar sa,ba zai iya karbar wannan soyayyar da noor yake nuna masa ba,domin hakan zai dinga saka shi a cikin kunyar sa sosai,shiyasa ya zama dole ya yakice noor daga kusa dashi don ba zai taba yafewa kanshi ba idan har wani abin ya qara samun noor saboda shi,Kauda kai crown Prince yayi gefe yana hawaye,Noor ya hango hannun crown Prince da aka daure masa da farin qyalle,riqo hannun noor yayi

"Yaya! Ciwo ka ji? Garin yaya?"

Fuzge hannunsa crown prince yayi

"Ya isaaaa!!! Yaya kace? Kar ka qara kirana haka! Ni ba yayanka bane! Ni maqiyin kane da ya kamata ka dinga jin haushi kuma kayi duk yadda zakai kaga bayana! Nima kuma haka kake a wajena! Domin irin rayuwar da muka tsici kanmu a ciki kenan!"

Ido a waje noor yace

"Yaya! Maqiya kuma? Meyasa zaka kiramu haka?"

"Yeon!! Kada ka raina min hankali! Kana nufin baka san mahaifiyata tayi yunqurin kashe ka bane? Ko baka sani ba?"

Kallonsa noor yayi

"Amma yaya,wannan ai..."

"Nace ma kada ka qara kirana Yaya! Kada ka qara yi min murmushi ko dariya! Kar ka qara damuwa da halin da zan shiga! Kallon maqiyin ka zaka dinga yi min!"

Qasa noor yayi da kanshi yana jin haushin abinda yake shirin faruwa tsakanin shi da yayan nashi,crown prince yace

"Ni da kai ba zamu taba zama 'yan uwa ba! Mu maqiya ne da zamuyi fada akan neman karagar mulki! Haka rayuwar masarautar mu take! Saboda haka kada ka qara zuwa wajena,ka fahimta?"

Kuka yakeyi a lokacin da yake fadawa qanin nasa haka,yana jin tafasar da zuciyarsa takeyi,barin wajen yayi ya bar noor a tsaye yana kuka shima.

Bayan noor ya bar wajen crown prince ya dawo cikin garden din yana kallon wajen yana tuna yadda yake zama da qanin nasa cikin farin ciki,suyi wasa tare,suyi karatu tare,suyi komai tare cikin farin ciki,amma yanzu saboda kasancewar su 'ya'yan sarki,masu rayuwa a cikin masarauta yasa ba zasu iya rayuwar farinciki tare ba.

ROYAL CONSORT 2Where stories live. Discover now