Page 48

79 3 0
                                    

Page 48

Suna zaune cikin rashin nutsuwa,jaleel yace mata

"Ki tashi ki bar cikin masarautar nan,na shirya miki masu tsaro na musamman saboda na tabbata idan aka gano ni kema ba zaki tsira ba"

Girgiza kai tayi da hawaye a fuskar ta

"Babu inda zani! Ba zanje ko'ina ba orabeuni! Kai ya kamata ka gudu saboda ka kare rayuwar crown prince"

"Your highness! Idan nayi yunqurin guduwa a yanzu,na tabbata ba zan fita daga cikin masarautar nan da rai ba,saboda haka dole daya a cikinmu ya rayu domin ganin lokacin da crown prince zai hau karagar mulki"

Cikin qaguwa tace masa

"Ka tashi ka tafi! Cikin kowane irin lokaci guards zasu iya zuwa nan nemanka,ka tashi ka tafi"

Kafin ya ce wani abu suka jiyo muryar Abdallah yana fadin

"Mai laifin jaleel yana cikin nan! Ku shiga a kamo shi"

Zaro ido su jaleela sukai a zaune,kafin su ankara tribunal guards sun bayyana a gabansu,rirriqe jaleel sukai zasu fita dashi,jaleela ta taso kamar zatai hauka tana son ta rirriqe shi,abdallah ne da wasu mutum biyu suka shiga tsakaninsu,tana haukan fadin

"Ku matsa min daga hanya! Ku matsa nace!!"

Abdallah yace mata

"Ai yanzu baki da damar fita daga quaters din nan naki! Domin ke ma mun kusa zuwa gareki!!"

Kallon idonsa take da yake cike da tsantsar tsana da kuma burin daukar fansa,ficewa abdallah sukai suka barta a wajen,yana fitowa waje ya kalli sojojin da ya jera a bakin quaters din yace

"Ku zagaya duk wata qofa da kuka sani da zata fitar da mutum daga quaters dinnan,ku tabbatar ba shiga ba fita!!"

"Yes sir!"

Suka ce tare da watsewa su aiwatar da umarnin sa.

Jaleela kam qafauwanta ne suka kasa daukar ta,kuka takeyi kamar zata ciro zuciyarta waje,yanzu babu kowa a qauters din sai ita kadai,tunda attendants din ta ma sun shiga cikin bincike.

..............................

Mai martaba a zaune a grand palace,'yar tsanar da take sanye da kaya irin na queen haneefah yake dagawa yana kallo,tare da dauko katakon da yake dauke da sunanta,hannunsa yana rawa ya ajiye su ya kalli naseer domin jin abinda zai ce

"Your majesty! Sun aikata wannan abin domin hallaka queen haneefah! Consort Sook ta san komai,amma tayi qoqarin bawa consort hui wata damar ta qarshe saboda darajar crown Prince,amma duk da haka sai gashi yanzu sun qara yunqurin kashe Consort Sook da Prince Yeon!"

A rude mai martaba ya qara dauko 'yar tsanar yana kallo

"Ta yaya? Yaushe jaleela ta zama haka? Ta yaya zasuyi mummunan abu irin wanann? Su suka kashe My queen?"

Huci yakeyi don zuciyarsa tayi masa matuqar qunci.

.................................

Washegari da safe,labarin abinda ya faru ya ratsa ko'ina,kasancewar abin ya faru cikin dare ne yasa ba kowa ne ya sani ba har sai da gari ya waye,Mai martaba cikin kumburarren idanuwansa da basu samu bacci ba,ga tsantsar bacin rai a kwance a fuskar sa ya shigo cikin fada,inda hakiman da ministocin suke zaune suna jiran qarasowar sa,bayan ya zauna ne suma suka zauna,cikin bacin rai yake qare musu kallo kafin ya fara magana

"Jiya da daddare! Wani mummunan abu ya faru! Abu ne wanda ko a mafarki ban taba tunanin faruwar sa ba! Sun aikata babban laifin cin amanar qasa da kuma cin amanar karagar mulki,Saboda haka ba zan taba yafe musu ba akan hakan! Sun sakawa gidan consort Sook wuta,Sunyi tsafi domin hallaka Queen haneefah,sannan kuma a qoqarinsu na rufe laifukan da suka aikata,sunyi yunqurin hallaka Consort Sook da Prince Yeon! To duk wanda yake da hannu a cikin wadannan abubuwan,zan nemo dukkansu,kuma ko ma wanene shi,duk matsayin sa,duk alafarmar sa,tabbas sai sun biya abinda suka aikata da rayuwar su! Babu dayansu da zan bari da ranshi kowaye shi!"

ROYAL CONSORT 2Where stories live. Discover now