Page 45
Cikin rakiyar wasu 'yan sanda crown prince ya taho domin zuwa gidansu a bayar da tara sannan su sake shi,wani gida ya kaisu inda shima bai san ko'ina bane,kafin su ankara ya falla a guje ya fice ya bar gidan,fitowa sukai suma 'yan sandan suka bi shi da gudu,ji yayi an rufe bakin shi an ja shi gefen katanga har 'yan sandan suka wuce basu ganshi ba,sai da suka gama wucewa sannan abdallah ya sakar masa bakin,juyawa yayi ya ganshi
"Waye kai?"
"Kada kayi magana da qarfi your highness! Ni tribunal inspector ne!"
Inda su shukriyya suke ya taho dashi,tana ta ajiyar zuciya ta taho da sauri gaban crown prince ta rusunar da kanta
"Kana lafiya cheo-ha? Babu abinda ya same ka?"
Shima crown Prince rusunar da kanshi yayi yace mata
"Maamaah!"
Abdallah ne yace
"Babu abinda ya sameshi"
"Ki gafarceni,na saka ki damuwa"
Crown prince ya fadawa shukriyya,girgiza kai tayi"Ba komai cheo-ha! Ni ce da godiya tunda ka dawo lapia"
"Nagode your highness!"
Yace mata yana murmushi.Abdallah yace
"Zamu tafi tare da his highness zuwa masarauta"
"A'ah! Naji ance rashin ganin nawa ya kawo babbar damuwa a cikin masarautar,idan muka koma tare za'a iya samun rashin fahimta"
"Amma your highness.."
Shukriyya tayi magana"Maaaa-maaaah! Qanina Yeon zai iya shiga matsala saboda ni,ni na takura masa muka fito tare,kuma ba zan bari ya sha wahala saboda ni ba! Tunda kum ce shi ya riga ya koma,bana son ku bari kowa ya san tare muka fito da shi,Please maaamaaah!"
Sakin baki shukriyya tayi tana kallonsa,labari take ji a wajen noor yadda yayan nasa yake son shi,amma yau ta tabbatar da idonta.
Wucewa yayi ya bar wajen,abdallah yana bin shi a baya har suka koma palace.
............................
Yana shigowa palace dinshi ya ci karo da mamanshi,da sauri ta matso tana dudduba jikin shi
"Lafiya kake my son? Babu abinda ya same ka?"
"Yea ommou-neey! Lafiya ta qalau"
Fada ta fara yi masa
"Menene amfanin haka? Me yasa ka aikata abinda ka yi?""Kiyi haquri! Ina son na sha iska ne,shine na fita ni kadai,amma ban yi hakan don hankalin ku ya tashi ba"
Kallon tuhuma take masa
"Kai kadai kace? Kana qoqarin kare Prince Yeon ne?"
"Me kike nufi ommou-neey?"
"Na san komai! Na san tare kuka fita da prince yeon,Na san cewar shi ya saka ka fita wajen masarauta"
"A'aaah ommou-neey! Ni nace zan je! Ba shi bane"
"Kuma kana son in yadda da haka? In ba don shi ba ai baka taba fita ba ko?"
"Ommou-neey!"
Yayi maganar cikin rarrashi"Ba xan taba yafewa Yeon akan haka ba! Ya ja ka kun fita cikin gari domin kaima ka zama dan gararamba irin shi ko?"
Wani eunuch din shi ne a gefe yace
"Ki gafarceni your highness! Amma ki sassauta muryarki,muryarki tayi qarfi akan Cheo-ha"
(Suna nufin ko ita mahaifiyarsa bata isa tayi disrespecting din crown prince ba,don a dokar qasa ya fi ta matsayi,don ita consort ce ba sarauniya ba,shiyasa aka yi mata magana saboda fadan da take yi! Gyara kimtsi da kyau!)
YOU ARE READING
ROYAL CONSORT 2
Historical FictionCigaban labarin ROYAL CONSORT littafi na daya Labarin ROYAL CONSORT labarine irinshi na farko a cikin labaran hausa novel,labari ne na tarihi amma wani bangaren labarin qagagge ne,labarin ya qunshi mulkin mallaka,tsantsar qauna,tasirin qarfin iko,m...