Page 38

109 2 0
                                    

Page 38

Zumudi yake tayi yana tambayar chief eunuch

"Suna ina?"

"Yanzu suka fito daga gaishe da queen! Sun dauki hanyar komawa palace din su,ko a aika musu cewar su taho grand palace?"

"A'ah a'ahh bar su,ni zan je na gansu"

Bude baki chief eunuch yayi zai yi magana mai martaba ya hana shi

"Ba zan iya jira ba,ya kamata naje naga Prince,yau ne rana ta farko da zai ganni a matsayin mahaifin shi,ba zan iya jira ba,yanzu zan tafi"

Yana maganar kamar yaro yaga alawa,dariya chief eunuch ya qunshe yana kallon mai martaba.

......................

"Kin ce kin taba ganin babana ko? Ya yake?"

Prince noor yake tambayar aliya,kallonshi tayi

"Mai martaba? Chabb! Ai ko damisa ma bata isa tayi hargagi a gabanshi ba saboda kwarjinin sa"

Zaro ido noor yayi
"Kai? Haka yake da abin tsoro?"

Jinjina masa kai tayi

"Ehh mana!"
Ta bashi amsa,sunkuyar da kan shi yayi cike da damuwar yaya zai ga mahaifin nasa,shin ko zaiyi murnar ganin sa ma?
Nan da nan ya fada tunanin lokacin da dan sandan sirrin nan yace masa ai babansa bai manta da su ba,ajiyar zuciya ya sauke
"Ban sani ba ma ko dan sandan sirrin nan gaskiya ya fada min,idan kuma babana bai ji dadin gani na ba fa?"

Zuwa yanzu aliya ta bar wajen,shi kadai ne a zaune,mai martaba ne ya shigo sanye da kayan da noor ya saba ganinshi da su

"Kai dan yaro!"
Noor yana jin muryarsa ya tashi cikin murna ya nuna shi

"Kai! Dan sandan sirri! Kamar ka san yanzu tunanin ka nakeyi! Kai ma wajena kazo?"

Mai martaba ya kalli kayan jikinsa,sai yayi sauri ya duqusa yace

"Yes your highness! Naji labarin kana cikin masarauta shine na taho har da gudu na in zo in gaishe ka"

Shiru noor yayi ya sadda kanshi qasa

"Dama ina ta tunani,ka san yau zan ga babana amma ina cikin damuwa"

"Damuwa kuma? Akan me your highness?"

"Attendant din da na tambaya ta fada min babana yana da abin tsoro kuma yana da kwarjinin da ko damusa ba zata yi hargagi a gabanshi ba,ina tsoron kada nayi masa ba daidai ba ya hukunta ni"

Jinjina kai mai martaba yayi

"Ai kuwa fa!! Hukunci ko? Kuma fa ina tunanin hakan zai iya faruwa"

A tsorace noor yace

"Da gaske?"

"Ehh mana! Kamar yadda ka fada ai mai martaba abin tsoro ne,kuma amma kana magana cikin rashin da'a a gaban sa,kuma bayan wannan yana sarki amma ka tilasta masa yin dambe,kuma ka saka shi yayi wanka a ruwa! Lallai kana cikin gagarumar matsala"

Zazzaro ido noor yayi yana kallonsa,sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan yace masaa

"Me kake nufi da hakan? Ta yaya babana zai san maganar damben da wanka a cikin ruwa?"

Kafin mai martaba yace wani abu shukriyya ta taho tana qwalla masa kira

"Noor! Noor!!"

Hango mai martaba da tayi a wajen ya sa ta qaraso da sauri ta rusunar da kanta qasa

"Cheo-nah!"
Kallonta noor yayi cikin rudani,shukriyya tace

"Your majesty? Lafiya na ganka a cikin wannan kayan tare da Prince?"

ROYAL CONSORT 2Where stories live. Discover now