Part 9: CONSORT SUK
Page 37
A daren aka kawo wa mai martaba labarin gobarar,hankalinsa ya tashi sosai! Dawakai aka dauko ya taho da mugun gudu kamar zai tashi sama zuwa gidan shi na cikin gari inda shukra ta taba zama a shekarun baya,yau ma can aka kaisu.
Shukriyya taqi tsayawa a duba nata qunar da tayi a hannayenta saboda yadda prince yake a sume,kuka kawai take tayi har sai da ya farfado ta ganshi lafiya qalau sannan hankalinta ya kwanta.Fitowa tayi farfajiyar gidan ta baya riqe da qirjin ta don yau sunga mutuwa ido biyu,Allah yayi da sauran kwanan su a gaba,kuma ta tabbata aiko su akayi a saka musu gobarar.
Tana kallon yadda qunar hannunta tayi jajir,juyowar da zatayi ta ganshi a tsaye,a tunanin ta gizo ne yake mata
"Cheo-nah!"
Ta furta a hankali,a hankali ya tako zuwa inda take tsaye yana kallonta"Me kake....me kake yi a nan?"
Ta furta cikin rawar murya tana hawaye,hannu ya miqa ya goge mata hawayen"Shukriyyah! Da gaske kece.....ke....ce a tsaye a gaba na?"
Rungumota yayi da qarfin gaske yana kukan farin ciki,ita ma kukan takeyi.
............................
Cikin matsananciyar damuwa jaleela take zaune ta hada kai da gwiwa,cikin sassanyar murya chief maid dinta tace
"Your highness! Ya kamata ki tashi ki tafi bed chamber dinki domin kin kwana biyu ba ki samu bacci ba"
Murmushin takaici ta saki
"Bacci? Ina ma ace zan iya yin baccin?"Muryar nusaiba suka jiyo daga waje
"Your highness! Nusaiba ce!"
Kamar mai kuka,a razane jaleela tace"Me kuma ya faru a cikin daren nan?"
Chief maid ce tace"Zaki iya shigowa"
A sukwane nusaiba ta shigo
"Your highness! Ina da mummunan labari!"
"Menene shi?"
Jaleela ta tambaya cikin zaquwa"Mai martaba ya tafi wajen consort malak"
"Me? Me kika ce? Mai martaba ya tafi ina?"
Jaleela ta jero tambayoyin cikin rashin nutsuwa
"Gidan consort malak ne ya kama da wuta shine mai martaba ya tafi....ya tafi.....kuma ya ganta.....kuma..."
"Ki fada min magana mai ma'ana!!!"
Jaleela ta buga mata wata uwar tsawa
"Me kike fada? His majesty ya tafi ina? Wajen consort malak? Wane irin shirme ne wannan nake ji?"
Ta yi maganar kamar mai shirin fashewa da kuka........................
Mai martaba ya shigo dakin da noor yake kwance amma yayi bacci hakan yasa har ya tafi noor bai ganshi ba.
Shukriyya kuwa tana waje tana ta tunanin yadda mai martaba ya qaraso cikin qanqanin lokaci,guards din da suke tsaye ta kirawo tare da tambayar su yadda akai suka san suna neman taimako,rusunar da kanshi yayi
"Tsawon shekaru shida kenan muna gadin gidan bisa umarnin mai martaba,haka nan kuma duk inda zaku shiga ke da prince akwai private guards da suke tsaron lafiyar ku a sirrance! Kiyi haquri da rashin zuwan mu da wuri your highness!"
Suna gama maganar mai martaba ya fito daga dakin da noor yake,guard din ya matsa daga wajen shi kuma mai martaba ya qaraso inda take tsaye,hannunta da aka nade da bandeji ya riqe cikin tausayawa yace mata
"Kiyi haquri! Ni na jawo miki kika samu wannan ciwon! Ni na jawo muku komai! Ban taba son na cutar da ku ba! Nayi qoqarin na baku kariya matuqar qoqarina"
YOU ARE READING
ROYAL CONSORT 2
Historical FictionCigaban labarin ROYAL CONSORT littafi na daya Labarin ROYAL CONSORT labarine irinshi na farko a cikin labaran hausa novel,labari ne na tarihi amma wani bangaren labarin qagagge ne,labarin ya qunshi mulkin mallaka,tsantsar qauna,tasirin qarfin iko,m...