Page 31

105 3 1
                                    

Page 31

Haka har gari ya waye kowa sukuku yake,babu wanda ya iya runtsawa a cikin shukra da duk magoya bayanta,ita kam daren gaba daya tare tayi shi da qaramin yarima,yana wajenta har gari ya waye.

Da safe 'yan jiran qiris suka shiryo tsaf cikin alkyabbar su ta ministoci,a durqushe suke a gaban fada kamar masu neman gafara suna ihun roqon mai martaba

"Ka ji koken mu your majesty! Consort Malak ta aikata laifin da babu yafiya! Ita din 'yar shugaban qungiyar takobin matasa ce! Ta wulaqanta qasar mu,ta ci amanar gidan sarauta ta hanyar boye asalinta har ta shigo ta zama matar sarki!"

"Your majesty! Ka ji koken mu! Ka hukunta ta your majesty!"

"Your majesty! Kuma an kama ta tana qoqarin taimakon shugaban qungiyar na yanzu! Ka hukunta ta tare da sauran 'yan qungiyar akan laifin cin amanar qasa your majesty!"

Haka suka dinga maganarsu daya bayan daya kafin su hada baki dukkansu sun kai su 20 suna fadin

"Kaji koken mu your majesty! Kaji koken mu your majesty!!"

.........................

Consort hui,jaleel da kuma haj jameela a zaune a sitroom din consort hui cikin farin ciki,sai taya juna murna sukeyi,a nan jaleel yake sanar dasu ministoci suna can suna tunzura mai martaba,jaleela da har yanzu hankalinta bai kwanta ba tace

"Ya kamata ace abin yafi haka tsanani,domin bana son mai martaba ya samu wata hanyar da zai tserewa yanke mata hukunci!"

Girgiza kai jaleel yayi

"Ki kwantar da hankalinki your highness! Mai martaba ba zai iya share su na tsawon lokaci ba"

"Hakane! A qarshe dai shikenan mun kawar da matsalar mu"
Cewar haj jameela,dariyar qeta jaleel yayi

"Hakane! A yanzu dai kam zamu iya yin bacci cikin kwanciyar hankali,har da minshari"

......................

Ministocin guda uku suka shigo queen's palace cikin rawar jiki suka tsugunna,minister of state affairs ne ya fara bayani

"Your majesty! Ba'a kammala binciken ba tukunna! Amma bana tunanin akwai wata hanyar tsira don komai a bayyane yake game da consort malak! Bana tunanin zata iya tsallakewa hukunci!"

"A'ahh dole ne a san yadda za'ayi minister!"

Da mamaki ya dago ya kalleta

"Your majesty! Bana tunanin akwai abinda zamu iya yi"

Ran ta a bace tace

"Lallai ba consort za'a hukunta ba,don ba ita tayi laifi ba"
Miqewa tayi tsaye ta fita daga sitroom din,suma suka miqe suka fita.

........................

Tana zaune cikin rashin nutsuwa tana jiran a yankewa shukra hukunci ta huta aka kawo mata saqon zuwan queen haneefah,kafin ta miqe daga kan shimfidar zaman ta ma queen haneefah ta riga ta shigo,da sauri jaleela ta miqe ta dawo gefe ta rusunar da kanta,yayinda queen haneefah kanta a sama ta taka har zuwa kan shimfidar zaman jaleela,tattare alkyabbar ta tayi sannan ta lanqwasa qafafuwanta ta zauna,matsowa jaleela tayi tana fuskantar ta,ta rusunar da kanta qasa sannan ta dago,lanqwasa qafarta tayi itama ta zauna a qasa tana fuskantar queen haneefah.

"Your majesty!"
Jaleela ta furta a hankali tana kallon queen haneefah a cikin ido,kallon kallo sukewa junansu kowa da abinda yake tunani game da dan uwansa.

........................

Yana zaune yana ta jujjuya takaddun reports din da aka kawo,a ciki har da royal seal din consort malak da tayi amfani dashi wajen samun jirgi,ajiye takaddun yayi yace

ROYAL CONSORT 2Where stories live. Discover now