Page 21

101 4 0
                                    

Page 21

Jin an bude dakin da take zaune tun dazu ne ya saka ta daga ido don ganin me shigowa,fuska a daure yace mata
"Taso ki biyo ni!"
Sum sum ta tashi tabi bayanshi,tsakar gidan suka fito har zuwa qofar wani dakin sannan ya tsaya ya furta
"My lady! Na kawo yarinyar!"
Izini aka basu sannan ya bude qofar ya shigo Shukriyya tana biye dashi har cikin dakin da matar take zaune,kallo daya zakai mata ka tabbatar matar wani hamshaqin ce,tana zaune akan carpet din zamanta da kuma dan qaramin tebur a gabanta,rusunawa sukai su biyun suka gaishe ta kafin mutumin ya zaunar da shukriyya a gabanta,da murmushi take kallon yarinyar tare da furta
"Lallai kyakykyawa ce yarinyar! Kin san dalilin zuwanki nan wajen?"
Kanta a qasa shukriyya ta amsa da
"Ehh! My lady! An fada min kina son ganina ne saboda gaisuwar sabuwar shekara"
Yadda shukra take magana cikin nutsuwa ya burge matar sosai
"Hakane! 'Yata zata auri dan babban gida a qasar nan,kuma yarinyar da zata je gaisuwar ta kamu da cutar qyanda,na samu labarin cewar kina da wayo da hankali sosai shiyasa nace a kawo min ke!"
Cikin murna shukriyya ta rusunar da kanta
"Nagode! Nagode my lady! Kuma ba zan baki kunya ba"
Jinjina kai matar tayi har yanzu tana kallonta tace mata
"Ya sunanki?"
"Sunana Shukriyya Anas Abdulmalek"
"A wace unguwa kike?"
"Qauyen Banchon"
A razane matar ta kalle ta kamar mai mamaki
"Banchon? Kenan ke lowborn ce?"
Sunkuyar da kai Shukriyya tayi,cikin tsawa matar ta kalli mutumin da ya kawo shukriyya
"Wane irin hauka ne wanann? Ba nace maka freeborn nake so ba? Meyasa zaka je ka kwaso min lowborn?"
A firgice yayi qasa da kanshi ya fara bata haquri
"Haka kika ce my lady! Amma babu yarinya a cikin freeborn din da tayi daidai da kwatancen da kike nema,wannan yarinyar lowborn ce amma tana da ilmi da kuma hazaqa,ga..."
"Ya isa haka!!"
Ta katse shi da wata tsawar
"Ya isheka haka! Ka tashi ka fitar min daga nan kai da yarinyar!"
Shukriyya da yake ranta yana so da sauri ta fara bata haquri
"My lady! Ni lowborn ce amma zan iya yin yadda kike so! Ki taimaka ki barni nayi! Na roqeki!"
Hararar mutumin tayi
"Me kake jira ne?"
A diririce ya tashi ya fara jan hannun shukriyya zai fitar da ita,ita kuma tana turjewa tana fadin
"Ki taimaka my lady! Ni har na haddace gaisuwar ma gaba daya! Ina ta gwada yadda akeyi kuma na iya,tunda gani ki taimaka na karanto miki kiji!"
Yana ta kici-kicin ya fitar da ita matar tace
"Dakata!"
Tsayawa yayi,shukriyya ta fara sunkuyar da kanta ta fara godiya tun kafin ace an bata damar,takaddar matar ta miqo mata a hankali ta karba ta fara karantowa har zuwa inda ta kakare,da muguwar harara matar ta kalleta
"Iya hakan kika iya karantawa shine kike fadar kin iya komai?"
Zazzaro ido shukriyya tayi tana girgiza kai
"Aaa'aahh ba haka bane! Harafan chainan cin ba'a rubuta dai dai ba"
Duk da mamaki suke kallonta,nan da nan ta fara bayanin inda aka samu matsala da abinda ya kamata a saka a wajen,da sauri matar ta karbi takaddar tana dubawa,ai kuwa gaskiyar shukriyya ne,akwai kura-kurai da yawa a ciki,da muguwar harara ta kalli mutumin
"Me hakan yake nufi?"
"Ki gafarce ni my lady! Ban iya kalmomin chineese sosai bane"
Sai da ta gama zazzaga masa masifa sannan ta juyo da murmushi ta kalli shukriyya
"Wato ba karatu kadai kika iya ba,har chineese ma kin iya karantawa?"
"Yes my lady!"
Shukriyya ta bata amsa,wata maid aka kira ta tafi da shukriyya wani daki aka bata kaya na silk da yaran masu kudi da sarauta suke sawa,dama burin shukra bai wuce ta ganta a cikin wannan kayan ba,hakan yasa take ta murna duk da kayan sun dan yi mata yawa,maid din tace
"Kin yi kyau sosai! Ki cire sai na kai a rage yadda zasuyi miki cif-cif ko?"
Da murnarta ta cire kayan,bayan sun yi sai safiyar washegari zata zo domin zuwa gaisuwar ta fito daga gidan tana jin dadi da farin ciki.

Wasu mutane ne suke binta a baya cikin sanda bata sani ba,ta zo kan kwana kenan taji an rufe mata baki ta baya an janye ta zuwa wani lungu,tana daga ido taga abdulshakur ne,yayinda su kuma wancan mutanen gani kawai sukai ta bace,sun dudduba har sun gaji amma basu ga inda tayi ba,suna ta dube-dube suka fara jin saukar duka,sai da abdullahi yayi musu li-lis sannan suka gudu da qafafuwan su.

Yayinda baban Shukriyya yana can yana rarraba mutanen su kowa da bangaren da aka bashi don ganin sun bada kariya ga wanda suke tunanin za'a iya kaiwa hari nan gaba,kuma suyi amfani da wannan damar don ganin masu aikata ta'asar a cikin kowane irin lokaci,hakan yasa chief Suh yayi ta nemanshi amma aka nemeshi aka rasa a cikin garin,dama yana nemanshi ne domin yayi masa bincike akan gawar sojan tribunal din da aka biyo kurkuku aka kashe shi,domin hakan ya qara tabbatarwa chief Suh lallai mutanen da yake zargi ba fa su bane suke aikata kisan,akwai dai wani boyayyen abu a qasa,kuma jin cewar ba'a ganshi ba kuma 'yar shi ma shukriyya bata dawo gida ba tun da ta baro wajen chief Suh dazu,hakan ya daga masa hankali sosai.

ROYAL CONSORT 2Where stories live. Discover now