Part 6: THE ROYAL CONSORT

146 5 0
                                    

Page 17

Part 6: THE ROYAL CONSORT

Sameer shirye cikin kayan makadan masarauta na musamman,wanda sai za'ayi taro na musamman suke sakawa,busa sarewa yakeyi idanuwanshi sunyi luhu-luhu,manager ne ya qaraso inda yake ya buge kansa
"Kai lafiyarka qalau?"
Sauke sarewar da take bakinsa yayi ya kalli manager
"Ehh lafiyata qalau mana!"
Jijjiga kai manager yayi
"Kalleka fa kamar mai shirin mutuwa,kwanaki uku ba kai bacci ba fa! Kalli yadda idonka sukayi!"
Lumshe ido sameer yayi
"Ai to nadin Our lady.......ina nufin nadin sarautar Her highness ne fa,ina son na baje duk qwarewa ta ne"
Girgiza kai manager ya qara yi
"A wannan yanayin naka sai dai ka baje mata qwarewar shirmen ka,tashi ni kaje ka kwanta kai bacci!"
Kamar wani qaramin yaro sameer yayamutsa fuska
"Saura fa bai fi awa daya ba! Ni ka qyaleni nayi ta bitar abinda zanyi,kayi tafiyarka duk ka dame ni!"
Mayar da sarewar bakinsa yayi,amma maimakon ya busa sai gyangyadi ya fara,hannu manager yasa ya bugi kan shi,firgigit ya kalle shi tare da dadumar sarewar sa ya cigaba da gashi
"Ni ba bacci nake ba fa! Ka tafi kawai!"

QUEEN's palace

Chief maid ce ta ajiye nannadaddiyar takaddar da aka manna ta da wata fata mai adon fulawoyi
"Ga Royal decree din da aka aiko daga royal secretriat"
Da tsananin farin ciki queen haneefah ta dauka ta bude
"Naji dadin kasancewar ni zanyi mata nadin sarautar nan da hannu na,haqiqa yau ranar farin ciki ce! Ta shirya ne?"

Tana quaters dinta tana daddaga kayan sawa na alfarma da sabuwar alkaybbar ta mai mugun kyau ta CONSORTS,su basma da aliya sai zuzuta kyawun kayan sukeyi,dafa fuskarta tayi tacewa basma
"Amma kamar na saka powder da yawa ko?"
Aliya da ba ita akaiwa tambayar ba ta cafe
"Your highness! Yanzu fa dole ki dinga yi mana magana a matsayin na qasa dake,saboda kada ki sa mu a matsala"
Murmushi tayi
"Toh my lady!"
Dariya suka sheqe da ita,da sauri Shukra tace
"Ina nufin Toh! Naji!"
Wata dariya suka qarayi,Aliya tace
"Zaki dinga jin baki saba ba,amma haka zaki dinga yi har ki saba your highness! Kinga yanzu ke ROYAL CONSORT ce"
Hannu shukra ta sa ta toshe bakinta kamar me jin tahowar amai,amma ba tai aman ba,hankali tashe duk suke tambayarta lafiya,dan dukan qirjinta tayi
"Qamshin powdar da na saka ne ya sa zuciyata take tash...."
Kafin ta qarasa ta qara jin tahowar aman,qara toshe bakinta tayi da hannu,basma ta zaro ido waje
"Your highness! Ko dai...Aliya! Je ki kirawo Royal doctor"

GRAND PALACE

Cikin farin ciki chief secretary yake sanar da mai martaba yadda shirye-shiryen suke tafiya,chief eunuch ne ya shigo da farin ciki ya rusuna,mai martaba ya tambaye shi
"Lady malak ta shirya zuwa Queen's palace din ne?"
Girgiza kai chief eunuch yayi
"A'ah your majesty! Ina ganin sai an dan qara lokacin akan yadda aka tsara"
"Qara lokaci kuma? Meyasa?"
Qasa yayi da kanshi
"Bata jin dadi ne,royal doctor ma yana can yana duba ta"
Zabura mai martaba yayi a zaune,tare da saurin miqewa ya fita.

Queen haneefah tana zaune a gaban shimfidar da likita yake duba shukra,cikin damuwa take cewa likitan
"Ka tabbatar ka duba ta sosai,me yake damunta?"

Mai martaba yana shigowa quaters din ya tarar da queen haneefah da kuma sauran attendants din a bakin qofar sitroom,hankalinsa a tashe ya qaraso,yayinda queen haneefah da duk wanda suke wajen suka rusunar da kansu qasa
"Your majesty!" Ta fada da murmushi,da damuwar da take kwance akan fuskar sa yace mata
"Ina lady malak din? Jikin nata da sauqi?"
Dagowa queen haneefah tayi ta kalleshi tare da girgiza kai
"Babu sauqi fa your majesty!"
A zabure yace
"Me? Babu sauqi? Me yake damunta?"
Murmushi tayi mai sauti tare da cewa
"Congratulations Your majesty! Lady malak tana da juna biyu"
Cikin murna yace
"Me kika ce my queen? Kikace tana da juna biyu?"
"Yea cheo-na!"
Kowa a wajen murmushin farin ciki yake yi,attendants din Shukra,na queen haneefah,da na mai martaba gaba daya,kada ma chief eunuch yaji labari,kowa farin ciki yake taya mai martaba,a tare suka hada baki suka ce
"Congratulations your majesty!"
Suna fada suna rusunar da kansu qasa.

ROYAL CONSORT 2Where stories live. Discover now