Page 7

155 7 0
                                    

Page 7

Basma da nadeeya jikinsu a sanyaye suka shigo wajen shukra,sai da suka tsaya suka rusunar da kansu sannan suka durqusa suka zauna,da murmushin ta tace musu
"Ya jikin yaran?"
Nadeeyah cikin sanyin murya tace
"Yanzu tunda munsan dalilin cutar,an fara yi musu maganin da ya kamata"
"Hakan yayi kyau sosai"
Shukra ta fada har yanzu fuskarta da murmushi,basma cikin bacin rai tace
"Babu fa abinda yayi kyau my lady! Mune fa muka samo cewar LEAD ne a cikin powdar amma gashi nan duk Queen jaleela ta qwace ladan komai kamar ita tayi qoqari ta nemo! Kuma bayan wannan ma yanzu duk mutane zasu dinga tunanin ta nemo gaskiyar ne domin ta fitar dake,kowa yanzu zaiyi tunanin sonki take yi"
Da gaske take masifar tayi kicin-kicin,dariya ta bawa shukra sosai,bayan ta gama dariyar tace
"Ni ai ina ganin tunda dai har an gano gaskiyar...."
"Bana tunanin gaskiyar kenan my lady!"
Nadeeyah ta katseta,kallon rashin fahimta shukra tayi mata
"Har yanzu baki san halinta ba? Ina ganin wannan shirin ta ne tun farko,ita ta shirya komai kuma da yadda zata fitar da kanta,ni abinda yafi damuna ma da ya kasance na fadawa mai martaba abinda muke tunani,yanzu na san zai rikice ne domin maganarmu sunci karo da juna"

GRAND PALACE

Ai kuwa yana zaune yana ta tunanin yadda jaleela tayi domin nemo gaskiyar,kuma sannan menene dalilin su nadeeyah na cewa suna tunanin haj jameela tana da hannu a ciki,lallai akwai wani boyayyen abu a cikin lamarin nan.

Bayan su nadeeyah sun tafi tana zaune take tunanin yadda jaleela ta gama raina musu hankali gaba daya,tunanin kalamanta na qarshe take yi a lokacin da taje wajenta neman alfarma
"Me kike tunanin dalilin da yasa ake aikata hakan tun farkon tarihi? Saboda MULKI ne! Saboda QARFIN IKO! Amma na tabbata zaki fahimta nan ba da dadewa ba cewar baki da wani qarfin iko kuma ba zaki iya tsinana komai ba!!!"
Bayan ta dawo daga tunanin ne ta miqe tare da fita zuwa queens palace,bayan anyi mata iso ta shigo ta zauna tana fuskantar jaleela,cikin halin ko'in kula jaleela tace
"Idan ma godiya kika zo yi min ai ina ganin babu buqatar hakan! Domin babu wata alaqar da zata sa mu dinga 'yan qananun hira marasa muhimmanci tsakanin mu"
Sauke ajiyar zuciya shukra tayi
"Ba godiya nazo ba! Kawai dai ina buqatar sanin dalilin da yasa kikai haka? Shin da gaske kin nemo gaskiyar ne saboda ni? Domin in dai don ni kikai....."
Dariyar da jaleela ta saka ne ya katsewa shukra maganarta,dariya jaleela takeyi harda tuntsirawa gefe,idonta ya ciko da ruwa tsabar dariyar mugunta,dan yatsan ta ta daga ta nuna shukra
"Lallai! Ke tsakaninki da Allah kike min wannan tambayar ko? Kiyi haquri ai dole ce ta sani dariyar"
Jikin shukra duk yayi sanyi,a hankali tace
"Your majesty!"
Jaleela cikin murmushi tace
"Kin san kin taba fitar dani a cikin irin wannan matsalar a shekarun baya!Ba kince zakiyi amfani da damar da kike da ita ba domin yin abinda ya dace? Toh ki tsaya kiyi kallo domin ki koyi yadda akeyi,nan masarautar ba wajen yin abinda ya dace bane! Nan wajene da ake mayar da abinda bai dace ba ya zama wanda ya dace,To idan kina son kici galaba akaina,kuma kina son ki dawo da korarriyar sarauniya kan wannan matsayin,to karki yadda ki sake nuna min wannan damammiyar fuskar taki! Ina fatan kin fahimceni,domin THIS IS JUST THE BEGINNING! Yanzu aka fara wasan"
Huci shukra takeyi tana sauke ajiyar zuciya tana kallon idon jaleela,cikin sanyin jiki ta miqe ta fito tana daga qafarta da qyar.

Waahegari da safe cikin shigar kakin kayan aiki chief Suh da abdullahi suka shigo,da murnarta ta fito da gudu baki har kunne tace
"Orabeuni"
Suna ganin ta fito suka dakata da tafiyar tare da rusunar da kansu qasa sannan suka dago,Abdullahi yace
"Maa-maa-neem!"
Tana cikin tsananin farin ciki ta juyo ta shigo ciki suka biyo bayanta,zama tayi akan shimfidarta suma suka zauna suna fuskantar ta,Abdullahi ne ya fara cewa
"Munji labarin abinda ya faru a acikin masarautar,da fatan dai yanzu komai ya daidaita"
Jinjina kai tayi
"Komai yayi dai-dai,kada ku damu"
Chief Suh yace
"Meyasa sai da bama nan abu irin wannan ya faru?"
Kawar da zancen tayi da tambayar
"Ina yallabai Naseer? Baku taho tare da shi bane?"
"Mun ajiyeshi a wani wajen,idan lokaci yayi zamu shigo dashi cikin masarautar"
Chief Suh ya bata amsa
"Naji dadi! Hakan yayi dai dai,kaga yanzu tunda kun dawo na tabbata mun samu hujjar da zata tabbatar da laifinsu"
Sunkuyar da kai sukai dukkansu babu wanda yace komai,jikinta ne yayi sanyi
"Ya na ga yanayinku haka? Me yake faruwa? Akwai wata matsala ne?"
"Mun samu labarin zuwan tawaga daga china domin kawo sahalewar matsayin yarima mai jiran gado"
A firgice tace
"Tawagar china? Kawo sahalewar yarima mai jiran gado?"
Jinjina kai abdullahi yayi
"Haka muka sanu labari"
"To amma ai registration archive din da aka basu na bogi ne,ya akayi suka kawo sahalewar?"
Shukra ta tambaya a rude
"Bamu san ya akayi haka ba,amma dai matuqar aka tabbatar da matsayin yaron a yarima mai jiran gado to lallai zasu tsallake hukuncin laifukan su,kuma sannan a matsayinsu na wanda suka hada jini da yaron,qarfin ikonsu zai qaru sosai"
Zaro ido tayi a gigice ta dauko littafin registration archive din ta bude
"Yanzu kenan! Yanzu kenan kana nufin wannan ma duk sun zama aikin banza kenan? Sun zama marasa amfani?"
Sunkuyar da kansu sukai qasa don basu da amsar tambayar ta.

ROYAL CONSORT 2Where stories live. Discover now