Free page 4
*FIL-HUB*♥️
(Acikin so💘)
Paid Book: N500
Written by
Billy s fari💎
______________________________
Ɗan murmushi ya saki kafin yace, "Ai kin ji, matsala ta dake kenan, komai naki na kuka ne, zaki matso ne ko kuma nazo da kaina na duba ƙafar?"Jiki a mace ta taso tana goge hawayen da har sun zubo mata akan fuska da hannu ta zauna a ƙasan gadon da yake zaune akai ta tura masa ƙafar tare da kauda kanta gefe, taɓe baki ya yi haɗe da kallon Mahmah ya gaida ita sannan ya ce ta bashi maganin daya zo dashi jiya da za a sake shafa mata, hannu ta miƙa kan madubi ta ɗauko ledar maganin ta miƙa masa tana faɗin,
"Ai naga ƙafar ma da sauƙi alhamdulillah."
Daidai lokacin wayarsa tayi ringing ya ciro daga gaban aljihu haɗe da karawa a kunnensa ya ce, "Good morning ya Haisam"
"Morning Hisham, kun tashi lafiya?"
"Lafiya klw, yasu Ammie da Ailat."
"Lafiya klw suke, ya jikin Madiyam?"
"Ta ji sauƙi?" Ya faɗa tare da saka wayar handsfree ya ajiye a gefen gadon haɗe da riƙo ƙafar tata yana faɗin, "Mahmah sammana kaɗa." Daidai lokacin shi kuma Haisam ya ce "ba Madiyam wayar?" Kallonta ya yi ganin yanda ta washe baki jin muryar Haisam daya ce a bata wayar haɗe da cewa, "Yi maganar ka tana jinka"
"Hello Madiyammm.." Haisam ya faɗa yana wani jan sunan cike da shauƙi, ɗan runtse idanuwa Hisham ya yi jin wani abu ya dakar masa a zuciya haɗe da buɗewa ya saukar dasu akan fuskar Madiyam da sai faman dariyar dake nuna jin daɗin Muryar ya Haisam ɗin da tayi takeyi haɗe da cewa,
"Laa..ya Haisam ina kwana?"
"Lafiya klw ƙanwata".
"ALLAH kafi kowa iya faɗan sunana ya Haisam".
"Da gaske kikeyi Madiyammm" ya sake daɗi fiye da yanda ya kasa ɗazu, sai data yi dariya sannan ta ce,
"Wlh kuwa, kuma ya ma fi daɗi abakinka idan ka faɗa, ina Aunty Ailat da Ammie."
"Duk suna nan lafiya suna gaisheki"
"Ina amsawa".
"Ya ƙafar taki inji da sauƙi?"
Sai data kalli Hisham daya riƙo ƙafar yana goge dattin dake sama da kaɗar da Mahmah ta miƙo masa sannan ta ɗan turo baki haɗe da cewa, "Eh da sauƙin ya Haisam ɗazu, amma yanzu gashinan ta fara ciwo."
"Ayya srry zata dena kinji ko?, kina dai shan magani?"
"A'a shafawa kaɗai akeyi" ta faɗa tare da fashewa da kuka jin yanda Hisham ke shafa mata maganin yana murza wajen sosai, saboda wani abu da yake ji na taso masa azuciya, uwa uba daya ji tana faɗar wai yanzu ƙafar ta fara ciwo tsabar ta rena masa da wayau, kenan don ta riƙa ƙafar shiyasa tafara yimata ciwo?, hakan ya sake tunzurasa ya cigaba da murzar ƙafar yana shafa maganin da ƙarfi, jin kukan ta ya sa Haisam ruɗewa haɗe da tashi daga kwancen da yake yana cewa, "ƙanwata lafiya?, meya faru kike kuka kuma? no kidena pls bana son jin kukanki kinji ko?"
"Ya Hisham ne.." ta faɗa tare da kasa ƙarasawa ganin yanda yake wurgo mata wata shegiyar harara,
"Yaya Hisham ne ya yi maki me cutie?"
"Ba komai" ta faɗa tana sadda kanta ƙasa,
"Shikenan barni dashi kinji ko, yi haƙuri ki goge hawayen gobe zanzo na dubaki, me kike so nazo maki dashi."
"Ni bana son komai" ta faɗa cikin shagwaɓa tana goge ƙwallan,
"Haddani bakya so?"
"A'a ina sonka"