Free page 1
*FIL-HUB*♥️
(Acikin so💘)
Paid Book: N500
Written by
Billy s fari💎
______________________________
Tunda ta hangosa gabanta ya yanke ya yi wata irin muguwar faɗuwa tayi saurin sadda kanta ƙasa tana jin ƙafafuwanta na sassarƙe mata waje ɗaya, ga wani irin nauyi da suka yi mata da take ganin daƙyar idan zasu iya ci gaba da ɗaukarta balle har su ƙarasa da ita inda ta nufa, yaushe ya Hisham ya dawo kuma? Ta tambayi kanta cikin zuciya tana ji tamkar ta fashe da kuka, iya adadin matsowar da takeyi a kusa dashi iya adadin bugawar da zuciyarta ke ƙarayi, ALLAH ma ya sani bata son ganin wannan bawan ALLAHn don ita kaɗai tasan irin yanayin tsoron da take tsintar kanta aciki, musamman yanda yake yimata wani irin kallo akoda yaushe idan suka haɗa idanuwa, sai taji kamar ta nitse cikin ƙasa saboda tsananin tsoro da tsabar firgita, jikkar littafanta na islamiya ta saka akan ƙirjinta ta rungume ko zata samu ƙwarin guiwar iya ci gaba da tafiya har ta ƙaraso ta gabansa zata wuce, da sauri ta rintse idanuwa sosai tana sake rumƙe littafan dake rungume a ƙirjinta saboda yanda zuciyarta ke halbawa kamar zata fito tayi saurin sinne kanta ƙasa, wata uwar tsawa taji ya daka mata haɗe da cewa "Wai ke wace irin baƙauyar yarinya ce? Ina kika taɓa ganin inda ake tafiya da idanuwa arufe ɓacin mutum na gani in ba sakalci ba?" Ba tare data kulasa ba ta wuce cike da tsoro tana sake ɗaga ƙafafuwan ta da sauri da sauri har lokacin idanuwanta na arufe, ai kuwa bata ankara ba taji ta bugi wata bishiyar icce dake gaban ƙofar gidan nasu, wata irin ƙara ta saki haɗe dayin baya zata faɗi ƙasa saboda wasu irin taurarin azaba data gani sun mamaye mata gaba, jin tayi anyi saurin tare ta tare da riƙota kafin takai ƙasa, wanda hakan ya sa tayi saurin buɗe idanuwa tare da juyowa, karaf idanuwanta suka sarƙe da nashi yana dalla mata wata irin hararar da ta sata saurin maida idanuwan ta rufe haɗe da ƙoƙarin zare jikinta daga riƙon daya yimata jikinta na rawa saboda tashin hankali, dama abunda take gudu kenan kuma gashi ya faru, ta faɗa cikin zuciyarta tare da sauko da hawayen da tun ɗazu suka cika mata idanuwa, ƙin sakinta ya yi ganin yanda take kokuwar ƙwace jikinta har lokacin idanuwanta na arufe tare da ƙarewa kyakkyawar fuskar tata kallo na tsawon sakanni uku ba tare daya damu da mutanen dake wucewa wajen dake kallonsu ba, sai daya rabar data ɗan saki jiki ganin yaƙi cikata sannan ya saketa ta faɗi ƙasa timm...tare da juyawa ya yi tafiyarsa ya barta wajen ƙasa a yashe, cike da jin zafin faɗuwar da kuma gigicewa ta miƙe ta nufi cikin gidan nasu tana maka masa ALLAH ya isa a cikin zuciya, tana ɗaga ƙafarta don ta tsallake kwalbatin dake bakin ƙofar shiga gidan nasu taji tsumbul ƙafarta ta zame ta faɗa ciki, wata irin ƙara ta sake saki da ƙarfi data sashi saurin juyowa daga can cikin gungun abokanansa da yake zaune haɗe da tasowa ya nufo wajen, a hasale ya fisgota daga cikin kwalbatin yana watsa mata wani irin mugun kallo kafin yace,"kin gani ko? Abunda nake faɗa maki kenan amma bakya fahimta, ALLAH ya ƙara maki tunda kunnen ƙashi ne dake". ya ƙare maganar cikin jin haushi yana kallon ƙafar tata da har ta ɗan gurje jini ya soma fita, runtse idanuwansa ya yi ya kauda kansa gefe haɗe da cigaba da cewa "Ai shikenan sai ki buɗe idanuwan yanzu ki tashi ki shiga ciki tunda kinci riba, in yaso idan Mahmah ta tambayeki sai ki faɗa mata cewa garin kallon samarin waje kika faɗa cikin kwalbati". fuskarta shaɓe-shaɓe da ƙwalla take sauraren faɗan nasa cike da jin haushi tana ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa tashi, komawa tayi ta zauna ƙasa tare da fashewa da kuka ta ce "wayyo Abbu.." kafin ta ƙara sa ya ɗaga hannu kamar zai daketa cike da takaicin jin taɓarar da take ƙoƙarin fara yiwa mutane data saba, abunda ya tsana kenan dake haɗa shi da ita akoda yaushe,"ki rufe wannan ƙaton bakin naki kona makeki a wajen, zaki tashi ne ko kuwa sai na makeki a wajen?"
"Wayyo ƙafata, wayoo Abbu". Ta sake faɗa tana dafe saiti ƙafar tata dake yimata zafi, tsaki ya yi haɗe da duƙawa ya tallabota daga ita har jikkar littafan tata ta islamiya dake gefe ya nufi cikin gidan da ita yana kallon yanda ta wage baki tana kuka sai kace wata ƙaramar yarinya, yana shiga Mahmah dake fitowa daga bayi riƙe da buta a hannun tayi saurin ƙarasowa wajen tana faɗin,