💫💫💫💫
_*MEE'AD*_
💫💫💫💫***CONTINUE***
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞
( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*THE BOOK IS WRITTEN*
*BY*
*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*
Follow me on wattpad
👇👇👇
@hauwancyy44JINJINA & SADAUKARWA
Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .
√√√√√ MEE'AD fan's kuyi hakuri da rashin post akan time, sbd wasu dalilai. √√√√√√
**** Pls don't forget to vote, share & comments 👌 love u fan's 💯%.
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️
Ina kuke masu son DATA ? ku taho da hazanri ku saya dan kuma nazo muku da Data a sassaukan rahusa idan kuna bukata📶 *MTN*📶
*500MB* 👉🏽 *#150*
*1GB* 👉🏽 *#300*
*2GB* 👉🏽 *#600*
*3GB* 👉🏽 *#900*
*4GB* 👉🏻*#1200*Mai bukata ya tura ta wannan account number
👇🏻👇🏻👇🏻3142669195 Hauwa Ibrahim First Bank .
Idan ka tura saika tuntubeni ta wannan number
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
09039285813.Ga masu buƙata akwai Glo da Airtel da kuma 9mobile.
Masu bukatan data maza kuzo ga dama tazo muku har gida.
🎃🎃🎃
Thank you for contacting Hauwa Misau! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE.
I am selling MTN data with cheap price.
MTN DATA PACKAGE
500mb ~ *#150*
1GB ~ *#300*
2GB ~ *#600*
3GB ~ *#900*
4GB ~ *#1200*Dial *146*4# Check data balance VALIDITY 1 MONTH.
Airtel, 9mobile, Glo also available.
You Can Pay Through Bank Transfer Or Cash
3142669195
Hauwa Ibrahim First Bank.Call or chat for more information ; 09039285813.
61 ~ 62
Yace keee dakata! Kinzo ki ƙara jaddada mini cewa kin yanke igiyar soyayyar dake tsakanina dake ne ko mi kikazo ki faɗa mini ?
Wallahi ban ta'ba tsammanin zaki iya duban idona kice baki sona ba.
Hmmm! Amal a matsayinki na yar uwata bai dace ki dubeni cikin ido ki furtamin kalmar baki Sona ba, Amma babu komai na fahimci wajenda kika sa gaba kuma Insha Allahu zanyi iya bakin 'ko'karina wajen ganin an d'aura miki Aure da wanda kikeso. Yajaa dogon numfashi kafin ya nuna mata hanyar fita yace zaki iya fice mini daga falona ko Malama ?.
Tashi tayi ta nufi kofar falon jiki a sanyaye, juyowa tayi Yaya dan Allah ka ro'ki su Daddy su Amince da Aurena da wanda nakeso sbd shid'in Farin cikinane kuma ina jinsa a jikina fiye da ko wani d'a namiji indai a fannin soyayyane.
Ya gyad'a kai cikin 'kaguwa yace y'an mata bakida matsala indai akan wannan zancen ne kisa a ranki bazaki taba auren wanda bakiso ba, Dan haka zaki iya tafiya, jiki babu kwari ta nufi kofar fita zuciyarta faal Farin ciki.
Yabi bayanta da kallo yayi yana kad'a kai zuciyarsa cike da kuna.
10;30pm Majeeed zaune bisa kujera hannunsa ri'ke da cup d'in tea, wayar dake gefensa tayi ruri a hanzarce ya d'auka yana fad'in Assalamu Alaikum Ina yini Daddy ? Daga d'aya bangare Daddy ya amsa da lafiya klau sannan yaci gaba da cewa Babana ka samemu a falon 'kasa munason yin magana daku, yana gama fad'in haka ya gimtse wayar a hasale.
'Bangaren Majeeed kuma cike da fargaba ya ajiye cup d'in hannunsa ya nufi falon Daddyn.
Da sallama ya shiga falon baiyi mamakin ganin d'aukacin mutanen gidan zaune a falon ba 'a cikinsu kuma hadda Hajiya Hindu da Mee'ad wad'anda baisan da zuwansu cikin gidan ba, jiki a sanyaye ya 'karasa cikin falon gamida samun waje ya zauna a gefen Hajiya Hindu.
Shirune ya biyo bayan zaman da yayi kafin daga bisani Daddy yayi gyaran murya ya fara jero bayanai kamar haka, " Da farko dai Ina godema Allah daya bamu ikon taruwa a wannan wajen sannan kuma Ina godema Mahaifiyar mu data 'karfafa mana gwiwa wajen ganinta 'karfafa mana dan'kon zumuncin da yayi 'ko'karin yin tangarda, Amma Alhmdlh komai ya tafi yadda mukeso cikin iko da kuma izinin ubangiji ," yajaaa dogon numfashi kafin yakai duba a gefen da Amal ke zaune bisa ga mamakin naji yace Amal ki kwantar da hankalinki Insha Allahu za'a aura Miki wanda kike 'kauna kinji ? Da taimakon d'an uwanki Majeeed na shafe duk wani 'bacin rai 'kunci dama dukka haushinki daya ziyarci zuciyata a yinin yau kuma ina mai Yi miki albishir da cewa kice ma wanda kikeso ya turo magabatansa ayi maganar aure nan da 1month, yana gama maganar ya 'kura ma Amal d'in ido dan jiran mi zatace .
Amal ta san dakai cike da kunya da zumud'i ta fara wasa ya yatsun hannunta, Umma ce tace Alhmdlh Ina mai godema Allah da kuma Majeed wanda sanadinsa y'ar uwansa zatayi Auren farin ciki, ta dubi Majeeed d'in fuskarta cike da Farin ciki tace Allah yayi maka 'albarka yasa ka gama da duniya lafiya ya kuma Yi maka za'bin alkairi Ameeeen.
Shirune ya biyo bayan maganar da Umma tayi, Abba dake zaune a gefen sai a wannan lokacin yayi gyaran murya cike da hamdala ya dubi Majeeed dake gefe cikin farin ciki yace Allah yayi maka albarka da ka zamo silar gyara zumuncin da ya saura 'kiris ya tintsire Allah yasa ka gama da duniya lafiya, muna alfahari da samu irinka acikin zuri'ar mu Allah ya albarkaci rayuwarku baki daya Ameeeen.
Shirun da Abba yayine ya bama Hajiya Hindu daman yin magana cikin farin ciki tace Allah ya albarkaci wannan zuri'ar tamu baki d'aya, dukansu suka amsa da 'ameen, daga bisani Hajiya Hindu ta kira sunan Majeeed da kakkausar murya ko kasan hukuncin da muka yanke bayan shawo kan wancan matsalar ? Majeeed ya jijjiga kai da 'alamar bai sani ba, gyara zama Hajiya Hindu tayi sannan tace mun zauna mun yanke shawarar hadaka da y'ar uwanka a karo na biyu wato MEE'AD! Damm yaji gabansa ya yanke ya fad'i yayinda ita kuma Mee'ad d'in ta dago kai fuskarta cike da 'alhini da dumbin mamaki.
Murmushi Hajiya Hindu tayi kafin tace dafatan bazaka watsa mana 'kasa a ido ba ? Kuma ina fatan Allah yasa ka kar'bi wannan yar uwan taka da hannu bibbiyu.
Majeeeed yajaah dogon numfashi kafin yace Hajiya Insha Allahu bazan taba baku kunya ba kuma nasan bazaku tabayi min za'bin maras kyauba na amshi abinda kuka bani da hannu biyu Allah yasa hakan ya zama alkairi.
Ameeeen sukace baki d'ayansu, nan sukaci gaba da tattaunawa akan matsalolin da dama, basu bar falon meeting dinba sai 12am, nan sukayi addu'ah kowa ya nufi makwancinsa a ciki harda Mee'ad da kuma Hajiya Hindu.
Kai tsaye part d'in Hajiya Hindu na cikin gidansu Mee'ad suka nufaa, sai da suka tabbatar Hajiya da Mee'ad d'in sun shiga kafin suka wuce nasu part d'in.
Mee'ad tana shiga ta nufi bed room d'in gefen na Hajiya Hindu ta rage kayan dake jikinta bathroom ta nufa tayi wanka sannan ta d'auro alwala danyin nafilan nan da kuma Addu'ar istikhara.
Shima Majeeed d'in yana komawa part d'insa alwala ya d'auro ya fara nafila.
Ita kuma Amal tin lokacin da taji Mee'ad ta maye gurbin data bari ta cika da mungun ba'kin ciki kuma tayi al'kawari a kan bazata ta'ba barin Auren Mee'ad da Majeeed d'in ya kasance ba.
Mai karatu biyoni kasha labari kuma Insha Allahu na dawo da rubutun littafina na MEE'AD har ranar da ubangijina zai nufeni da 'kare littafin taku har kullum yar mutan Misau.
pls
Follow
Share
Vote
Comment
Fisabilillah 🙏🙏🙏.
YOU ARE READING
MEE'AD
ActionLove story💕 heart touching 🤔😍 follow me an read more...😊😊😊 Taku har kullum Hauwa Ibraheem Misau pls fans don't forgot to read, vote an share.