*ZAFIN HAWAYENA*
'''A True Life Story'''
_Wattpad@SaNaz_deeyah_*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link
SUBSCRIBE to our youtube channel👇https://youtube.com/c/KARAMCITV
Book2
'''Page 20'''Yana driving kiran Momma ya shigo wayar, ɗagawa yayi cikin kasalalliyar murya ya ce "Momma na san Sumayya ta kawo ƙarana ne"
"Eh ai kaima ka san kayi ba dai-dai ba, dan haka ka dawo yanzu ina nemanka"
"Har na kusa fita daga kano, zanje Abuja ne ana nemana urgently"
"Fauwaz a wannan yammacin zakayi tafiya, amma dai ba da mota ba, zaka bi jirgi ko?"
"Momma ban riga nayi booking ba, kuma bana son damar nan ta suɓuce min, ke dai kiyi min addu'a"
"Allah ya kaika lafiya, amma dai karka sake ka dawo yau, ka samu hotel ka kwana bana son tafiyar dare kai ka sani"
"Okay Momma, insha Allah"
"Yauwa, kuma kana sauka ka tabbatar ka kira Sumayya ka bata haƙuri kaji ko?"
"Eh Momma insha Allah zanyi hakan"
"Allah ya tsare"
"Amin ya rabbi."Suna gama waya da Momma, yayi dialing number Amatul'ahad.
Tana zaune a ɗakinsu tana tsifar kai, kiran Fauwaz ya shigo, cikin fara'a ta ɗauki wayar tare da ɗagawa ta manna a kunne.
"Yanzu nake tunanin kiranka" Ta faɗa cike da fara'a.
Shi kuwa da yake cikin jin haushinta yake, a daƙale ya ce "Ina hanyar zuwa Bauchi"
"Bauchi kuma, hala wani aikin zaka zo?"
"Oh sai dole aiki ne zai kawoni, to gurinki zanzo"
"Naji kamar muryarka da damuwa lafiya?"
"Kin ga driving nake, idan nazo zan kiraki" Bai ma jira abinda zata faɗa ba ya katse wayar.Shiru tayi tare da luluwa duniyar tunani, sam ta rasa dalilinsa na yin hakan, tayi duk tunanin da zatayi amma bata gane dalilin fushinsa ba.
"Idan yazo zanji dalili, yanzu haka Zayyan ne ya ɓata masa rai" Ta ja tsaki sannan ta cigaba da tsifar kanta.*3 Hours Later*
Awoyi uku ne suka kaishi Bauchi, saboda gudun da yake ta shararawa, a wani masallaci ya tsaya yayi sallar magrib sannan kai tsaye ya wuce school ɗin su Amatul'ahad.
Gaban hostel inda babu mutane sosai, anan yayi parking, har a lokacin ransa a ɓace yake.
Wayarsa ya ɗaga ya kira numberta. Tana ɗagawa ya ce "Ki fito ina waje, daga ƙofar hostel"
"Wai dagaske ko da wasa?"
"Na taɓa miki irin wannan wasan?"
"Wow! Gani nan yanzu kuwa."
Da zumuɗi taja gyalenta ta fesa turare sannan ta fita.
Idanu ta riƙa wurgawa har ta gano inda yake, sannan ta ƙarasa da ɗan saurinta.Buɗe motar tayi ta zauna a owner's seat tare da faɗin "Ina yini"
"Waye Sultan?" Shine abinda ya tambaya bai ko amsa gaisuwar ta ta ba.
Mamaki ne ya cikata, ta kalleshi tayi murmushi sannan ta ce "Ina fatan ba shine abinda ya kawoka Bauchi ba"
Cikin faɗa ya ce "Tambayarki nake waye Sultan?"
"Haba Fauwaz, yanzu akan wannan tambayar ka taho tun daga Kano, ai da ka kirani sai muyi maganar a waya ma"
"Amatul'ahad kina nufin kin ɗauki maganata a matsayin wasa? Kin ɗauka wannan magana ce ta waya? Kina tunanin ko daga Lagos ba zan iya tahowa akan wannan maganar ba."
Murmushi ta sakeyi sannan ta ce "To wai wane ya faɗa maka?"
"Amatul'ahad tambayarki nayi, kuma amsa nake nema"
Wasa ta farayi da yatsun hannunta fuskarta ɗauke da murmushi ta fara magana. "Sultan wani bawon Allah ne daya juya akalar rayuwata daga baƙin ciki zuwa farin ciki"
"Kina nufin ni ban miki wannan ba?"
"Kayi min komai, abinda kayi min ko mahaifina bai min shi ba, domin ka soni a lokacin da kowa ya gujeni, sai dai banbamcinka da Sultan shine, kai kana min son ƴan uwantaka shi kuma so na aure yake yi min."
YOU ARE READING
ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅
Horror"A ganinka wannan shine adalcin da zakayi min, matsayina na matarka amma idan zakayi kwanciyar aure dani sai dai kayi min fyaɗe, wannan wace irin azabtarwa ce, ni ba zan taɓa hanaka haƙƙin ka na aure ba, amma muguntar da kake min ta isa haka, likita...