SEASON_2 EPISODE_7

47 7 1
                                    

🧟‍♂️🧟‍♀️☠️☠️🧟‍♂️🧟‍♀️

    
        *RUHI BIYU*
  _[a gaangar jiki daya]_
                       *RETURNS*

                       🧟‍♀️🧟‍♂️☠️☠️🧟‍♀️ 🧟‍♂️      ‍

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
      _Kungiya d'aya tamkar da dubu._

        *_SPECIAL EDIT 2021/2022_*

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*Phone no:*
2349077974042

         *REPORTS*

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*📣📣📣SANARWA SANARWA📣📣📣*
_Ga masu Bin littafin Kofar aljali littafi na biyu Ina Mai Baku hakuri game da rashin posting da kuka ga ba'ayi gaskiya abubuwa ne sukayi yawwa..._
_dan hakan Ina Mai Mika sakon ban hakuri ga fans inshallah bada jimawa ba zaku jini love you all_

*😷😷STAY SAFE...  STAY AT HOME😷😷*

*FREE BOOK💯✅*
*📚LITTAFI NA BIYU*
*EPISODE_0️⃣7️⃣*




#Ramla
Farkawa tayi ta tsinci kanta a kwance Kan wata makekiyar Katifa,sai data dauki Mintuna Mai yawa tana ta jujjuya Idanu cikin wannan daki kafin Nan ta jiyo muryar Mahaifiyarta na cewa.

"Ramla wai har Yanzu baki tashi daga bacci ba."
Aiko jiyo hakan datayi sai kwakwalwarta ta daure ta kasa gane halin da tace ciki.

"Ramla maike Shirin faruwa da kene,Ya akayi Kika farka a gida bayan tare da Faruq da Kuma boka bakin bawa kuke."

Tambayar dake yimata yawo a cikin kwakwalwa kenan,Aiko kasa gane Komi tayi Nan da Nan ta d'aga Idanu ta dubi Agogon dake manne jigin bango.
nanma ta sake Shiga rud'ani Danko karfe Goma na safe ta tadda bayan karfe shadaya suka shige waccen tsohon gini.

Nanfa ta soma kokonta shin washe gari ne ko Kuma dai mafarki take...
Dauko waya tayi ta soma Kiran Faruq which is not reachable,Nan ta Mike ta bude kofa da Mahaifiyar ta ke kwankwa tuntuni.

"Ramla wacce Iriyar bacci ne wannan?,Har goma baki farka ba Aiko da Zan fita Unguwa da Babu Wanda Zaki tarar a gida domin ko Harun ya kwana a school mahaifin ku kuma ya wuce gun aiki early Yau."

Kyale ummar Nata tayi tana ta yimata wannan surutan wacce ciki ta da tambayoyi Amma taki ansa tambayar illa da tace "Umma wacce Rana ce yau." Tayi Shiru.

"Alhamis,Amma Mai yasaka Kika tambaya?."
Ansar da ummar nata ta bayar kenan hade Kuma da tambaya...

"Umma Babu Komi,kwanan wata fa?."

"Sha'takwas 18th."

Aiko da jiyo hakan ta juya Idanu gefe guda,yayinda ko zuciyar ta cike fal da wasu maganganu wacce sune.

"A Yau hakan ta faru domin kwanan wata da Kuma Rana duk daya ce,Amma tayaya lokaci ya dawo baya, sa'annan tayaya na tsinci kaina anan bayan Ina wancen ginin tare da boka da Kuma Faruq wacce suka sakani tsare kwai...."
Haka takeyima kanta wannan tambayoyi cikin kasan ranta.

Aiko shirun da tayi duk idanun Umman nata na kanta...inda tace da ita.

"Ramla lafiya kuwa."

"Umma Ina Kuma lafiya,Bayan yau da karfe sha'dayan Rana Faruq yazo ya daukeni muka fita Amma sai gani na sake tsintar kaina Nan dakin bayan Nan Kuma lokaci ya dawo baya Komi Yana Shirin maimaita kansa."

RUHI BIYI (a gangar jiki daya)Where stories live. Discover now