*ZAFIN HAWAYENA*
'''A True Life Story'''
_Wattpad@SaNaz_deeyah_*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Book1
'''Shafi na sha-tara'''"Ya ka tashi a firgice? Kamar wanda nazo masa da mugun abu?"
"Fauwaz sanin kanka ne na tsani jin ko sunanta, bare wani abu daya shafeta"
"Ya zama dole kaji abinda ya shafeta, tunda haƙƙinta gaba ɗaya a kanka yake"
"Fauwaz ko dai akwai wata alaƙa tsakaninka da ita? Na kasa gane maka, tunda kazo ka ganta tun daga ranar baka ƙara goyon bayan abubuwan da nake mata, bayan ka san ta cancanci fiye da haka ba"
"Zayyan bani da wata alaƙa da ita, hasalima ban santa ba, ban kuma taɓa ganinta ba sai dana zo gidanka, amma tun ranar da naga irin dukan da kake mata, na zauna nayi tunani, matsayina na abokinka bai kamata ina gani kana haka kuma in cigaba da biye maka"
"To yanzu ya kake so ayi?"
"Zayyan ina so ka bani hankalinka"
"Ina sauraronka
"Yana daga cikin imani mutum ya yarda da ƙaddara mai kyau da marar kyau, Zayyan dan Allah ka haƙura ka kuma miƙa lamuranka ga Allah"
"Hmmm Zayyan kenan, ai ina ganin duk abubuwan daka faɗa min an faɗa min su kafin ka faɗa, dan haka idan wannan ne ya kawo ka gidana to ka fita kawai domin ni ba zanji ba"
"Meyasa wannan ɗin ba zaka ji ba? Meyasa ba zaka yarda da ƙaddara ba, meyasa kake haka? Wannan wace irin rayuwa ce"
"Fauwaz maganar da kake kamar kanayi ne da iska, wallahi har na daina gane abinda kake faɗa"
Tashi Fauwaz yayi, ya kalli Zayyan yana girgiza kai sannan ya ce "To tunda ba zaka saurareni ba, ni zan tafi" Bai jira abinda Zayyan zai faɗa ba kawai ya wuce. Shima Zayyan bai yi magana ba kuma baiyi yunƙurin bin shi ba.
******A harabar asibitin ya tsaya yayi parking, a hankali ya fito tare da ɗauko ledojin dake bayan seat, kai tsaye asibitin ya nufa kuma ɗakin da aka kwantar da Amatul-ahad.
Sai daya fara knocking kafin ya tura ƙofar ya shiga, bakinsa ɗauke da sallama.
Zaliha ita ta amsa masa, tare dayi masa barka da zuwa.
"A'a zauna abinki" Shine abinda ya faɗa lokacin daya ga Zaliha na ƙoƙarin bashi kujera ya zauna.
Jikin gadon ya tsaya, Amatul-ahad kuwa lumshe ido tayi dan bata son haɗa ido dashi.
"Ya jikin nata?"
"Da sauƙi" Zaliha ta faɗa tana kallon fuskar Amatul-ahad.
"Sumayya ta shigo kuwa?"
"A'a amma dai nurse ta shigo, bata daɗe da fita ba"
Ledojin ya ajje sannan ya ce "Ki buɗe kuyi break ko, na san baku ci komai ba."
"Zaliha ki zuba ki ci, ni ba zanci ba na ƙoshi" Amatul-ahad ta faɗa har a lokacin idanunta a rufe suke.
Dukkansu kallonta sukayi cike da mamaki.
"Ki zuba mata ta fara ci sannan ki ci, zan je in jira a mota, idan kun gama zan dawo" Yana gama faɗa ya juya ya fita."Aunty dan Allah ki daure ki ci ko kaɗan ne"
"Bana jin yunwa"
"Ba dan yunwa ba, dan lafiyarki Aunty dan Allah."
Kai kawai ta gyaɗa bata sake cewa komai ba.
Haka Zaliha ta zuba abincin sannan ta ɗagota.
*Few Minutes Later*Ko daya shigo ɗakin a zaune ya ganta kan gado, ta jingina bayanta da pillow, Zaliha kuma na zaune kan dadduma.
Kujera yaja ya zauna, yana ganin yadda take sauke numfashi a tsorace, da alama tana mugun tsorata idan ta ganshi.
Ido ya kafeta dashi ita kuma ta juyar da kai gefe.
Juyawa yayi ya kalli Zaliha ya ce "Idan babu damuwa ki bamu guri zan yi magana da ita"
Da sauri Zaliha ta miƙe, ita kuma Amatul-ahad ta juyo tana kallonsa, yayinda shi kuma yake kallon wayarsa dake hannunsa duk da ba wani abu yake da ita.
Zaliha na fita ya ɗago ya kalleta, tayi saurin ɗauke ƙwayar idanunta a kanshi.
"Tsoro na fara baki kenan?"
Shiru tayi bata ce komai ba.
"Dan Allah ina so ki fitar da tsoron in yi miki tambayoyi, domin ina buƙatar sanin amsoshinsu.
"Fauwaz..." Ta kira sunansa kai tsaye, sai yaji abin wani iri dan bai saba jin hakan daga gareta.
"Na san an faɗa maka abubuwa da yawa game dani, bana buƙatar ka ƙara maimaita min su, duk abinda aka faɗa maka a kaina gaskiya ne"
"Gaskiya..." Ya maimaita.
"Eh, domin wanda ya faɗa maka ya san komai game dani"
"Kenan yadda aka faɗa min a kanki haka ne?"
"Eh hakane..." Ta furta lokacin da wasu zafafan hawaye suka biyo kuncinta.
"Amatul-ahad meyasa? Meyasa kika lalata rayuwarki? Na san ki da tarbiyya da tsoro ya akayi kika lalata komai?"
"Ƙaddarata ce Fauwaz, nima na tsinci kaina ne a sabuwar rayuwa, idan har ban aikata haka ba bana iya sukuni"
"Dagaske kinyi yawon bariki?"
"Kada ka zargeni, naso kazo gidanmu kayi magana da mahaifina amma ka nuna baka ƙaunata ko kaɗan"
"Ban nuna hakan ba, Amatul-ahad na taɓa furta cewa bana sonki?"
"A'a amma dai ko da baka furta a baki ba, ai ance labarin zuciyata a tambayi fuska"
"Amatul-ahad kin yiwa fuskata mummunar fahimta, ina matuƙar son ki soyayyar da ban taɓa yiwa wata ƴa mace ba, ko dawowar da nayi yanzu na dawo ne da niyyar aurenki, naje gidanki da niyyar Zayyan ya rakani gidanku kawai sai tarar dake nayi a matsayin matarsa"
Hannu biyu ta saka ta rufe fuska tare da fashewa da kuka.
"Amatul-ahad wannan shine kuskuren dana aikata mafi muni a rayuwata, ban san wane laifi nayi ba Allah ya jarabceni da wannan baƙar ƙaddarar"
Hannu ta cire daga fuska tana goge hawaye, kafin ta ce "Da nayi tunanin duk runtsi na tsaya na jira ka dawo, sai nayi tunanin ko da ka dawo ma ba lallai ka saurareni ba, idan kaji irin rayuwar da nayi, kuma aure nayi tunanin zai zamo mafita a gareni, sai kuma ya zame min wata barazana ga rayuwata, Fauwaz dan Allah ka roƙa min sassauci daga Zayyan"
Da mamaki kawai yake kallonta, duk yayi tunanin sharri ake mata, ashe gaskiya ne.
"Amatul-ahad dagaske har HIV kin kwaso a yawon da kikayi?"
Girgiza kai tayi sannan ta ce "Bani da HIV amma dai idan har aka auna a asibiti tare da mutanen da nake son kare kaina a gurinsu sai aga ina da ita."
"Ban fahimta ba?"
"Zayyan da Daddy indai mukaje asibiti dasu to tabbas re_ult zai nuna possitive, Fauwaz duk abinda aka min ni na san aikin asiri ne, amma ni ina fatan Daddy da Zayyan za su fahimci hakan anan gaba"
"Na kasa fahimtar abinda kike nufi"
"Fauwaz nayi bariki amma bani da HIV wallahi bani da ita, sharri kawai aka min"
"Amma....."
"Ba wanda zai fahinceni sai Allah, dan haka na barwa Allah komai"
"Na fahimceki, na san baki min ƙarya"
Shashsheƙar kuka ta fara, ta kauda kanta gefe.
"Amatul-ahad ina so dan Allah ki yafe min, na san da ace nazo gareki da hakan ba zata faru dake ba, inajin zafi sosai akan abinda ya faru da rayuwarki"
"Fauwaz...." Ta ƙara fashewa da kuka sannan ta ce "Amatul-ahad wallahi da nazo na tarar da rayuwar da kika shiga da ba zan rabu dake ba, da ba zan taɓa yarda rayuwarki ta shiga matsala haka ba, amma duk da haka zan yi ƙoƙari wajen nemo miki farin ciki, amma dai kafin nan ina so ki faɗa min irin rayuwar da kikayi a baya"
Ji tayi gabanta yayi mugun faɗuwa, ta ɗaga kai ta kalleshi, shima kallonta yake.
"Ki daure ki faɗa min please"
"Fauwaz bana son tunawa"
"Ki daure ki faɗa min gaskiya, dan in san ta ina zan fara."*Makaranta zan dakata anan, zan barku ku fara zuba mamaki akan abinda kuke ta muhawara akai, ba kun ɗauka cewa Fauwaz ne ya lalata ba, kuma shine ya saka mata cutar HIV, to yau kunji gaskiyar zance, zan barku ku tattauna*
_Ku shiga youtube, kuyi searching KARAMCI TV sannan ku danna mana SUBSCRIBE_
_Sadeey S Adam✍️_
YOU ARE READING
ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅
Horror"A ganinka wannan shine adalcin da zakayi min, matsayina na matarka amma idan zakayi kwanciyar aure dani sai dai kayi min fyaɗe, wannan wace irin azabtarwa ce, ni ba zan taɓa hanaka haƙƙin ka na aure ba, amma muguntar da kake min ta isa haka, likita...