Jump to content

Wikipedia:Tutorial/Mahadar shafi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gabatarwa Rajistar account Yadda ake gyaran Wikipedia Yadda ake mahadar shafi Bada madogarar bincike Shafukan tattaunawa Manufofin Wikipedia Karin bayani  

Hada shafuka masu alaka a cikin Wikipedia yana da matukar muhimmanci a Wikipedia, shine yake ba mutane dama cikin sauki su tsallak daga wannan shafin zuwa wannan shafin, sanna yan taimakawa wajen gano sabbin abubuwa wanda mai karatu bai sann dasu ba.

Yadda ake mahadar shafi

Wannan bidiyon na Turanci yana bayanin wasu muhimmanci hanyyin gyaran Wikipedia tare da yadda ake mahadar shafi.

Idan kuna so kuyi mahada daga wani shafi zuwa wani shafi (ma'ana: wiki link), Sai kawai kusa sunan shafin a cikin baka hudu, biyu a farko, biyu a karshe, kamar haka:

[[Ghana]]

Da zarar kunyi haka, in anzo karanatwa zai zama: Ghana.

Idan kuna so kuyi mahadar shafi, amma kun a son yin amfani da wani suna a madadin sunan shafin, sai kuyi amafani da alamar "|". Zaku fara sa suna shafin, sai kusa alamar "|", sannan sai kusa sunan da kuke so, sai kuma ku kulle da baka biyu. Misali:

  1. [[Kano (jiha)|Kano]] Da zarar anzo karantwa za'a ga Kano.
  2. [[Kaduna (jiha)|Jihar Kaduna]] Wannan kuma za'a ga Jihar Kaduna.

Sannan za'a iya yin mahada kai tsaye zuwa wani sashe a cikin kowane shafi ta hanyar amafani da alamar hash "#".

Kamar haka[[Sunan shafi#Sunan sashe]]
Misali: [[Nijeriya#Tarihi]] zai zama Nijeriya#Tarihi

Hakazalika, zaku iya zabar kuyi amafani da wani sunan da ya dace, a madadin cikakken sunan sahafin da sashen.

Kamar haka [[Sunan shafi#Sunan sashe|Rubutun da ake so ya fito]]
Misali: [[Nijeriya#Tarihi|Tarihin Nijeriya]] zai zama Tarihin Nijeriya

Mahada zuwa shafin yanar gizo na waje

Za'a iya yin mahada zuwa wani shafin yanar gizo na waje, wato wanda ba'a cikin Wikipedia yake ba. Domin yin hakan, kwai za'a sa cikakken sunan gidan yanar gizo ne a cikin baka biyu, daya a farko, daya a karshe.

Kamar haka: [http://www.example.com].
Shine zai bada haka [1], wwanda zai kaika zuwa shafin kai tsaye.

Sannan zaku iya amfani da sunan shafin, ko wani daban, in akwai bukatar hakan.

Kamar haka: [http://www.example.com Example.com].
Shine zai bada Example.com wainda shima zaikai zuwa wancan gidan yanar gizon kai tsaye.

Visual editor

Visual editor wata hanya ce ta gyaran Wikipedia, zaku iya ganin karin bayani a Wikipedia:Visual editor. A Visual editor zaku iya yin mahada zuwa wasu shafukan cikin sauki. Za'a iya yin mahada a kowane shafi ko na cikin Wikipedia ko shafin yanar gizo na waje ta hanyar latsa mabaalli mai alamar ko kuma ta hanyar amfani da hanyar sauri ta malatsin Ctrl tare da K wanda za'a latsa a lokaci daya.

Idan za'a yi mahadi da shafin Wikipedia na cikin gida sai kawai a rubuta sunan sa, da zarar ya fito sai a zaba kamar yadda aka nuna a hoto na kasa.
Mahadar shafi ta hanyar amfani da Visual editor
Idan kuma za'a yi mahadi a shafin yanar gizo na waje, sai a latsa malastin gefe na external link, sai asa suna shafin da ake so, kamar yadda yake a hoto na kasa.
Mahadar shafi na waje ta hanyar amfani da Visual editor

Zaku iya gani wasu hanyoyin gyare-gyaren da dama a shafin Wikipedia:Cheatsheet.


Ci gaba zuwa Bada madogarar bincike