Jump to content

Wayar hannu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Wayar hannu
mobile phone network standard (en) Fassara da mobile phone generation (en) Fassara
Bayanai
Masana'anta Sadarwa
Amfani *#06# da Wireless WAN (en) Fassara
Gajeren suna GSM
Ta biyo baya 3G (en) Fassara
Lokacin farawa 1990 da 1992
wayar salulah
wayar semens
hoton mutumin daya kirkiran Wayar hannu
wayan hannu ta zamani
wayar Motorola ta zamani
Set of phone

Wayar hannu (salula) wata na'ura ce wacce me jawo nesa kusa, me debe kewa me daga ko saukarda tattalin arzikin mutum.

Ita dai wayar hannu wato (salula) waya wata irin na'urace ce wacce aka kirkireta 1973, ta hanyar Dr. Cooper Dan kasar Amurka ne, kuma an haife shi ranar 26 ga Disamba, 1928. Ya girma a garin cikago kuma ya yi digiri a fannin Injiniyan lantarki. A shekarar 1954 ne, kamfanin Motorola ya dauki hayar sa, inda ya yiwa kamfanin aiki wajen samar da yan-madaidaitan kayayyaki, musamman ma dai na sadarwa. Daga cikin abubuwan da ya yi wa wannan kamfani har da radiyon hannu ta sadarwa tsakanin yan-sanda. Kai shine ma mutumin da ya fara yin irin wannan radio ta sadarwa a Duniya, a shekara 1967. lokacin da yake aiki da kamfanin Motorola, wanda ya samu daman zama shugaban masu bincike a kamfanin. a hakika shine Mutumin da ya samu nasarar yin kira na farko a Duniya ta amfani da wayar Salula. Kuma ya yi wannan kira ne daga wani wajen hada-hadar Mutane a garin New York, Ranar 3, ga watan Afrilu, 1973. In da ya kira wani abokin hamayyarsa yace da shi“Joe ina kiranka ne da wata na’urar wayar Salula ta hannu yar-madaidaiciya’’

Bayan shekaru 10 da kirkiro ta ne, aka fara sayar da wayar ta Salula a kasuwa, lokacin da kamfanin Motorola ya fara fito da ita akan farashi na $3,500. Amma abin mamaki duk da waɗannan makudan kudi na wayar ta Salula a wancan lokaci. Amma ba tare da wani tsawon lokaci ba, sai wannan sabuwar fasaha ta samu karɓuwa ka’in da na’in.

Wayar hannu dai ta zamo tamkar zuciyar al'umma tayanda mutum baya iya rayuwa saida ita ,Babu shakka batun wayar salula abune da ya dabaibaye Duniya a Halin yanzu. Da dai kafin zuwan wayar Salula, Mutane suna rayuwarsu ne hankalinsu a kwance, amma yanzu da wayar Salula ta zama ruwan-dare game Duniya, babu wanda yake so ya rayu ba tare da ita ba. To shin zargi zamu yi ko kuma godiya ga wanda ya kirkiro mana da wannan abu, wanda yake cinye wa mutane kudi? To imma dai zarginne ko kuma yabon, to wanda za’a zarga ko baya bayanai sun gabata kan tasirin mu'amala da wayar salula, ga al'umma baki daya, da kuma tasirin hakan ga kebantattun mutane.  Wannan na da muhimmanci wajen taimaka wa mai amfani da wayar salula ya san yadda zai yi, don kada ya afka cikin wadannan munanan tasiri su shafe shi. Duk wani abu na mu'amala yana da bangare biyu ne; da bangaren amfani, da kuma bangaren cutarwa. Ya danganci yadda mai amfani da abin yayi.  A yau kuma ga bayanai kan tsarin amfani da wayar salula a warware. Domin sanin tsarin amfani da wayar salula ne zai taimaka wa mai mu'amala fahimtar hanyoyin da zai bi wajen magance dukkan matsalolin da ke jawo munanan tasiri wajen mu'amala da wayar salula.kuma a yaba shine Dr. Martin Cooper.

A baya bayanai sun gabata kan tasirin mu'amala da wayar salula, ga al'umma baki daya, da kuma tasirin hakan ga kebantattun mutane. Wannan na da muhimmanci wajen taimakawa mai amfani da wayar salula ya san yadda zai yi, don kada ya afka cikin wadannan munanan tasiri su shafe shi. Duk wani abu na mu'amala yana da bangare biyu ne; da bangaren amfani, da kuma bangaren cutarwa. Ya danganci yadda mai amfani da abin yayi.[1][2][3][4]

  1. https://www.bbc.com/hausa/vert_fut/2015/08/150807_vert_fut_future_of_education_in_africa_is_mobile
  2. http://fasahar-intanet.blogspot.com/2013/02/tsarin-muamala-da-wayar-salula-1-10.html?m=1
  3. https://m.dw.com/ha/waye-ya-kirkiro-wayar-salula/a-2842623
  4. https://www.bbc.com/hausa/vert_fut/2015/08/150807_vert_fut_future_of_education_in_africa_is_mobile