Tuwon shinkafa
Tuwon shinkafa | |
---|---|
Tuwo da shinkafa | |
Kayan haɗi | shinkafa |
Tarihi | |
Asali | Najeriya |
Tuwon shinkafa tuwon shinkafa dai yana cikin kalar abincin mutanen Arewacin Najeriya wato Hausawa.[1] Yana daga cikin nau'ikan tuwo. Sai dai shi ana yin sa ne da shinkafa. Ana haɗa shi da miyar kuka ko miyar taushe ko miyar kubewa wajen ci.[2]. Wato tuwon shinkafa yana daya daga cikin abincin gargajiya, saboda shi ma akan hada shi da garin masara wani sa’in. Amma mafi akasari wasu ba sa sa wa, sannan sunan tuwon shinkafa ya samo asali ne daga shinkafar da ake yinsa da ita. Kuma duk Najeriya ko a ina suna amfani da ita. Akan ci shi da kowace irin miya, amma an fi cin shi da miyar taushe.[3][4][5]
kayan Hadi
[gyara sashe | gyara masomin]Shinkafar Tuwo
Ruwa[6]
Yadda ake hadawa
[gyara sashe | gyara masomin]zaa wanke shinkafar
a zuba ruwa a tukunya idan ya tafasa sai a zuba shinkafar
idan shinkafar ta dahu sosai sai a dauko muciya aci gaba da tukawa har sai ta koma tuwo
sannan sai a rufe ta dan kara silala[7]
sai a kwashe
ana ci da miyan kubewa, tabshe, ogbono da sauran su
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Hausa home videos : technology, economy and society. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. ISBN 978-36906-0-4.OCLC 61158034.
- Abubakar Aliyu Mohammed. Cultural Torism. ISBN:978-978-087-937-2
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "How to make Tuwon Shinkafa (Rice Fufu)". All Nigerian Recipes. Archived from the original on 7 July 2015. Retrieved 6 July 2015.
- ↑ "Tuwo Shinkafa (Tuwon Shinkafa) - made from Raw rice and also with Rice flour". Nigerian FoodTV. 23 August 2014. Retrieved 6 July 2015.
- ↑ https://cookpad.com/ng/recipes/13931115-tuwon-shinkafa?via=search&search_term=tuwon shinkafa
- ↑ https://cookpad.com/ng/recipes/13692517-tuwon-shinkafa?via=search&search_term=tuwon shinkafa
- ↑ https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
- ↑ https://www.allnigerianrecipes.com/fufu-recipes/tuwo-shinkafa/
- ↑ https://www.allnigerianrecipes.com/fufu-recipes/tuwo-shinkafa/