Jump to content

Tuwon masara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tuwon masara
Tuwo
Kayan haɗi tuwon masara
Tarihi
Asali Najeriya

Tuwan masara, abincin gargajiya ne mai dadadden tarihi, kuma mafi akasarin 'yan kasar musamman 'yan Arewacin Nijeriya musamman ma Hausawa ke cin shi, akan ci shi ne da miyar kuka[1]. Ana kuma matukar girmama shi tun daga karni na baya har zuwa yau ana amfani da wannan abincin. Yadda ake hada shi kuma shine akan samu masara bayan an same ta, sai a wanke a surfa,a kuma bakace dussar, wadda shima a kan sayar ga masu kiwon dabbobi. Bayan an bakace sai kuma a nika shi ya zama gari.To daga nan kuma sai girki. A sanya ruwan zafi ya tafasa har dai a kai ga tuka shi. Shikenan sai a rinka tukawa har ya yi kauri, shi ne ya zama tuwo kenan. Ana cin shi da kowace irin miya, amma an fi cin shi ne da miyar kuka a Arewacin Nijeriya wanda tun a baya da ita ake amfani sai kuma miyar kubewa.[2][3][4][5][6].

Yadda Akeyi

[gyara sashe | gyara masomin]

Da farko zaka nemi masararka ka kai a nika idan an niko sai a tankade a fidda tsaki sai wanke sai azuba ruwa a tukunya ya tafasa sai asa wannan tsakin yai ta dahuwa sai a debi tankadadden gari a zuba awani wuri sai asa ruwa adama sai azuba akan wancan sake kan wuta sai akara yan mintuna kadan sai a tuka abarshi ya sulala

  • Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Hausa home videos : technology, economy and society. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. ISBN 978-36906-0-4.OCLC 61158034.
  • Abubakar Aliyu Mohammed. Cultural Torism. ISBN:978-978-087-937-2


  1. https://en.wikipedia.org/wiki/Tuwon_masara
  2. https://bakandamiya.com/blogs/1229/96/tuwon-masara?mobile=0[permanent dead link]
  3. https://cookpad.com/ng/recipes/13378123-tuwon-masara?via=search&search_term=tuwon masara
  4. https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
  5. https://cookpad.com/ng/search/tuwon masara
  6. Adamu, Abdallah Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Hausa home videos : technology, economy and society. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. p. p 473-475 ISBN 978-36906-0-4.