Sartor Resartus
Sartor Resartus: The Life and Opinions of Herr Teufelsdröckh in Three Books wani littafi ne na marubucin rubutun Scotland, masanin tarihi da falsafa Thomas Carlyle, wanda aka fara buga shi a matsayin jerin a cikin Fraser's Magazine a watan Nuwamba shekarar alif 1833 zuwa watan Agusta shekarata alif 1834. Littafin yana nufin ya zama sharhi game da tunani da farkon rayuwar wani masanin falsafa na Jamus mai suna Diogenes Teufelsdröckh (wanda ke fassara a matsayin 'Allah-haifiyar Iblis'), marubucin wani littafi mai suna Clothes: asalinsu dakuma kalubale . Tunanin Transcendentalist na Teufelsdröckh ya kasance mai shakka ne daga mai bita na Ingilishi (wanda ake kira Edita) wanda kuma ke bada bayanan rayuwa game da masanin falsafa. Aikin, a wani bangare, ya zama abin dariya game da Hegel, da kuma Jamusanci Idealism gabaɗaya.