Muhammad Yusuf
An taskan ce wannan muƙalar a cikin jerin Muƙaloli_masu_kyau a Hausa Wikipedia
Ana sa ran wata rana wannan muƙalar zata kasance a Babban Shafin Muƙalar mu a yau |
Muhammad Yusuf | |||
---|---|---|---|
2002 - 30 ga Yuli, 2009 - Abubakar Shekau ⊟ | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jihar Yobe, 29 ga Janairu, 1970 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | Maiduguri, 30 ga Yuli, 2009 | ||
Yanayin mutuwa | (extra-judicial killing (en) ) | ||
Ƴan uwa | |||
Yara |
view
| ||
Sana'a | |||
Sana'a | Mai da'awa | ||
Aikin soja | |||
Ya faɗaci | Rikicin Boko Haram | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci |
Muhammad Yusuf Ya kasance kuma An Haife shi a ranar: 29 ga watan Janairun Shekara ta 1970 - ya Mutu a ranar: 30 ga watan Yulin shekara ta 2009), kuma an san shi da Ustaz Muhammad Yusuf, dan Nijeriya ne kuma malamin addinin musulunci ne. wanda ya kafa akidar cewa karatun boko haramun ne, an masa kallan dan ta'adda wanda ya kafa kungiyar Boko Haram a Najeriya a shekara ta 2002, wanda yanzu haka tasirin wannan gungiyar ta Boko Haram ya shiga kasar Nijar, Cadi, da Kamaru, Shi ne shugaban ta na farko har aka kashe shi a rikicin Boko Haram na farko a cikin garin Maiduguri [1], wanda daga baya mataimakin sa Abubakar Shekau ya ci gaba da jagoranta. Muhammad yusuf ya kasance yana bibiyan karatun Mallam Ja'afar Mahmud Adam wanda mallam Ja'afar ya hadu da shi a makkah ya nuna masa wannan akida da yake so ya kafa mutane a kai ba daidai ba ne ya rantse da Allah cewar wadannan mutanan ba dalibansa ba ne ya kara da cewa shi bai san su ba sai mallam ja'afar mahmud adam ya ce indai kana son ka kubuta daga wannan aqida to ka dauki alkalin da zai rubuta da yawunka kai ka kubuta daga wannan aqida da ake jingina ka da ita haka muhammad yusuf ya sa aka samo alkalin da suke cewa aikin boko haramun ne shine yayi masa rubutu da yaran da ake cewa haramun ne akayi har ,muhammad yusuf yasamu yadawo najeriya daga baya ya nuna wa duniya shi yana nan akan bakan sa na nunawa duniya cewa yin karatun boko haramun ne.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Yusuf wanda aka haifa a kauyen Girgir, a cikin Jakusko, jihar Yobe ta yanzu, a Najeriya, ya sami ilimi a gida, wato a ƙasa Najeriya, musamman ma a Borno. [2] A farkon rayuwar shi ya fara shi'anci ne, daga baya ya tuba ya koma salafiyyanci, Daga baya ya kara karatun addinin Musulunci kuma ya zama dan Salafiyya.[3] inda a gab da karshan rayuwar sa shugaban salafiyya na Najeriya mai suna Muhammad Auwal Albani Zaria ya barran ta da shi, bayan jin akidar shi na Boko Haram.
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]A cewar wani masani Paul Lubeck na Jami'ar California da ke Santa Cruz, a lokacin da yake saurayi Yusuf an koyar da shi Shi'a a karkashin jagoran cin Ibrahim Zakzaky. daga baya yace ya tuba ya koma Ahlus-Sunnah, inda ya kulla alaka da Salafiyya, kuma yace yana bin koyarwar Ibn Taimiyya .[4] Yana da kwatankwacin karatun digiri na biyu, a cewar wani malami dan Najeriya Hussain Zakaria. Yusuf bai taɓa kwarewa sosai a Turanci ba kamar yadda aka ruwaito. Ya yi imani da aiki da shari'ar Musulunci sosai, wanda ke wakiltar abin da ya dace da shi na adalci bisa koyarwar annabin Islama, Muhammad.(SAW) Mayakan Boko Haram za su kashe membobin wasu kungiyoyin Musulmi kamar kungiyar Izala ta Salafist da 'yan kungiyar Sufi Tijjaniyya da Qadiriya.[5] A cikin hirar da yayi tare da BBC, wacce ta yi da shi a shekarar 2009, Yusuf ya bayyana imaninsa cewa batun ilmi kan cewa duniyan da ke zagaye da sararin samaniya ya saba wa koyarwar Musulunci kuma ya kamata a yi watsi da shi . Ya kuma yi watsi da juyin halittar masanin kimiyya mai suna Darwin, da kuma batun kewayen halittar da ke samar da ruwan sama. [6] A cikin hirar harma ya ce:
Error: No text given for quotation (or equals sign used in the actual argument to an unnamed parameter)
— "Akwai wasu fitattun masu wa'azin addinin Islama da suka gani kuma suka fahimta cewa ilimin zamani irin na Yammacin Turai ya gauraya da batutuwan da suka saba wa abin da muka yi imani da shi a Musulunci," in ji shi.
Error: No text given for quotation (or equals sign used in the actual argument to an unnamed parameter)
— "Kamar ruwan sama . Mun yi imani halittar Allah ce maimakon kazamar ruwa da rana ta haifar wanda ke tattarawa kuma ya zama ruwan sama.
Error: No text given for quotation (or equals sign used in the actual argument to an unnamed parameter)
— "Kamar faɗin duniya yanki ne . Idan ta ci karo da koyarwar Allah, sai mu ki shi. Mun kuma ki yarda da ka'idar Darwiniyanci."
A Ƙida
[gyara sashe | gyara masomin]kamar yadda wani masani a harkan ta'addanci mai suna Paul Lubeck na Jami'ar Kalifoniya ya fada, yace Muhammad Yusuf a lokacin kuruciyar sa ya fara bin akidar Shi'a ne a karkashin jagoranci Ibrahim Zakzaky, wanda daga baya yace ya tuba, daga bisani sai ya koma akidar Salafanci, inda ya fara karatu a karkashin Albani Zaria da Ja'afar Mahmud Adam, kuma yana bayyana cewa yana bin koyarwar Shehin Musulunci mai suna Ibn Taymiyyah, bayan ya bayyana akidar sa na cewa Boko Haramun ne sai Albani Zaria da Ja'afar Mahmud Adam suka barran ta da shi, kuma suka yi masa wa'azi gami da raddi.
An ruwaito cewa bai iya turanci ba, amma manazarta ilimin sun karyata hakan, rahotanni sun tabbatar da cewar yana yin Turanci sosai,sannan ya iya larabci daidai gwar gwado kuma yakasance me halartar karatun mallam ja'afar mahmud adam
Kafa gungiya
[gyara sashe | gyara masomin]Muhammad Yusuf ne ya fara da'awan kungiyar mai suna da larabci Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad, wanda a larabci yake nufin "Al'umma masu bin Sunna, masu da'awa da jihadi ". [7] Musulmi ne kuma dan Najeriya wanda ya kafa kungiyar Boko Haram a shekara ta 2002. Shine ya zama shugaban ta har izuwa lokacin da ya rasa ransa a shekarar 2009. Asalin sunan kungiyar ita ce Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan rikicin Boko Haram na watan Yulin 2009, sojojin Najeriya suka kama Yusuf a gidan surukin sa, daga baya sun mayar da shi hannun rundunar yan sandan Najeriya. [8] 'Yan sanda sun kashe Yusuf a gaban jama'a a gaban hedkwatar' yan sanda na Maiduguri . [9] [10] [11] Jami'an 'yan sanda da farko sun yi ikirarin cewa an harbe Yusuf ne a yayin da yake kokarin tserewa, ko kuma ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu a yayin artabu da sojoji.[10] [11]
Rayuwar shi
[gyara sashe | gyara masomin]Yusuf yana da mata hudu da ‘ya’ya 12, [12] daya daga cikinsu shi ne Abu Musab al-Barnawi, wanda ya yi ikirarin cewa shine shugaban Boko Haram tun shekarar ta 2016 a matsayin sahihin shugaban kungiyar Boko Haram, yana adawa da Abubakar Shekau.[13] An ba da rahoton cewa yana rayuwa na jin dadi, wanda ya haɗa da mallakan kayan alatu, irin su Mercedes-Benz, wayar hannu da kuma Komfuta.[14]
Diddigin bayanai na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Al Jazeera (9 Fabrairu 2010), Bidiyo ya nuna 'hukuncin kisa' a Najeriya
- Duodu, Cameron (6 Agusta 2009), "kwanakin karshe na Yusuf Yusuf", The Guardian
- Kungiyar Kare Hakkin Dan-Adam (2012), "Rikicin Rikici: Hare-haren Boko Haram da Zagin Jami'an Tsaro a Najeriya", 11 ga Oktoba 2012
- Murtada, Ahmad (2013), Boko Haram: Tushenta, Ka'idoji da ayyukanta a Najeriya, Sashen Nazarin Addinin Musulunci,Jami'ar Bayero, Kano, Najeriya
- Duodu, Cameron (6 Agusta 2009), "kwanakin karshe na Yusuf Yusuf"[permanent dead link], Gistlover
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Boko Haram: The Emerging Jihadist Threat in West Africa – Background, Anti-Defamation League, December 12, 2011.
- ↑ "West African Militancy and Violence", page 74
- ↑ Dowd, Robert A. (2015-07-01). Christianity, Islam, and Liberal Democracy: Lessons from Sub-Saharan Africa (in Turanci). Oxford University Press. p. 102. ISBN 9780190225216.
- ↑ Johnson, Toni (2011-12-27). "Backgrounder – Boko Haram". www.cfr.org. Council of Foreign Relations. Retrieved March 12, 2012.
- ↑ Vicky, Alain (2012-04-01). "Aux origines de la secte Boko Haram". Le Monde diplomatique (in Faransanci). Retrieved 2019-12-04.
- ↑ "Nigeria's 'Taliban' enigma". BBC News. 28 July 2009. Retrieved 2009-07-28.
- ↑ "Who are Nigeria's Boko Haram Islamists?". BBC News. 26 August 2011.
- ↑ "Nigeria row over militant killing". BBC News. 31 July 2009. Retrieved 27 June 2015.
- ↑ Adam Nossiter & David D. Kirkpatrick (May 7, 2014). "Abduction of Girls an Act Not Even Al Qaeda Can Condone". The New York Times. Retrieved 2014-05-08.
- ↑ 10.0 10.1 Human Rights Watch (11 October 2012). Spiraling Violence: Boko Haram Attacks and Security Force Abuses in Nigeria. Retrieved 27 June 2015.
- ↑ 11.0 11.1 "Video shows Nigeria 'executions'". Al Jazeera. 9 February 2010. Retrieved 27 June 2015.
- ↑ "Nigeria sect head dies in custody". BBC News. BBC. 2009-07-31. Retrieved May 25, 2012.
- ↑ "Shekau Resurfaces, Accuses New Boko Haram Leader al-Barnawi Of Attempted Coup". 360nobs. 4 August 2016. Archived from the original on 17 July 2018. Retrieved 16 July 2018.
- ↑ "Nigeria's 'Taliban' enigma". BBC News. 28 July 2009. Retrieved 2009-07-28.
- CS1 Turanci-language sources (en)
- CS1 Faransanci-language sources (fr)
- Muƙaloli masu kyau
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from June 2023
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- Wikipedia articles with GND identifiers
- Wikipedia articles with PLWABN identifiers
- Wikipedia articles with VIAF identifiers
- Wikipedia articles with WorldCat-VIAF identifiers
- Mutane
- Kanuri
- Yan ta'adda
- Yan Boko Haram
- Mutane daga Jihar Borno
- Musulman Najeriya
- Malami
- Malaman Najeriya
- Mutuwan 2009
- Haifaffun 1970
- Yan ta'addan a Najeriya
- Malaman Musulunci a Najeriya