Masarautar Bauchi
Masarautar Bauchi | ||||
---|---|---|---|---|
masarautar gargajiya a Najeriya | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Najeriya | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | Jihar Bauchi |
Masarautar Bauchi wacce daular ce da Fulani suka kafa a farkon karni na 19 a jihar Bauchi yanzu ta Najeriya, tare da babban birninta a Bauchi . Masarautar ta samo asali ne karkashin “kariya” ta Biritaniya a zamanin mulkin mallaka, kuma a yanzu ana alakanta masarautar da masarautar gargajiya.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Kafin jihadin na Fulani, yankin na Bauchi yana da kananan kabilu da yawa, wasunsu kuma suna magana da yaruka da Hausa, wasun su musulmai ne. Yankin na Bauchi ya ci nasara tsakanin Shekara alib 1809 zuwa shekara alib 1818 ta jarumawan Fulani karkashin jagorancin Yakubu gerawa, dan wani basarake wanda ya yi karatu a Sakkwato kuma ya yi karatu a karkashin Shehu Usman dan Fodio.
Masarautar ta ci gaba da zama a karkashin mulkin daular musulunci ta Fulani har zuwa shekarar alib 1902 lokacin da Turawan Ingila suka mamaye babban birnin kasar ba tare da yin fada ba. Kasar Ingila ta soke cinikin bayi, wanda ya ɗore har zuwa wannan lokaci, sannan ta naɗa sabon sarki, wanda ya mutu bayan ƴan watanni. A cikin shekara ta alib 1904 sarkin da yayi nasara yayi rantsuwa da rawanin Burtaniya.
Sarakuna
[gyara sashe | gyara masomin]Sarakunan da suka mulki Masarautar Bauchi, wadanda ake yiwa laƙabi da Lamiɗo, sune:
Fara | Ƙarshe | Mai Mulki |
---|---|---|
1805 | 1845 | Yaqubu I dan Dadi (b. 1753 - d. 1845) |
1845 | 1877 | Ibrahima dan Yaqubu |
1877 | 1883 | Usman dan Ibrahima |
1883 | 1902 | Umaru dan Salamanu |
1902 | 1902 | Muhammadu mu'allayidi dan Ibrahima (d. 1902) |
1903 | 1907 | Hasan dan Mamudu (a. 1907) |
1907 | 1941 | Ya`qubu II dan Usman (d. 1941) |
1941 | 28 Satumba 1954 | Yaqubu III dan Umaru (maje wase) |
Mayu 1955 | 19. . | Adama Jumba dan Yaqubu |
27 Yuli 1982 | 24 Yuli 2010 | Suleiman Adamu (d. 24 ga Yuli 2010, shekara 77) |
29 Yuli 2010 | Rilwanu Suleimanu Adamu (b. 1970) |