Mansur Mukhtar
Mansur Mukhtar | |||
---|---|---|---|
17 Disamba 2008 - 17 ga Maris, 2010 ← Shamsuddeen Usman - Olusegun Olutoyin Aganga ⊟ | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | jahar Kano, 21 Satumba 1959 (65 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
University of Sussex (en) King's College, Lagos | ||
Thesis | The dynamics of agricultural development in Nigeria : a critical assessment of radical political economy perspectives and a case study of groundnut producers | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Mai tattala arziki |
Mansur Mukhtar (an haife shi a ranar 21 ga watan Satumban 1959) masanin tattalin arziƙin Najeriya ne wanda aka naɗa shi ministan kuɗi a majalisar ministocin shugaba Umaru Musa Ƴar'Adua a ranar 17 ga Disambar 2008.[1] Ya bar mulki a watan Maris ɗin 2010 lokacin da muƙaddashin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya rusa majalisar ministocinsa.[2]
Fage
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Mukhtar a ranar 21 ga watan Satumban 1959 a garin Kano. Ya halarci Kwalejin King da ke Legas, sannan ya yi karatun digiri na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Tattalin Arziƙi shekarar 1980.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Ya yi aiki a Babban Bankin Najeriya a matsayin Mataimakin Masanin Tattalin Arziƙi (1980-81), kuma a matsayin mataimakin malami mai digiri, a 1981 da 1982 a Jami'ar Bayero dake Kano. Ya sami digiri na biyu a fannin tattalin arziƙi da siyasa na ci gaba daga Jami'ar Cambridge, United Kingdom a shekarar 1983, sannan ya sami digiri na uku a fannin tattalin arziƙi daga Jami'ar Sussex, Brighton a cikin Fabrairun 1988. Mukhtar ya kasance shugaban sashin tattalin arziƙi kuma malami a jami'ar Bayero ta Kano daga 1988 zuwa 1990.[3]
Muhtar ya kasance mai bada shawara/mataimaki na musamman ga ministan noma da albarkatun ƙasa daga 1990 zuwa 1992. Ya yi aiki a Bankin Duniya (1992-2000) a ayyuka daban-daban. Ya kasance mataimakin babban manaja a bankin United Bank for Africa tsakanin watan Yulin 2000 zuwa Maris 2001, sannan ya zama babban darakta a bankin ci gaban Afirka da ke Tunis.[3]
An naɗa shi ministan kuɗi a majalisar ministocin shugaba Umaru Musa Ƴar’adua a ranar 17 ga watan Disambar 2008.
Mukhtar ya kasance babban daraktan bankin duniya daga 2011 zuwa 2014. [4] Naɗin da ya yi a kan wannan matsayi na cikakken lokaci a birnin Washington ya samo asali ne sakamakon samar da karin kujera ga Afirka a cikin kwamitin bankin duniya . Yanzu Afirka na da kujeru uku a hukumar tun watan Nuwamban shekarar 2010. Ayyukan Dokta Mansur a cikin hukumar za su haɗa da tsara dabaru da kuma amincewa da manufofi da shirye-shiryen ƙungiyar Bankin Duniya a ƙasashe mambobin ƙungiyar, amincewa da manufofin cikin gida da suka haɗa da albarkatun ɗan adam da sa ido kan al'amuran da suka shafi gudanar da ayyukan ƙungiyar.[5]
A shekarar 2014 ya koma Jeddah a ƙasar Saudiyya inda ya zama mataimakin shugaban ƙasa na ayyukan bankin ci gaban Musulunci.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ http://allafrica.com/stories/200812195005.html
- ↑ http://allafrica.com/stories/201003171041.html
- ↑ 3.0 3.1 https://www.hugedomains.com/domain_profile.cfm?d=triumphnewspapers.com
- ↑ 4.0 4.1 Business for Africa and the World, Dr. Mansur Muhtar – Vice President Operations, Islamic Development Bank Archived 2019-08-21 at the Wayback Machine, 2018
- ↑ http://allafrica.com/stories/201105180566.html