Jump to content

Lasisi Elenu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lasisi Elenu
Rayuwa
Cikakken suna Nosa Afolabi
Haihuwa Kwara, 20 ga Afirilu, 1991 (33 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ilorin
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a jarumi, cali-cali da brand ambassador (en) Fassara
Ayyanawa daga
Imani
Addini Kiristanci
Lasisi Elenu

Nosa Afolabi (an haife shi 20 ga watan Afrilun shekarar 1991), wanda aka fi sani da Lasisi Elenu, ɗan wasan barkwanci ne, ɗan wasan kwaikwayo, ma kaɗi kuma mawaƙi[1] daga garin Offa, Kwara a kasar Najeriya.[2] Ɗaya daga cikin shahararrun masu tasiri a Afirka, an san shi da skits tare da faɗin bakitacewa yayin wasan kwaikwayo da kuma a kan kafofin watsa labarun. Elenu kwanan nan ya fito a cikin Netflix thriller,[3] The Ghost and the Tout.[4]

A cikin shekarar 2018, an zaɓe shi don bayar da Kyautar Future Awards Africa don na ɗan wasan barkwanci. A cikin watan Maris din shekarar 2020, an nada shi daya daga cikin manyan 25 na kasar Najeriya na ƙasa da 30 Superstars.[5]

Farkon asali da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Elenu, ko da yake an haife shi Nosa Afolabi a jihar Kano, arewacin Najeriya, ya fito ne daga Offa a jihar Kwara. Ya kammala karatunsa na Ilimin Kiwon Lafiya da Lafiyar Muhalli daga Jami'ar Ilorin.[6]

Mai wasan barkwanci yana ɗaya daga cikin mashahuran masu tasiri na kafofin watsa labarun nahiyar tare da mabiya 75,000 akan TikTok[7] kuma sama da 3.4 mabiya miliyan a Instagram.[8][9]

Skits nasa yana mai da hankali kan batutuwa daban-daban daga doka zuwa laifukan yanar gizo, tattalin arziki, rashin tsaro da falsafa, sun fara ne a matsayin mawaƙa kafin karkata zuwa kasuwancin ban dariya.[10] Aikin da ya yi na baya-bayan nan, Mama & Papa Godspower, shiri ne na tsawon mintuna 16 wanda ke mayar da hankali kan gidaje masu karamin karfi a Najeriya.[11][12]

Takaddama ta barke ne a watan Yulin shekarar 2020 lokacin da mambobin ƙungiyar lauyoyin Najeriya suka gargadi Elenu, wadanda suka yi ikirarin barkwancinsa na bata sunan lauyan da yi masa barazanar kai ƙararsa.

A wata hira da ya yi, ya kuma yi iƙirarin cewa wasu daga cikin masoyansa mata sun nemi yin lalata da shi daga wurinsa.

  1. "Lasisi Elenu (Nosa Afolabi)'s schedule for Social Media Week Lagos". socialmediaweeklagos2018.sched.com. Retrieved 12 November 2020.
  2. "Female fans usually ask me for sex –Musa Afolabi, comedian". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 12 November 2020.
  3. "The Ghost and the Tout | Netflix". www.netflix.com (in Turanci). Retrieved 12 November 2020.
  4. "The Future Awards Africa Prize for Comedy". The Future Awards Africa (in Turanci). 2 December 2018. Archived from the original on 12 November 2020. Retrieved 12 November 2020.
  5. "See Who Made Top 25 Under-30 Nigerian Superstars". P.M. News (in Turanci). 4 March 2020. Retrieved 12 November 2020.
  6. "10 things you Probably Don't Know About the Fast-Rising Comedian, Lasisi Elenu – Opera News". za.opera.news. Archived from the original on 18 November 2020. Retrieved 12 November 2020.
  7. Okike, Samuel (8 August 2019). "African meme accounts are becoming big on Instagram, but this comes at a price". Techpoint Africa (in Turanci). Retrieved 12 November 2020.
  8. "Lasisi Elenu (@lasisielenu) • Instagram photos and videos". www.instagram.com (in Turanci). Retrieved 12 November 2020.[self-published]
  9. BellaNaija.com (13 January 2018). "Lasisi Elenu shares his Journey to Fame in New Interview | WATCH". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 12 November 2020.
  10. Isaac, Michael (15 April 2020). "'This Country Isn't Safe, I Don't Feel Safe' – Lasisi Elenu (Video)". Information Nigeria (in Turanci). Retrieved 12 November 2020.
  11. "Lasisi Elenu launches new web series "Mama and Papa Godspower"". P.M. News (in Turanci). 8 September 2020. Retrieved 12 November 2020.
  12. Tv, Bn (8 September 2020). "Lasisi Elenu is Out with a New Comedy Series "Mama and Papa Godspower" | Watch Episode 1". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 12 November 2020.
  13. "The Ghost and the Tout", Wikipedia (in Turanci), 12 November 2020, retrieved 12 November 2020
  14. "'Sylvia' producers star Lasisi Elenu in upcoming comedy, 'The Razz Guy'". Pulse Nigeria (in Turanci). 18 May 2020. Retrieved 12 November 2020.
  15. Newswatch.ng (18 May 2020). "Lasisi Elenu Star in New Comedy Movie "The Razz Guy"". Newswatch Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 19 May 2020. Retrieved 12 November 2020.