Jump to content

Hari a Jos da Maiduguri, 2010

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
2010 Jos da Maiduguri
Yan Boko Haram

A ranar 24 ga Disamba, 2010, ƙungiyar Boko Haram ta kai hare-hare a Jos da Maiduguri a Najeriya, inda suka kashe mutane 38. [1]

Wasu bama-bamai huɗu sun tashi a garin Jos Jihar Filato inda mutane 32 suka mutu: biyu kusa da wata babbar kasuwa daya a yankin da akasari mabiya addinin kirista ne da kuma wani kusa da titin babban masallacin birnin. [1] Mutane 6 ne suka mutu sakamakon harin da aka kai wasu majami'u biyu a Maiduguri, jihar Borno . [1]

Kungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin kai dukkan hare-haren. [1]