Guga
Guga jam'in ta shine Guguna dai ana nufin makamfata ce wadda ake debo ruwa daga rijiya, guga dai abu ce da ake amfani da ita wajen debo ruwa da ita a rijiya ta hanyar kulla mata igiya.[1] Kuma guga kala-kala ce akwai wadda dabbobi ke jan ruwa da ita akwai kuma wadda mutane ne ke jawo ruwa da ita, wannan ya nuna akwai babba akwai karama, akwai kuma ta karfe da roba har ta fata misali idan kaje irin Nijar zaka ga kusan dabbobi ne ake amfani dasu wajen debo ruwa da guga wadda babba ce.Ana yin karin magana wai "guga baki tsoron rame" ma'ana idan kaji an yi wa mutum wannan karin maganar to ana nufin ba yada tsoro.
.
Amfanin guga
[gyara sashe | gyara masomin]Amfanin guga dai amfani ne da baya musultuwa domin babu wata al'ummah ko dabba da za'a iya rayuwa ba tare da ruwa ba. [2].
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]https://www.rumbunilimi.com.ng/ Archived 2021-03-03 at the Wayback Machine