Dapo Sarumi
Appearance
Dapo Sarumi | |||
---|---|---|---|
ga Yuni, 1999 - ga Janairu, 2001 - Jerry Gana ⊟ | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Epe (en) , 20 century | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Jam'iyyar SDP |
Dapo Sarumi ɗan siyasar Najeriya ne daga jihar Legas.[1][2] Ya kasance tsohon ministan yaɗa labarai. A cikin shekarar 1991 ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar Social Democratic Party (Nigeria) a ƙarƙashin jam’iyyar People’s Front ta SDP ƙarƙashin jagorancin Shehu Musa Ƴar’adua, ƴan jam’iyyar PF sun haɗa da Yomi Edu, Bola Tinubu, Abdullahi Aliyu Sumaila, Abubakar Koko, Babalola Borishade. Umaru Musa Ƴar'adua, Sabo Bakin Zuwo, da Rabiu Musa Kwankwaso amma daga baya aka hana shi takara.
A ƙarshen shekarar 2000, ya yi hatsarin mota kuma ya rasa wasu mataimakansa biyu na ministoci." Minista ya yi asarar mataimaka a haɗarin hanya," Kamfanin Dillancin Labarai na Panafrica, Disamba 27, 2000.[3]