Ashraf Mansour
Ashraf Mansour (FAAS (Larabci: أشرف منصور) Masanin kimiyya ne ɗan ƙasar Masar kuma farfesa a fannin kimiyyar lissafi ta polymer. Shi ne wanda ya kafa kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na Jami'ar Jamus a Alkahira (GUC).
Ilimi da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Mansour ya sami digirin digirgir kuma ya sami ilimin kimiyyar polymer daga Jami'ar Ulm a shekara ta 1992.[1]
A cikin shekarar 1994, Mansour ya fara aikin samar da Jami'ar Jamus a Masar. Jami'ar Jamus a Alkahira (GUC) ita ce jami'ar Jamus ta farko da aka kafa a wajen Jamus da kuma wajen iyakokin Turai. An kafa ta ne bisa wata doka ta shugaban ƙasa a shekara ta 2002 da tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak, da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schroeder, da kuma wasu fitattun mutane a fannin ilimi da masana'antu na Masar da Jamus suka bayar.[2][3]
A cikin shekarar 2003, an ƙaddamar da GUC a wajen iyakokin birnin Alkahira. Mansour ya tabbatar da gina sabuwar jami'a ta fasaha a birnin New Alkahira, ya ba da tallafin kusan Euro miliyan 15 daga masu ba da taimako na Masar, kuma ya ba da taimakon ikon koyarwa na jami'o'in Stuttgart da Ulm don tabbatar da manufarsa. Sun taimaka wajen ginawa da kafa ɗakunan gwaje-gwaje ta fasaha kuma sun kawo manhajar karatunsu na Jamus. Shirin ya samu tallafi daga hukumar ta DAAD a kuɗi kimanin Yuro 600,000 a wani bangare na shirinta na fitar da kwasa-kwasan Digiri na Jamus.[1][4] Dalibai, malamai, da masu bincike daga GUC suna samun ƙarin tallafi daga DAAD da Gidauniyar Alexander von Humboldt yayin zaman nazari da bincike daban-daban. Shi ne shugaban kwamitin amintattu na jami’ar.[5][6][7]
Bayan juyin juya halin Masar na 2011, Majalisar koli ta Sojoji (SCAF) ta ba wa Ashraf ya zama shugaban ma'aikatar ilimi mai zurfi a shekara ta 2014 amma majalisar koli ta jami'o'in Masar ta nuna rashin amincewa da naɗin nasa.[8][9][10] Hossam Eisa ya kasance a matsayin kuma Ashraf El-Shihy ya maye gurbinsa a watan Satumba 2015.[11]
Kyaututtuka da karramawa
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekarar 2008, Mansour ya sami Federal Cross of Merit,[12] kuma shi Sanata ne mai daraja na Jami'ar Ulm.[1] An zaɓi Mansour a matsayin fellow mai daraja na Kwalejin Kimiyya ta Afirka a shekara ta 2018.[13]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Prof. Dr. Ashraf Mansour". www.daad.de (in Turanci). Retrieved 2022-11-19.
- ↑ "German University in Cairo - History and Facts". www.guc.edu.eg (in english). Retrieved 2022-11-19.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "GUC has 42% of Deutsch universities' students outside Germany - Daily News Egypt". dailynewsegypt.com (in Turanci). 2019-10-03. Retrieved 2022-12-04.
- ↑ "Egypt is gateway to Africa, Arab world:German University chief". EgyptToday. 2017-09-23. Retrieved 2022-12-04.
- ↑ "من هو اشرف منصور وزير التعليم العالي ؟سيرة ذاتية ومعلومات ويكيبيديا" (in Larabci). Retrieved 2022-11-30.
- ↑ "نموذج أشرف منصور - عماد الدين حسين - بوابة الشروق". www.shorouknews.com (in Larabci). Retrieved 2022-11-26.
- ↑ "German University in Cairo - Professor Dr. Ashraf Mansour In Germany for GUC's 20th Anniversary". www.guc.edu.eg (in english). Retrieved 2022-11-19.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "القوى السياسية والحزبية: الحكومة الجديدة عودة لدولة ما قبل 25 يناير". جريدة المال (in Larabci). 2014-02-27. Archived from the original on 2023-01-01. Retrieved 2023-01-01.
- ↑ "هل تمرد القضاة على السيسى؟". الصحراء (in Larabci). Retrieved 2023-01-01.
- ↑ القاهرة, محمد هجرس- (2014-02-28). "حراسة عسكرية بالدبابات على سجن طرة". alyaum (in Arabic). Retrieved 2023-01-01.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "Egypt's Sherif Ismail cabinet with 16 new faces sworn in by President Sisi - Politics - Egypt". Ahram Online. Archived from the original on 2020-12-23. Retrieved 2023-01-01.
- ↑ "Professor Ashraf Mansour mit Bundesverdienstkreuz ausgezeichnet|Botschafter Erbel: "Gallionsfigur der deutschen Kultur in Ägypten" - Universität Ulm". uni-ulm (in Jamusanci). Retrieved 2022-12-04.
- ↑ "Mansour Ashraf | The AAS". www.aasciences.africa. Archived from the original on 2022-11-19. Retrieved 2022-11-19.